27

5K 464 35
                                    

* YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.27
            Ina ganinshi na saukar da kaina kasa, kwallar dake idanuna ne suka shiga sauka da sauri da sauri, kamar an buɗe pampo....
       "Muje kici abinci."
   Ya faɗa min babu alamar sassauci a maganarshi, ɗago kai nayi zance na koshi naga fuskarshi tam, jikina na rawa na wucce har inda aka jera abincin.
          Tunda na zauna nake shashekar kuka, daga Dadda har Mamie babu wanda ya ɗ'ago kanshi asalima banza sukayi dani.
                   Na gaza cin komi sai kuka, ran mamie ne ya ɓaci ta ajiye cokalinta da mugun karfi, wanda yasani ja da baya. Ina kallonta jikina narawa cikin isa da mulki tace.
"Zan baki zaɓi biyu kija bakinki kiyi shiru ki karya, ko kuma ki tashi ki koma ɗ'akinki. Kuma zan faɗa miki abu na karshe baza'a kaiki Bauchin ba, kiyi duk abinda zakiyi wawuyar Yarinya ce miki akayi gidan sarauta daidai yake da sauran gidajen, ko da kika ganshi shima career ɗinshi ya bari ya amshi mulkin da tashine da yanzun muna sudan, ki shiga hankalinki karki bari na fusata da yawa dan bani da kyau."
      Da gudu na tashi nabar gurin, ina shiga ɗaki na fara farfasa musu duk wani abin da yake cikin ɗakin tare da wargaza komi dake jere.
     Ina kuka tare da cewa.
"Bana son, ku kaini gurinshi ni bazan zauna daku ba, ni bana son gidan sarauta ku kaini Gurinshi kawai ni bansan ku ba, kawai taimakona kuka yi. Ku mai dani inda nasa ba, Wayyo Ya Maheer."
    Ihu nake musu tare da fasa duk wani abu.
    Dafe goshinsa Dadda yayi, ajiye cokalin dake hannunta tayi jikinta yana masifar rawa, ta nufo ɗakina.
  Buɗe ɗakin tayi taga komi a lalace ina tsakiyar kwalabe, hannuna da kafana duk sun farfashe.
         Cike da takaici take kallona.
              Ranta na kara zafi, ko ba'a faɗa mata yau takara tabbatarwa Khadija Yartane, amma tashi a mabanbantar guri ya maida mata Y'a mara ɗ'a'a da sanin ya kamata.
            Rufe kofar tayi takira Bayi suka shigo aka gyara min ɗakin kaina a cikin cinyoyina, ina gunjin kuka.
           Dafa ni akayi na ɗago da sauri, Dadda ne. Faɗawa jikinshi nayi cikin kuka nace.
"Dadda kayi hakuri bani kumawa, sai dai i miss him lo...."
      "Tashi muje bauchi."
     Yace min, tare da rufe min bakina.
       Kallon hannuna nayi inda na yanke, nace.
"Bana son zuwa, na hakura tunda baku so,,,"
    Shiru nayi sannan nacigaba da cewa.
"Dadda forgive me, kacewa Mamiena am so sorry kar tayi fushi dani."
        D'ago ni yayi zuwa ban ɗaki ya wanke min hannuna, sannan ya saka tissue ya goge min hannuna ya dawo dani bakin gado ya zaunar dani, yana cire kwalbar dake cikin hannuna. A madadin naji zafin ciwon sai zafin zuciyana nake ji.
     Yana gama cire min ya fita.
     Sai gashi da abinci zama yayi ya bani a nutse har na koshi, sannan ya duba Pcm ya bani nasha sannan ya gyara min kwanciya.
....... Da yamma ina kwance dake zazzaɓi ya rufe ni sai ga Aunty Maryam da Aunty Fatima, suka zo. Sun gama hiransu zasu tafine suka shigo ɗakin, tashi! Nayi na zauna ina murmushi Aunty Fatima tace.
     "Hajja Khadi! Kin kyauta, da saka iyayenki a damuwa, ce miki Ya Bamai shima son wannan sarautar yake ne, ko ance miki bai san mi yake ba. Tun bayan ɓ'atar ki ban sake ganin kwalla a idanun ɗ'an uwana ba sai yau akanki, kinsan illar fushin iyaye kuwa, ko ance miki bazasu kai ki gurin mutumin da kike hauka akanshi bane, duk soyayyar da muke miki yau munji bata da wata amfani sabida ke ba Y'a tagari bace, duk Y'a ta gari bazata faɗawa Iyayenta bata sonsu ba. Nafisatu auren dole aka mata bata son Ya Bamai, amma haka ta zauna dashi. Makirci babu wanda ba's mata ba, a haka ta zauna da shi shine kike ce musu bakya kaunarsu, ki kwantar da hankalinki zasu kaiki gurinsu tunda su waɗa'ncan sunfi iyayenki."

   Tana gama faɗar haka suka bar min ɗakin, kuka ne ya kwace min. Wato har abin ya kai haka.
             ..... Kwana biyu tsakani sai binsu nake ina basu hakuri basu ce min kala ba, abincine dai dakanshi yake kawo min har ɗakina dan Mamie tayi rantsuwa matukar nazo gurin cin abinci bazata ci ba, fushin da take dani har yafi na Dadda.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now