4

5.9K 419 17
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu....

           _Toh banda abinku Yar Gidan Yaddiko ta tsani gasa_
4
     Najibullah Imran shine cikaken sunan Ya najib Mahaifinshi ne Custom, yana zaune a abuja. Autan Yaddiko kenan. Ya najib yana da kanne mata uku, Shamsiya, Sai Samha da Kubra.

              Yana karatun degree ɗinshi na biyune a jami'ar khartum nakasar Sudan, shi da Ya Maheer.

                A burin Iyayensu su haɗasu auren zumunta, dan za'ayi baikone tare da bikin Yar Hajiya Sadika.

      Inda aka haɗa Ya Najib da Binta Yar wajen Hajiya Aisha, sai Maheer za'a haɗa shi da Sailuba Yar gurin Hajiya Sadika, duk sai sun karasa karatunsu za'ayi bikin.

        Yanzun ma hutu suka zo shine aka turosu mutafi bikin kafin a fara.

Ya Najib yana da hakuri da kawaici ga kara, shi mutum ne na kowa bashi da wata damuwa, a duniyarshi kuma bai da aboki sama da Maheer, ga rikon addini dan yana daga cikin ɗaliban makarantar gwalaga, matashin ɗan ahli sunnah. Wanda ya haɗa ilimin Addini da na boko. Yabi jikinshi da jininshi ko wandonshi ka kalla zaka tabbatar da haka.

........Maheer Ibrahim cikaken sunanshi shima jikan Yaddikone, miskili babu ruwanshi da kowa, ba ka taɓa gane gabanshi balle bayanshi, Yana da kane biyu. Ammar da Hafsa.

     Ba ruwanshi da shirgin mutane, asalima idan da cinkoso a guri fita yake yi.

        Mahaifiyarshi Zainab Yar nabardo ce, babantane hakimin can.
             Maheer da Najib suna karatun likitancine, Maheer ta ɓangaren mata da kananun Yara, Najib kuma Likitan zuciya ne,  komi nasu ɗaya sai dai banbanci halaya, Maheer yana shan taɓa. Najib kuma ko warinta baya so.

          ......Hajiya Sadika tana da Yaronta irin marasa jin nan dan yana cikin matasan yan sara suka, Faruq ya addabi Yan unguwarsu kandahar zuwa bakoro dan ma mahaifinshi bai kyaleshi haka ba.

        Hajiya sadika tana da yara bakwai Faruq, Sailuba, Alawuya, Habibu, Laweeza, Firdausi, Sai Ahmad.
        Yaran Hajiya Aisha kuwa, biyar ne.
    Binta, sai Fauziya, Wasila, Nuhu. Da Jamila.

       Wannan sune jikonki Yaddikona idan aka tara nidi kuma har da aminaina dan suma na kala musu dangantaka da Yaddiko(😎)

          ...... "Maza saka kayanki muje ni za'a gayawa zuciya daɗin abin kafin ya zama kansila nan yake zuwa amsar bashina har yau ina binshi dubu goma, ɗan banza hala sai a lahira ya biya."

         Dariya nayi na washe hakorana, saka kayan nayi, zamu fita. Ya Najib yace.
"Ai Yaddiko kika kuskura kika saya mata kayan nan tabbas mayune zasu cinyeta, dan jiya nayi mafarkin indai ba ɗauketa akayi daga garin nan ba. Toh ba shakka turen aljani zasu mata, da kuma nayi istahara sai naga tabbas zasu lashe miki shatuwarki ke burinki bai cika na niman Iyayen...."
.     "Kaiii Najibullahi karka karasa, Yar yaddiko kinji abinda malam Najibu ya faɗa muhakura idan muka je bauchi na saya miki kinji Yar nan."
   Komawa gefe nayi na fasa ihu, tare da zuɓewa kasa ina kuka. Mai cika kunne.
    "Wayyo na higa uku na lalace, hikenan an fasa min kayan turawa, toh Kwarankwatsa. Tsirara zanyi yawo."
              Daga Yaddiko har Ya Najib sun ruɗe, rarrashina suke amma ina botsarewa.
         "Duk wanda ya fasa yawo tsirara a gidan nan ya rena kanshi, idan kin isa ki gwada na gani sai na miki zanen dodo a jikinki."
   Ya buga min tsawa da har gagi, bansan lokacin da na shige jikin Ya Najib ba, tare da sauke bahagon ajiyar zuciya.
     D'ago ni Yayi yaga idanuna sun kafe.
           D'ago kanshi yayi yace.
"Man ta suma fa."
           "And So what." ya shige abinshi, ai jin batun na suma Yaddiko ta bishi ɗakin cikin balbalin masifa tace.
"Mahar kaci ubanka wancar katon tsawar da ka buga mata, da izinin waye, munafuki dama kazo kashe min itane.."
     Shiru yayi ya juya mata baya, a waje kuwa ruwa, Ya Najib ya shafa min.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now