26

4.9K 460 39
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.26
          Cike da bakin ciki Mama kalli Yaddiko, sannan ta zare hannunta akanshi tace.
"Idan ya mutu kema kin huta, Yaddiko laifi tudune kin hautaki kina hango na Maheer, bayan tare kuka tozarta Yarinya nan, idan maheer ya mata bazata ji zafinshi kamar yanda ke da kika riketa kika faɗa mata magana ba, zata iya jure fushi da kowa amma banda naki, kika nuna mata cewa ai ita ba naki bace kodan Albarkacin rokon da kika mata tabar Jikarki, yanzun da gari yawaye shine zaki juye mishi laifinda kuka aikata, shi kenan ya mutu...."
    Tana gama faɗar haka ta wucce sama ta ɗauko jakarta tare  ɗauko hijab ɗinta sannan ta sauko fita tayi ta kira Najib da Ammar, a tare suka shigo gidan.
        Jikin Yaddikone yayi mugun sanyin tunda har Mama ta iya ajiye kawaicinta ta faɗa mata magana sai take jin masifar kunyar Maman dan tsakani da Allah ta maida laifin kan Ya Maheer.
                  Babban asibiti aka nufa dashi inda Najib da wasu likitoti suka rufa akanshi dan ceto rayuwarshi.

               *****
A maiduguri kuwa bazan iya ɓoye farin cikin da muke ciki ba, sabida yanda mutane suka nuna kaunarsu a kaina da kanena.
         Sai dai a haka Mamie tace nayi baya baya da kowa.
      Muna zaune zamu ci abincin dare, amma ni zuciyata da ruhina yana bauchi. Juya cokalin nake Ya Maheer yana yawo a koina najikina, mikewa nayi na bar musu abincin.
            Bina Mamie tayi da ido tace.
"Yarinyar ta faɗa son wani ne fa."
     "Haba dai tayi karama da so ko aure." ya bata amsa.
            Zaga gidan nake ina kallon yanda aka wadata shi da hasken wuta.
           Ina tafiya tare da shakar kamshi queen of th nit, wutar gidane ya ɗauke na juya zan koma, naji anyi sama dani tare da rufe bakina.  Ihu nake tare da cilla kafafuna, hannun da aka rufe bakina ne akayi rashin dace yatsar hannun ya shiga bakina take ta gantsara mishi cizo.
      Yarfe hannun yayi na kwalawa Dadda kira da karfi.
          Sake rufe min bakina akayi aka shiga niman turani cikin flower zai haye kaina.
                    Bansan ya akayi ba, naji mutumin ya fasa ihu dan yana kaina, ne ɗago shi Dadda yayi tare da kara rufeshi da duka, sosai sannan ya cire abinda Ya rufe fuskarshi da ita.
       Cak Dadda ya tsayar da dukanshi yace.
"Kanna! Y'ar cikina ka biyo ka lalata min ita? Kenan shekarun baya kaine na kama a ɗakin Nafisatu? Bayan zuwan farko da kayi, Kanna mai na tsare maka ne? Mai na hanaka samu, Yarinyar da kake da sa'arta kabiyo Kanna. "
    Bakin ciki ya hana Dadda karasa magana, sai lokacin Mamie ta iso dan tana tsoron karta fito wani abu yasami yaranta, sai ta goya su, da abin goyon turawa tafito ganin yanda Dadda ya rike Kanna yasata turusss.
              Waiwayawa tayi inda nake kwanci cikin flower, na kifa kaina a kasa ina shashekar kuka.
     Jikinta na rawa ta iso inda nake, ta saka hannunta tare da ɗagoni, cukwaikuyeta nayi tare da sake kuka mai karfin gaske, ga gaban rigana a yage kallon Dadda tayi wanda yake rike da Kanna a hankali ta iso gabanshi tana kallon fuskarshi da yaki su haɗa idanu tace.

   "Abubakar!...Y'ata akazo lalatawa fa, kuma bakayi wani Abu akai ba. Lokacin da aka min baku ɗauki wani mataki ba, yau ga Y'arka da...."

       Jan Kanna yayi cikin ɓacin rai ya fita dashi har gidan Sarki Umar. Ya shiga dashi ya watsar a falo a gaban sarki da Iyalanshi.
             Cikin mugun ɓacin rai yace.
"Wallahi Umar! kazama shaida zan kashe Usman  har lahira, miye matsalar shi da iyalina. Abinda ya faru baya aka hanani magana tabbas zan aikata komi dan kare rayuwar Y'ata, yayi na farko yayi na karshe idan kuma ya sake kwatanta wani abu zan baku mamaki."
    Yana gama faɗar haka ya juya yabar falon ranshi a ɓace.
          Cikin ɓacin rai Sarki Umar yace.
"Wallahi kayi asara, wai kai baka da wata damuwa sai nason cutar da ɗ'an uwanka, toh ina faɗa maka ka bari Bamai yasan da saka hannunka gurin sace mishi Y'a wallahi takare maka dan sai kotu ta rabaku da shi, kafita hanyar iyalinshi gaka kaine babba amma kayi girman kwabo."
            Cikin borin kunya ya mike tare da cewa.
"Dan anga banyi zurfin ƙaratu ba sai a maidani mutumin banza, shine zai min sharri toh wallahi zaiga abinda zai faru da y'ar tashi."
       Yana gama fadar haka ya fita daga gidan yana tonawa kanshi asiri.
               *****
     Tunda Mamie ta maida ni ciki na birkice mata, nifa su kaini gurin Yaddiko. Sosai a cikin daren na ɗaga musu hankali.
           Washi gari akayi raɗa sunan Yara, duk shagalin da ake nak'i fita ko waje. Asalima rufe kaina nayi a ɗaki,  ana sallar azhar aka maidawa Dadda sarautarshi, ana murna Mamie ta buga min kofa takawo yaranta muka zauna, dan itama tsoro take ji kar akuma mana illa.
             Bayan an watse aka sake shirin zuwa dinner, dakyar na yarda nabisu. Inda Aunty Maryam suka zabo min, wani gown blue. Aka min kyalliya dukda haka bana cikin farin ciki da jin daɗi dan duk lokacin da na tuna abinda ya faru, tsorone ke kama ni sosai.
                .......
Cikin rashin ɗa'a ya kalle mahaifiyanshi yace.
"Wallahi zan kashe Bamai a yau, dan wanzuwarshi yasa aka ki bani sarautata."
           Tsaki tayi sannan tace.
"Ai bazaka taɓa samun wannan damar ba, sabida ce maka nayi akashe Yarinyar idan aka saceta shine zai baka damar samun mulkin amma kace a b'atar da ita."
          "Umma yau zan karasa aikina nima na huta." ya faɗa a hasale.
            ......
    Dukkansu sunyi cirko cirko a bakin kofar emergence, sai suntiri suƙe, ba kamar Yaddiko wacce tafi kowa shiga damuwa....

      A sanyayye Najib ya fito, wanda shima karfin hali kawai yake, da za'a buɗe jikinshi babu jinin a cikinta sabida kaɗuwar da yake ciki, sakamakon matakin da Maheer yake ciki.
              Wasu likitoti ukune suka fito suma jikinsu a sanyayye, dan Allah kaɗai zai iya fiddashi daga halin da yake ciki basu ba. Dan zuciyarshi kumbura tayi.
            Kowannensu wuccewa yake kanshi a sunkuye. Cacumar Najib Yaddiko tayi cikin tashin hankali tace.
"Haka zaka min Najibu baza taimaka min, ɗan uwanka ya tashi ba."
    Kwace kanshi yayi tare da jingina da bango yace.
"Ɓazan iya mishi komi ba yaddiko bazan iya bashi lafiya ba, kowani cuta da maganinshi Maheer maganin cutarshi Aisha.."

           Kuka tasaka tare da rike kanta tana faɗin.
"Na cuceka mai sunan malam na zalince ka, zamana cikinku baida amfani tunda nagaza sama muku farin ciki."
                Haka sukayita kokawa halinda yake ciki.
        *****
    Hidimar taro ake amma sam hankalina baya kai, zuciyata kewar Ya Maheer take, bansan ya akayi ba na zare jikina na tafi ban ɗaki.
     Duk akan idon Mamie,  ina shiga na buɗe famfo na fashe da mugun kuka, tare da zubawa mirron ban ɗakin ido, kuka nake kamar raina zai fita sabida tsabar kewarshi ji nake komina ba'a cike yake ba, haka kawai zuciyata take hango min su Dadda basu min adalci ba.
  Buɗe kofar ban ɗakin akayi dukda nacewa masu tsaron karsu bar kowa ya shigo.
   Juyawa nayi a tsorace, mamie ce ta shigo tana jingina bayanta a jikin kofar ta zuba min ido, buɗe hannunta tayi na karasa da sauri na faɗa jikinta, nace.
"Mamie ina kewa..."

         "Shiiii! Kina kewarshi ba, yau shine ake kewarshi Yaddiko fa?"
          Kifa kaina nayi ina dariya mai haɗe da kuka na buɗe baki zance wani abu, tayi saurin cewa.
"Kina sonshi ko?"
         Girgiza mata kai nayi cikin wauta da ɗanyen yarinta nace.
"Bana sonshi kawai ina kewarshi ne, da masifarshi."
     Dariya na bata tayi murmushi tace.
"Gaskiya kina kewarshi kam tunda gaki a toilet kina kuka, kuma babu so a ciki, sorry my luv zo muje ku gaisa da mutane."

      Abinda na fahimta mamie manna min hauka tayi tasani wnk fuskana muka fito nan aka shiga gabatar dani, a gurin manyan mutanen da aka faɗa musu akurarren lokaci.
                   Cikin haka muka isa mazaunin gwanar borno, inda aka gabatar mishi dani, ba tare da wani damuwa yace yana nimawa ɗ'anshi mai suna Naufal da yake karatu, a Ukrain.
              Murmushi Uncle Ibrahim yayi yace.
"Toh Y'armu dai, ba yanzun zamu aurar da ita ba, sabida zamu turata riyad karatu."
      dake gwanar abokinshine, tare sukayi jami'a zaria.

               Haka dai muka cigaba da gaida manyan mutane, duk haushi suke bani, kamar na rufe kowa da duka, karfi da yaji ana wani gabatar dani sai kace dole.
      Koda muka koma mazauninmu Yan matan familynmu suka shiga zuwa min tare da gabatar da kansu.
         Amsa musu kawai nake, har aka tashi hankalina baya jikina so nake na keɓe ni ɗaya nayi kuka.
     Muna dawowa kuwa tunda na shiga ɗakina, nasaka key nake rusa kuka. Rungume teddy nayi ina jin kamar zuciya zata fita sabida kewar Ya Maheer, da Yaddiko.
          ****
      Dakyar Abba ya lallaɓa yaddiko ta dawo gida....
      Sailuba kuwa kamar zatayi hauka, jin dalilin shigar kamar mahaukaciya ta dawo gida, tana kuka, ganin babu mafita ta nufi gurin mahaifiyarta domin niman mafita.
        **** 
    Washi gari nak'i fitowa dukda yanda Dadda yake buga kofar na fito da kumburarriyar fuskana idanuna yayi fulufulu......
  
*CELE QUEEN💁*
       

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now