7

5.4K 411 27
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

_Mommyn Sayeed da Noor, goyan bayan Mayyer fa kike, toha kiyayye Mai nima_😂

*Fatan alkhairi gareku, Ayusha Abraham, Rukayya Umar Mom Nur, Najida, Hafsat Abubakar, Tare da wanda ban kira sunansu ba da fatan zaku cashe a sabon wakarmu mai suna tunkwal a rawan wutsiya_😎

Page 7
Murmushin mugunta na sake lokacin da nafito falon ina, yar tsallen nasara.
Tsura min ido yayi, na ganshi sarai na saka nayi kaman bansan da mutum a gurin ba na fita a gidan, shiru yayi yana nazarin dariyar da nayi.
*Wannan Yarinyar iblishiya ce, sam bata da nutsuwa*
Abinda yayita aiyanawa kenan, can kusan mintina goma da fitata, sailuba ta fasa ihu tana sosa jikinta.
Mikewa yayi ya sameta ta kwaɓe rigarta, tana ihu da hauka.
Komawa yayi da baya yaja mata kofar dan yanda take babu kaya baxai yarda yakai mata taimako ba, gudun faɗawa tarkon shaiɗan.
Fita yayi gurin Yaddiko ya faɗa mata, aikuwa ta taso jikinta na rawa, suka nufi cikin gidan dan Mama bata nan, taje sunar Yar kawarta a Tafawa balewa Estate ita da Hafsat.
Yaddiko na shiga ɗakin, tasameta tumbur tana ihu da sosa jiki, sororo Yaddiko tayi cikin jin haushi tace.
"Ke ! bana son shegantaka mike damunki?"
"Kaikayi Yaddiko! Sosa min baya, wayyo kirjina, nan ba can ba. Na shiga uku na lalace Yaddiko ki taimake ni."

Toh dake Yaddiko bata kawo cewa karara bane, sai tayi tsaki tare da barin ɗakin.
Kuka tasaka ta ihu.
......Dan gulma sai gani na sake zuwa, yana falo a zaune na shigo. suna magana akan kaikayin nazo ina raba idanun nace.
"Yaddiko mike faru?"
Watsar da Hannunta tayi bayqn tayi tsaƙi tace.
"Wancar shashashar ke mana hauka mana"
Nuna min ɗakin nayi kaman ban da masaniyar komi na shige ciki.
Kaɗa kanshi yayi, yana girmama kundin rashin kunyata.
Ina shiga na ganta gatsuuu kamar gayar tuwo.
Rike k'uguna nayi nace.
"Yaseen ina da maganin kaikayin karara amman sai kin min rawan, asosa."
Kamar zata tayi hauka ta gyaɗa min kai, nace.
"Toh ai hikenan, amma kisani dole ki min rawa sosai da amshi."
Shiru nayi na rasa wani waka zan mata kawai nace.
"Kawai ki min rawan kaikayi"
Juyawa tayi tana kallona kwalla na zuba a idanunta ta fara rawan kaikayi.
_Kaikayi-Kaikayi-Kaikayi_
Yo fansa zan ɗauka sai da naga tana kuka wiwi na fecce a ɗakin na kalli Yaddiko nace.
"Yaddiko ki mata a gaji da toka da manja Kwarankwatsa Karara ta kwaso garin hegen Iyayinta."
Ina gamawa faɗa musu na fita da gudu zuwa gurin awakina,
Ina shiga na fashe ds dariya nace.
"Yaseen na ɗauki fansa, ku tsaya na na baku labarin abinda ya faru."
Nan na kwashe duk abinda ya faru na faɗa musu, "Sannan zamuyi wakar tunkul tunkul rawan wutsiyarsu.

_Tunkwal - Tunkwal rawaɓ wutsiya kowa ya iya ya huta_
Aikuwa suka zuba kofatarsu a kasa yabada tunkwal tare da kaɗa wutsiyarsu, nan na cigaba da wakata.
_Nima na iya na huta_
Yoni ai ba wutsiyarce dani ba sai na kaɗa musu Yar k'uguna,
_Tunkwal_
_Uwar garke ta iya ta huta_
Sai da tayi tunkwal sannan ta kaɗa wutsiyarta.
_Faratu ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_D'an maraya ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Sangami ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Yar Kyamus ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_Iyale ma ta iya ta huta_
_Tunkwal_
_D'an duna ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Talle ma ya iya ya huta_
_Tunkwal_
_Yan biyun Faratu ma sun iya sun huta_
Tsallen sabin jarirai suka min.
_Allah ya barni da ku na huta_
_Tunkwal_
_Allah Ya kahe makiyarmu mu more_
_D'an bakin ciki ya fecce_
_D'an bakin rai ya sheka_
_Mahassada su kone_
_Masu kaunarmu mu so su_
"Toh Aljana Yar madabo zaki zo kiwucce ki sai nakira Mahauta sun yanke min kawunan shaiɗanun dabbobinkin da ba'a cinsu sai kiwo."
A tsorace na juya, tare da raɓa gefenshi na wucce, rakani yayi da harara. Yana mai buga tsaki.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now