12

5K 452 34
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Ga pagen kunan My Watpad Fans nagode sosai,😍

Page.12
Ana rufe min baki suka shaka min wani abu, wanda shi ya gusar min da hankalina a jikina.
Da sauri suka wucce dani bayan zaranda, suka kaini.
Ajiye ni suƙayi a gaban faruq, wanda yaketa lasar bakinshi.
"Oga kaci ka rage mana muma mu ɗanna, wallahi hannuna da ya taɓa kirjinta karka ji lau....."
Ɗirka mishi naushi akayi, ya juya kan nakusada shi ya ɗirka mishi shima, nan faɗa ya nemi kacamewa tsakanin.
Dirowa Faruq yayi yana dariya, yace.
"Shegu aljanuntane suke cin ubanku, bari kuka abinda na shirya. Dan na gama tsara komi saura na baje yar nima."

Fitowa yayi da wani abu ya watsa a gurin, take guguwa ta tashi dariya yayi sannan yace.
"Sunan can, suna shagali muna nan muna namu."
Zuwa kaina yayi yana sauke numfashi.
*****
An kira angwaye da amare, koda yafito kallon agogonshi yayi, kamar wanda aka ingizashi ya fita a filin.
Da wani irin sauri, yana tattare rigarshi.
Yana fitowa yaga yarinyar da tafita dani, riko hannunta yayi suka fita waje, baiyi wata wata ba ya tsinka mata mari.
"Ina yarinyar da aka turo ki ki ɗauƙa."
Jikinta na kerrma tace.
"Sunyi baya da ita."
Bai saketa ba ya isa gurin masu tsaron hotel ɗin ya faɗa musu. Take suka kira Yan sanda.
(duk wanda yasan zaranda hotel yasan akwai ofishin yan sanda a kusada hotel ɗin.)

Ganin zasu ɓata mishi lokaci ya nufi gurin da yarinyar ta faɗa mishi da sauri har yana tuntuɓe.
Tafiya ce mai tazara, ya sha karamar wuya kafin ya isa gurin, ya hango su.
A hankali ya taka har inda suke, saka hannunshi yayi a aljuhu ya zaro sigarinshi ya kyasta leta, take wutar ta kama.
Zukar ɗaya yayi mata ta kare tass.
"Wato dana maka kashedi akan Ummi Aeesha baka ji bako? da nace kafita hanyar Humaira baka ji ba ko? Hmm ynx zaka gane baka da hankali."
Ya nufi kan faru,aikuwa yan daban faruq. Suka taso mishi da wuka.
Sarkin yawa yafi sarkin karfi, dan haka suka rufe shida duka sukayi tare da yanka shi a gefen cikin shi da kuma dantse hannunshi.
Faruq kuwa hankalinshi kwance ya rabani da rigar jikina, tare da kananun kayana,, ya rage daga ni sai under, ɓalle bra ɗina yayi. Kifa kanshi yayi a kaina tare.
Sai saukar naushi yaji a fuskarshi sai da ya hantsila, a lokacin yan sandan suka iso gurin.
cafke yan daban sukayi, Ya Maheer ya taso dakyar sabida jinin dake bin jikinshi, ya cire babban rigarshi ya lullub'a min,
Kafin ya koma kan Faruq ya rufe shi da duƙa, kamar mahaukaci. Dukda faruq a sume yake. Haka bai hana Ya Maheer masa wani kafirin duka wanda yasa shi sai da ya farka, sabida dukar ma'aikatar sadarwan da Ya Maheer yayi.
Dakyar Yan sanda suka kwaci Faruq, kaina Ya maheer yayi ya ɗauke ni yana kallon fuskana.
A hankali ya juya dani, lokacin har an bazama nimanmu.
Jiri ke sashi haɗa hanya m, dukda Yan sandar sun nime ya basu ni amma fir yaki. Suna fitowa sai ga abokanshi da Ya Najib sun iso gurin dake masu tsaron gurin yaje ya faɗa musu.
Da sauri Ya Najib ya isa gurinshi tare da mika mishi hannu ya bashi ni.
"Kayi hakuri babu kaya a jikinta. Ka buɗe min mota nasakata."
Ba musu Ya Najib ya buɗe mishi mota yasani, juyawa Ya Najib yayi yaga yanda Yan sanda suka caccumo, faru hancin shi da bakinshi yana fidda jini, ga fuskarshi da tayi wani irin baki.

Asibiti Ya Najib ya nufa damu, lokaci zuwa lokaci Ya Maheer yana leka fuskana da nake famar barcin magani.
Shima kuma jinin yake fiddawa, dan ko iya buɗe idanun shi baya yi. Muna isa asibitin Ya Najib ya fito zai ɗauke ni ya rike hannunshi.
"Don Allah karka taɓa ta, zanji ba daɗi."
Ya faɗa mishi,
"Akan me bazan taɓa ta ba? Nifa aurenta zanyi kai kuma naka a wanne, dalla matsa min na ɗauketa ka fara wucce iyaka, akan haka kuwa duniya zata iya jinmu."
Ture Ya Maheer yayi ya buɗe motar zai fito dani. Ji yayi ya finciko shi yace.
"Karka taɓata nace, na haɗaka da Allah."
Bai kula shi ba ya tunkuɗe shi sai da ya faɗi.
Kamar mayye haka yasake mikewa yazo ya tare Ya Najib yace.
"Kabar min ita na ɗauketa, babu kaya a jikinta najib kai ba sonta kake ba, shirme kake akanta ka bari Yarinya tasan ciwon kanta ta bi abinda ranta ƴake so."
Ganin bai kula shiba har ya fito dani, yace.
"Ok kayi abinda kaga ya dace amma ina faɗa maka ko mutuwa zakayi bazaka taɓa aurenta ba. Dan Mahaifiyarka ta gama cusa kiyayyarta a zuciyar Aisha, kuma tayi mata gargaɗi da ta fita harkanka. Ni na hanata ta faɗa maka ko ta sauya maka, idan kuma kana ganin karya ne ka tambayi yarinyar zata faɗa maka."
Cak Najib ya tsaya tare da juyawa yana kallon Maheer, a hankali yaiso gabanshi ya mika mishi ni.
"Tun yaushe haka ya faru banda masaniya?"
Najib Ya tambayi Maheer, "bansani ba amma idan kana son jin bayano ka tambayi binta."
A hankali yake takawa ga wani uban jirin da yake ɗibanshi.
Jikin Ya Najib a sanyaye yake bin bayanshi har emergence.
Cikin gaggawq aka amshini a hannunshi shima kuma aka shiga dashi wani ɗaki dan kula,da lafiyarshi.
.........
A can kuwa rikicine ya ɓalle tsakanin Hajiya Sadika da Mama, inda ta shiga cin mutuncin mama a gaban mutane.
"Dan tsabar mugunta da sharri, akan yarinyar da tasaba bin maza, shine Maheer zai kashe ɗan uwanshi, yarinyar da bata da asali balle tushe. Wallahi dani aƙe zance dole yarinyar tabar gidan nan ko kuma.."

Dake Mama bata da niyyar tanka mata, motar Ammar ta shige tace ya kaita asibiti.
Kafin wani lokaci an juya zance ya koma cewa faruq ya kamani da Ya Maheer, turmi da taɓarya. Abin dariya ita hajiya sadika ta manta da cewa Yarta maheer yake aure, kuma sunanta take ɓatawa tunda ɗan ɗan uwantane.

Karshe rikici ya ɓalle da taimakon zugar Umman Najib, da wasu kawayenta.

Mama da Najib a asibiti suka kwana ita a gurina nikan ba'a min komi ba sai ruwa da aka samin da allura mai karfi wanda zai kashe karfin abinda suka shaka min.

Da misalin karfe bakwai sai ga Abban Ya Maheer yaje har ɗakin da yake, a lokacin ya tashi ma yana shan tea wanda Baba altine takawo mana, na karyawa.
Zama Abba Yayi yana kallon raunin dake jikin Maheer yace.
"Mi ya faru jiya? Hankalina ya gaxa kwanciya."
"Ana cikin tarone naga wata Yarinya tafita da Aisha, kuma bayan wasu mintoti bata dawo ba."
Shiru Abbanshi yayi yana kallon shi, kafin yace.
"Toh amma kuma Sadika tace, sau biyu Sailuba tana kamaka da Aisha, ni hankalina baya kwance tunda maganar ya isa kunnen Yaddiko bata ce komi ba tace dai a dawo mata da Aisha zasu koma gumau, dan tunda suka zo bauchi suke haɗuwa da tashin hankali."

Sauka yayi daga gadon ya ɗauki rigarshi yasaka, dukda baya jin daɗin haka, cewa Abbanshi yayi.
"Babu amfanin zaman asibitin, kawai muje gidan"
.......
A waje kuwa zuwan.Umma Ya najib taja shi suka fita, cikin ɓacin rai tace.
"Najib!!! Ni wacece a gareka."
Kanshi a sunkuye yace.
"Mahaifiyata."
"Toh Madalla, idan nice na haifeka kar nakuma ganinka a gurin Aisha, in kuma naji labarin haka toh ban yafe maka ba."

D'ago kanshi yayi a sanyayye yace.
"Umma! sonta nake fa."
Kamar zai fashe da kuka,
Hararanshi tayi tace.
"Toh, ban isa dakai bane. Wato ban isa nace ga abinda nake bukata ba, shi kenan kaje na...."
"Don Allah kiyi hakuri naji zan fitan."

Tana jin haka tasaƙe murmushi "ko kaifa. Allah yayi maka albarka."
Komawa tayi cikn asibitin yabita da ido zuciyarshi na zafi, ashe da gaske ne abinda Maheer ya faɗa, shikenan Umman shi ta katse mishi farin cikinshi.
.........
A d'akina nima na farka, dake an kawo min kayana mama ta tattara min gashina ta haɗa min ruwa nayi wanka, ina fitowa tabani abin karyawa.

Ina cikin karyawa ne, Ya Maheer suka shigo tare da Abba gaishesu nayi, Abba yake tambayana ya jikin nace da sauki.
Kallon tambaya Abba yayiwa Mama, murmushi tayi tace.
"Ai babu abinda ya faru, sai dai tana mitan kirjinta na ciwo."
" Ok yanzun zamu koma gida ai."
Niman likitan Ya Maheer yayi suka magantu, daga nan aka bamu sallama.

........
Koda muka isa, gida wani irin mugun rikici akayi wanda har Ya Maheer ya furta ya saki Sailuba, abinda ya kara ruru wutar rikicin.
Yaddiko tace babu wanda ya isa ya, yayi mishi dole ya maida ita, tunda dole aka mishi ya zauna da ita, sannan abinda Faruq yayi sannan Allah sai yabi min hakkina, kamar yanda ya nemi keta min haddi insha Allah tasa a ranta sai anwa Yaranta tunda itama Yaran mata tana gani, akan idanunta za'a mata abinda faruq yayi min.

Dakyar Abban Ya Najib yasa Ya Maheer ya dawo da Sailuba.....

Ku min uzuri........ Am tired

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now