35

6.7K 688 99
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.35
________________________________
       _Wannan shine pagen da zanyi muku shi na karshe da Izinin Ubangiji, kuyi hakuri dole ce tasani hutawa har zuwa lokacin da Allah yaso ganawarmu ina bawa duk wanda Alkalamina ko ni kaina na b'ata mishi rai ya gafarceni ya kuma Yafe min ni_
__________________________________

A duk Binta ta kiɗime ta razana da abinda mamah ke shirin fad'a. Murmushi tayi sannan tace.
"Kwantar da hankalinki, Ammar nake niman alfarman ki aureshi. Dukda nasan tsiranku babu yawa, nayi imanin zai riƙe ki da daraja."
      Kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta, tana hasashi yanayin matashin d'an shekaru ashirin da shida, ita kuma tana niman, ashirin da hud'u. Amma idan da zasu had'u Aunty yake ce mata, d'alibin a engineering, kammala degree ɗinshi na farko a jami'ar A.t.b.u, yanzun yana had'a nabiyune kuma ba laifi yana kasuwanci bayan karatu dan shine yake kula da gidan man Abbansu wanda yake Miri da wanda yake Inkil. Matashi mai ji da kanshi, kukan Nanah suka ji yasata d'ago kanta cikin isa Mama tace.
"Wucce d'akinki."
    Ba musu ta shige d'akin cogewa Umma tayi daga baƙin kofa tace..
    "Ke Binta zoki bawa Aisha nono
"
          "Babu ne a kirjinki ki bata mana, na yayeta dan ina son nima nanda kwanaki ta haifa min jikoki masu albarka. Kuma bazata bata nono ba dan bana son D'ana ya aureta da kwantattun nonuwa kije ko bata naki da suke manne da kirjinki"

        Mamah ta fad'a.
    "Ni Safiya bana son fitina taya yarinyar da ko suna ba'ayi ba za'a tsigeta a nono, yaushema najib d'in ya rasu da za'a fara maganar binta tayi wani auren, ni kan ki barta ta bata nono kawai."

         "Sai kiyi kuma." Mama ta bar falon.
          Abu kamar wasa, sai gashi har da Yaddiko da Abban Ya Najib shima da yaji kan magana yace taje ta rike Babyn abin dariya Yaddiko ma ta goyawa Mama baya, dakya Abban Ya Maheer ya tankwara mamah ta amshi babyn Binta ta bata nono.

         ****
  Tunda mukayi magana da Mamie bata sake min magana ba. Amma muna gaisawa da Dadda. Gefe d'aya, kuwa karatuna nake a nutse.
           ****
     Zaune take a gaban Dadda cikin kulawa tace.
     "Daddan Yara!"
     D'ago kanshi yayi ya kalleta sannan ya maida kan karamin littafin dake hannunshi yace.
"Hmmm"
       "Hm dama akan Khadija ce da Annur." shiru tayi tana nazartan fuskarshi a nutse.
    "Ina jikinki." yace mata a takaice,
            Gyara zama tayi tace.
"Tun had'uwarsu acan yake bina da maganar yana sonta, toh yanzun na turashi suyi magana da ita tayi mishi rashin kunya ko zaka saka baki dan har Hajiya Hauwa ta tabbatar min da yasanar da  Zanna."
        Shiru yayi ko shine dalilin da yasa Zanna yayi mishi magana a fada d'azun, takaice ni ya lullube shi ya juya gareta yace.
"Ita yarinyar tace miki ta amince ne?"
      "A'a sai ma rashin tarbiya da ta nuna min ita mijinta take so ko taya zata koma bayan saki uku yayi mata."
           Tashi yayi ya zauna sosai sannan yace.
"Maganar gaskiya yaron nan bashi ya saketa ba, dan haka ki bar maganar Annur idan Yaron yazo ya mu turashi sudan ko idan taxo hutu nakirashi su daidai."

        "Taya haka zai yuwu, bayan kasan zubewar mutuncine sakin mace a cikin masarauta irin haka, yayi hakuri mu bar maganar ta auri Annur."
           "Dani dake waye shugaba?"
     Ya jefa mata tambaya tare da tsareta yayi da manyan idanunshi, alamun babu wasa a cikinsa. Tare da tsuke fuska, sunkuyar da kanta tayi tare da fashewa da kuka shareta yayi ya cigaba da aikinshi, yana jin kukanta dake ya kushin zuciyarshi tare da cizon duk wata zaren azabarin sadarwan jikinshi, take  zuciyarshi ta tunbatsa da tsanar kukanta ya ajiye littafin ya janyota jikinshi. Cikin manyantaka ya samu nasaran goge laifinshi ita kuma tayi amfani da damarta gurin kafa mishi ra'ayinta.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now