6

5.6K 417 12
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu....

        *_Masu Yalwata da zunzuruntu ɗaukaka basu cika damuwa da kiran kansu suna dashi ba, sai dai daga mu'amalarsu zaka fahimci haka, Wannan zance nakine Aunty Gimbiya Allah Ya karawa Mai Martaba nisan Kwana Ya kare zuri'arshi da sharrin masharranta Nagode sosai Kina raina_*

         Sadaukarwa gareki Aisha Alto.
     '''Gabaki ɗaya wannan book ɗin na baki Kyautarshi Aunty Nice'''

                 *Jamila Safyanu, Maman Ihsan, Asma'u ka'oje, Maman Khairat da sauran Member Taskar Mai Dambu ga shafinku amma gaskiya team ɗin Najibullah nake, Mayyer yaci kanshi😂*

____________*Queen Indo nd Deejah A Chiroma, idanunku yafita akan Mayyer😂*

__________________________________
Page...6

Dake yau babu hegen Iyamurin fita nayi makota, na sami wani yaron Me suna Abbati, ya rakani dajin angasawa. Dan naji wai Sailuba zata zo gidan, ni kuma ina cike da ita kamar Yanda tamin duka shekara biyu baya yanzun ni kuma zan ɗauki fansata....
        "Yaseen ni Yar Yaddiko ba gaba da gaba ko tabaya sai an hirya"
             Tunda na lura mayyer baya gida sai na sulale muka fita, kallonshi nayi nace.
"Abbati karara nake so zanyi amfani dashi."
        Zaro ido yayi cikin al'ajabi yace.
"Yar Yaddiko! Karara fa, taɓ wallahi bazan iya tsinko miki ba."
      "Dalla can banza kawai nuna min zakayi na tsinko."
      Gyaɗa kai yayi yace.
"Basai munje angasawa ba, nuje bayan house akwai a can"

     Aikuwa muna nufi bayan house muna zuwa na samu a kasa laidar da na ɗauko nasaka hannuna ciki na ɗauki kararan nace.
"Hikenan banza matsoraci."
       Bai ce min komi ba, ya wucce muka dawo dan yasan sai na makeshi.
     Muna shigowa naga ta sauka a napep dariya nayi, nace.
"Barka da zuwa sansanin Yar Yaddiko."
   Wucceta nayi abuna ko kallon bata isheni ba, har zan k'ule tace.
"Keee Yar tsintuwa."
    Dukda bani da hankali yanzun na fara fahimtar kalmar Yar tsintuwa bata cikin kalma masu daɗi, juyawa nayi, ina kallonta.
       Kallonta nayi daga sama har kasa, sannan nace.
"Yo ba gwara ni Yar tsintuwa bace, ke da baki iya zaman gidan Ubanki fa."

    Ina faɗar haka nayi shigewata, gurin Yaddiko, da take sauraran radio, kular gabanta naja naga tuwon laushi miyar karkashi murmushi nayi najuyi miyar karkashin na fice a falon, nasan duk rintsi sai tazo duba mayyer ban wani ji ɗar ba, nage na zuba miyar a matakalar biyun karshe da kuma barandar.

    Na koma na ajiye filet ɗin, fita nayi naje na kirawo Abbati, Abdul da Fatu, abokaina ne. Na ɗauko taburma muka zauna muna hira bayan na kwaso musu chocolat biskit, chewgum, da sauran kayan ciye ciyen da Ya Najib ya jibge min sai sabuwar Yar tsanata, wacce nasaka mata suna Yar amana da wata dolina, ire iren wannan abun yasa bana maida hankali a makaranta, bawai dan bana fahimta ba sai dan wasan da yaci raina, kuma ba'a sami wanda zai jani a jiki yasani nayi karatun babu takurawa ba.
                 Muna zaune sai gata ta ɗibo kwalliyarta tana kareraya, a raina nace.
*Yar wofi aikina na jiranki*
     
     Kallonta mukayi, tare da fashewa da dariya muka tafa, dan na faɗa musu shirina.
         Aikuwa muka fara cewa.
"1....2....3....4..."
  Yanda take hawa matakalar muke kirgawa, bata kai ga inda ya dace ba, ta juyo ta banka mana harara, tana hayewa, nace.
      "Sauka lafiya mai sunan ifiritaiii."
   A fusace tajuyo ai kuwa santsi ya kwasheta, ta rikito daga, sama dai dai shigowarshi gurin kenan.
  Mukuwa muka fashe da dariya.
      Nace.
"Ni bandamu da sanin asalina ba, da kike ce min Yar tsintuwa, abinda na sani aikina nasan asalinshi dan ba tsintarshi na haka kawai ba, Yaseen kin bugu a mazaunarki da gohinki."
     Juyawa nayi muka tafa ina dariya, ɗago kan da zanyi sai akan fuskarshi.
         Ya naɗe hannunshi a kirjinshi, yana kallona. Yanda nake zaro manyan magana,
   Tsabar na razana fitsarine ya kwace min, idanuna suka kawo ruwa. Lagwaɓe kaina nayi ina share kwalla,

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now