30

5.6K 580 75
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

       *Yaseen comments ɗinku hek'e ni yake ku cigaba da bulbulo cmmnts nd vote ku hai mamakious*

Page.30

        Hannuna nasaka fuskana fasa ihu tare da kiran Dadda, a tsorace drvn ya juyo yaga kuka nake wiwi karawa motar wuta yayi muka isa fada, ko buɗe min kofar ban bari yayi ba na fita inda su Mama fulani ke jirana.
   Na faɗa jikinta cikin kuka nace.
"Ku kaini Daddana da Mamiena"
       Duk sun ruɗe haka muka shiga mota ina rike da takardan sakin a hannuna, har muka isa airport. Rike ni Mama fulani tayi dan ko tsayuwa bana iyawa, muna shiga jirgin na kwanta sharaf, numfashi na na fita da mugun sauri.

             Allah kaɗai ya kaimu maiduguri. Ga manyan motar alfarma da gwanon barno ya bawa Dadda aka zo ɗaukarmu. Ina jikin mama idanuna a rufe. Har muka isa fada, wani irin birkicewa nayi jikina kamar wacce aka lulluɓe da ɗanyen nama, haka muka isa falon Dadda, ina jin muryanshi na buɗe idanuna akanshi na janye jikina daga rikon mama, na isa jikinshi na zube, sannan na ɗago hannuna dake rike da takardan na mika mishi, a hankali nace.
"Ya sakeni Dadda." a hankali numfashina ya shiga fizga kamar mai cutar asthma, rungume ni Dadda yayi sosai, yace.
       "Ku bani ruwa."
    Da sauri aka mika mishi goran ruwa ya buɗe bakin tare da shafa min a fuskana amna ina numfashina ma niman hanyar feccewa yaƙe a jikina, hankalin kowa a tashe, dan dole ya cinciɓeni zuwa waje, duk mai imani idan yaganshi a lokacin sai ya zubda kwalla, sabida idanunshi sunyi jajjur. A hankali yake tafiya yana furta...
"Subhanallhi wabil hamdihi, Subhanallahi Azim" itace abinda yake iya furtawa sabida niman aron juriya da tawwakalli.

                Cikin gida babu wanda yasan abinda ya faru, sai da Mama fulani tashiga cikine ta faɗa musu halin da ake ciki. A fujajjan Mamie tabiyo bayanmu.
       Babban Asibitin maiduguri aka kaini, take likitotti suka rufa min kowa na bakin kokarinshi, ganin an ceto rayuwata.
                 ****
  Lokacin da Mamie ta iso kuka take wiwi, rikota Dadda yayi ya zaunar da ita sannan ya mika mata takardan sakin da na bashi.
    A hankali ta warware zuba idanunta tayi akan takardan, a hankali ta lumshe idanunta wasu hawaye suka zubo mata cikin muryan kuka tace.
"Bamai! Laifina ne fa, nice naki Yarda da k'addaran aurenta, kuma naki amincewa da karamcinsu a garemu, amma Bamai komi mukayi Yarinyar bata cancanci haka ba, dan tayi karama da zawarci. Sha bakwai fa? Idan munyi laifi ita bata cancanci a hukuntata da saki uku ba, nasan nice na jany.."
     "A'a nafisatu! K'addaran Khadija ne, wallahi ban ɗaura miki laifi ba, asalima girman kaunar da kikewa Y'arki yaja haka, Allah ya bata lafiya  kawai."

      Bai fasa tasbihi ba, har awa guda ya shuɗe. A awa nabiyu ne liƙitottin suƙa fito tare da sharce zufa,  Mikawa  Dadda hannu babban likitan yace.
"Alhamdulillah, zamu iya tafiya ofishina muyi magana." binshi Dadda yayi har cikin officer ɗin. Nunawa mishi kujera yayi ya zauna, cikin nutsuwa.
      Buɗe file ɗin dake gabanshi yayi yan rubucce rubucce sannan ya zare glass, cikin nutsuwa yace.
"Sir! Yarka zuciyarta ta kusan fashewa, sakamakon firgita da tsoratan da tayi, jininta yayi mugun hawa. Dan har yakai 320 amma Alhamdulillah, cikin ikon Allah munyi kokarin juya akalar alamarin. Don Allah a kiyayye abinda zai sanyata tashin hankali."
            Rubutu yayi ya mikawa Dadda godiya yayi, sannan ya fita.. Ya dawo ɗaƙin da aka ƙwantar dani.
     Sam baya jin daɗin abinda ke faruwa akaina toh ya zaiyi, matuƙar ya nuna damuwarshi toh kamar ya tunzira Mamie ne.
        .....
   Ban tashi farkawa ba, sai karfe sai karfe biyar na yamma har an sake min wani ward inda babu hayaniya balle surutu, ɗakin ya gaji da haɗuwa dan babu abinda babu a ciƙi daga tv da frezee, har ac komi dai ba laifi a dakin ga curtain da manyan cushion.
            Ƙaƙarin miƙewa nayi.
  "Koma ki kwanta jikinki da saura tukun."
         Lumshe idanuna nayi ina son manta da abinda Ya Maheer yayi min amma ina, kamar akan brain ɗina aka rubuta. Abubuwa ne suke shigowa da fita a cikin brain ɗina. A hankali nake kuka tare da kauda kaina, shigowar Mamie tare da yan uwan Dadda yashi mikewa zai koma gida.
       Yana fita suka shiga rarrashina, dakyar nayi shiru ina sauƙe ajiyar zuciya, mikewa nayi na zauna tare da cewa.
"Zanyi sallah."
         Tashi Mamie tayi ta kalli ruwan ya kusan karewa, danna kararrawa kiran nurse tayi can sai gata tazo.
          Cire min ruwan tayi, dan har ya kare, a hankali nataka zuwa ban daɗi nayi alola na fito sallah nazo na gabatar. Zama nayi sosai ina addu'a karshe na fashe musu da kuka.

          Jikin Mamie yayi sanyi, dawowa tayi kusadani. Ta janyoni inda na cigaba da kukan.
....... Dakyar nayi shiru, bayan sallar isha aka sallame ni, tunda na dawo na koma ɗakin Mamie, duk wani kulawa ta tattara ta ɗaurawa kanta,

        ****
   Washi gari aka tashi da bikin naɗin sarautar sabon shehun barno. Sosai akayi shiri gashi an zuba jami'an tsaro.
    Ana gama bawa Dadda sanda da wukar yanka, aka tada hayani tare da harbe harbe, cikin ikon Allah aka samu nasaran cafke tsagerun, akayi awon gaba dasu. Sannan aka cigaba da shagali.
        An gama taro cikin koshin lafiya, daga cikin Yayun Dadda da suka zo har da Gimbiya Zaituna. Da zata koma sukayi magana da Dadda,  bayan tafiyarta yasa aka shiga nima min, takardun visa zuwa Sudan dan acan suke da mijinta da Yaranta.
               ****
  Sati ɗaya tsakani aka tattara min shirgina, zuwa sudan har da shi ɗin, muka mamie kan mun barta da yaranta.

        Tunda muka iso nake share kwalla, har muka isa gidanta dake  cikin masarautar Sudan, cikin mutuntawa aka karɓemu, inda aka shiga hidima damu baji ba gani.

               ..... Kwanar Dadda biyar dan sai da ya tabbatar da an sani a makaranta sannan yayi min nasiyya, sosai sannan yabar kasar, na b'oye ciwon dake raina ne kawai dan iyayena su sami nutsuwa, amma sam bana jin daɗin zuciyata. Dan jinta nake kamar zatayi bindiga.
         ***
   Haka na cigaba da renon damuwata, dan ma Aunty Zaituna tana kokarin ganin na manta komi ga makarantar da nake zuwa, boko da islamiyya, idan na dawo rufe kaina nake nayi kuka har nagodewa Allah, san na rasa farin cikina. A yanzun na yarda da Ya Maheer yayi min illa ta hanyar shayar dani soyayyarshi.
      Ya gama cutar dani, fiye da kima, sam bana jin daɗin rayuwata. Na maida hankaline a karatuna dan kar na zubawa Iyayena kada a idanunsu.
    Yaran Aunty Zaituna, akwai Nimra da Nadia,, sai Amjad da Ra'iz,, sai sa'ata Buhaina.
            Sosai muka saba da ita, dan yanayinmu ɗ'aya. Itake kokarin mantar dani komi har muka shaku, sosai gashi ajinmu ɗaya a boko a islamiyya kuma tafini, Babansu shine wazirin sudan dan, a hankali nake kokarin cire damuwata dan gani nake zata iya kawo min nakasu.,
      K'iyayyar Ya Maheer ya cinye min zuciya bana sonshi ko sunanshi naji raina baci yake.
           .......Muna zaune a falo bayan mun gama game, Buhaina taje kamar zata haye saman cinyar Aunty Zaituna aikuwa ta maketa, ihu ta fasa tare da saka kukan sakalci tace.
"Ammi! Zan faɗawa Abbu, kin bugu autarshi "
      hararanta tayi cikin gwatsilewa tace.
"Autar ko shirme, haba Buhaina ruwan zafi ma baki iya dafawa ba, zanga mijin da zai xauna dake a haka."
   Tura bakinta tayi sannan tace.
"Ammi nifa kibar kira min aure dan tsoronake ji, ga Aunty Nimra tana aure ta zama abin tsoro, haka ma Aunty Nadia, kaii ina kullum kaje gidansu Akhhe basa fita, daga ɗakinsu sai kayita zaman jiransu wallahi idan haka ake auren banayi duk a hanaka sak..."
      "Ke bana son shirmen wofi,tashi kuj..."
         "Assalamun Alaikumun."
      "Laaa! Bro Izzudeen barka da zuwa, Yaushe kazo ya hanya. Ina tsarabata."
   Dafe goshinsa yayi cikin gajiya da surutunta ya kalli Aunty Zaituna kamar zaiyi kuka yace.
"Ammi zan iya komawa gobe, idan ta tafi mkrnt na shigo."

      "Khadijah rike Y'ar uwarki ku bani guri."
           Juya kanshi yayi gare ni, ya tsura min wasu mayatattun idanunshi da nake jinshi har cikin jinin jikina, d'ago kaina nayi muka haɗa ido, cikin sauri na mike tare da barin falon jikina na rawa,  lumshe idanunshi yayi cikin sark'ak'iyar murya yace.
"Ammi! Wannan yarinyar fa?"
  Murmushi tayi sannan tace.
"Yar kanina ce, daga gida tazo tana karatu ne a makarantarsu Buhaina."
       Gani na ba karamin saukar mishi da kasala yayi ba. Irin macen da ya jima yana nima ken.....

  #Izz-Khad
#Aish-Mah
#Naj-Aish        
#Aish-Nur

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now