37

5.4K 576 62
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

*_Amin Ya Allah nagode sosai daAddu'o'inku Allah ya saka da Alkhairi ya kuma bar zumunci_*
___________________________
~ 😂 Allah tsabar yawanku ban san wanda zan bawa Pagen ba wallahi dan ko na bawa wancar wata zata ce mai dambu son kai dan haka wannan na kowa da kowa ne I no remove any one oooo kuyi manegi da littile Ingilise ɗina da irinshi Jennefa ta cigaba😂~
Zauren Mai_Dambu
Musha Karatu
Ummyn Yusrah novel Fans
Yar Gidan Yaddiko Fans G
Taskar Mai_Dambu
Abadan-Da'iman Novel Grp
Matar So Comments Room
Qaddaranmu ce Grp
Aisha Alto novel Grp
Aisha Novel Grp
Aisha A Muh'd Novel Grp
Real Nanah Aisha
Mommyn Sayeed nd Noor
Sis Nanah & Aunty A'i
Mr Mohmud & Ummu Sayeed
Yawwo Idan dambu Yayi yawa baya jin mai.... All i heart you😍😘 Yo wasu basu iya kiran Dambu ba amma sun iya Amebo😂 Sai kaji sun kare da Danbu😂 gaskiya ana cutar da Sunana fa😹👌 *DAMBUJEE Nake shake wuyar Yan tsurku* 😉
___________________________

Page.37
A firgice Buhaina ta shiga girgizani, cike da tsoro a hankali nace mata.
"Daddana kawai zaki kira min, karki kira kowa." daga hakan na lumshe idanuna, kamar mahaukaciya ta fasa ihu, tare da d'agani ta kwantar da ni akan kujeran falon ta ruɗe baki ɗaya, Fita tayi har room ɗin Sajida Kader ta faɗa mata halin da nake ciki da sauri suka kira motar asibiti, aikuwa cikin mintuna sai ga motar a fita da no cikin wani mugun yanayi aka sani cikin motar, dakyar Sajida ta lallaɓa Buhaina takira Dadda kuma ta faɗa mishi abinda nace.
****
Tunda Faruƙ ya kwale boko, Hajiya Sadik'a ta kwala ihu, jini na fita ta hancinta da Bakinta, a birkice sukayi T.H da ita, hankalinsu a tashe sannan suka Kira Abban Ya Maheer suka faɗs mishi halin da ake ciki.

***
Hmmm wasa wasa Khairat ta zarme cikin komar Ya Maheer idanunta sun rufe, shima kuma gefe guda yayita tsarata tun bata biyo shi gurinsu har ta shiga binshi, cikin kwana biyu ya kamata yanda yake so, inda ya cigaba da gini mata soyayyarshi a zuciyarta.
Aikuwa yawon da suke a cikin masarautar yan gulma suka kaiwa mamie tsegumi, da maraicin ranar Jumma'a bayan taje ta gaida Nanah, ta biya ta gurin Mamie da take fama da yan biyunta, bayan ta gaisheta cikin nutsuwa Mamie ta amsa sannan kalle cikin sakin fuska tace.
"Baby naji labarin kina yawan yawo da wani bak'o a gidan nan ko? Ki rabu dashi ba sonki yake ba ya mai dake makaminsa ce da zaran ya sami biyan bukatarshi zai wurgar dake yayi tafiyarshi pls bana son ki shiga halin da Sisternki tashi sabida so kinji my Baby."

D'ago idanunta tayi cike da mamaki sannan tayi kasa da kanta tare da gyaɗawa mamie, tace.
"Zan wucce shashinmu."
Murmushi Mamie tayi dan ta hango jin haushin maganar da tayi a cikin kwayar idanun khairat.
......Tunda tafita ranta ya kara ɓaci, dan haka can lambun taje dan tasan yana gurin.
Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya cikin damuwa ta samu gurin ta zauna kusa da shi, kanta a sunkuye ta rasa ta inda zata fara magana ta kalle shi, shima ita yake kallo cikin son karanto abinda ke kwayar idanunta wanda suke cike da kwalla. A hankali suka shiga saukowa muryanta narawa tace.
"Ka gaya min gaskiya, kazo cin amanata ne? Ko kazo ida nufinka ne akaina? Dan yau naji asalin ko kai waye kashigo mana masarautane dan ka yaudareni meye nayi maka da zafi haka da zaka shiga rayuwata ehhee faɗa min meye kake nima a gurina, Daraj..."
"Ya isa! Baki da abinda zan nima a gurinki nima kaddarar so ce ta kawo ni nan, tabbas duk wanda ya faɗa miki bayi karya ba dan yaudaranki nake da muradin ƴi, babu sonki a zuciyata, ki nutsu na faɗa miki abinda ya kawo ni da kuma abinda zan tambaye ki."
"Kaii waye da zaka daka min tsawa? Sabida kaga na damu da kai bayan ka zalimci wawuyar zuciyata, waye kaii? Me kake nim."
"Ki saurare ni nace." ya buga mata wani mugun tsawar da sai da taja da baya, take ys koma Ya Mayyernshi na asali ya kuma kara da tsuke fuskarshi ya buga mata harara, ganin yanda jikinta ke rawa ya sashi ce mata.
"Ki nutsu babu abinda zan miki, bana son rashin kunya ne, Mace d'aya tal take min rashin kunya na kyaleta bayan ita bana jin zan iya ɗauƙar renin hankalin wata Ƴa Mace, idan ba Aisha ba. A hankali ya warware mata matsalarshi da ni, da kuma dalilin da yasa yake niman amfani da ita, kuka take wiwi a hankali tace.
"Ta kare min, amma mi yasa kayi amfani da soyayya da tambayana kayi ai da zan faɗa maka kai tsaye."
Tausayi ta bashi sosai cikin rashin jin daɗi yace.
"Idan na faɗa miki zargina zakiyi amma da abin ya shafi so kinji yanda muke ji kiyi hakuri da abinda ya faru, yanzun don Allah Aisha tana ina ne."
"Tana babba birnin Sudan khartum, anan take karatunta na law." tana gaya mishi haka ta mike tabar lambun.
........ "Ranki shi daɗe ya sami labarin inda Gimbiya khad...." Shigowar Dadda a hanzarce yasa bawan ya mike tare da barin falon, kallonta Dadda yayi irin kallon tuhumar nan amna tayi fuska.
"Fulani ki haɗa min kayana, zanyi tafiya zuwa bulgery." ya faɗa mata."Lafiya? Da tafiyar gaggawa haka?" "A'a wani taron kasa da kasa aka haɗa na masarautun gargajiya shine gwanatin tarayya tasani na wakilci k'asata." yana faɗa mata haka ya bar falon.

Kiran bayin da suke renon yan biyu tayi, tare da mika musu yaran sannan tabi bayanshi, ta same shi yana cire kayan shi cikin gaggawa ta haɗa mishi kayan. Sannan ta fito dashi falo bayi maza suka fita dashi, dan Mamie samun duniya bai sata ta kasance d'aya daga cikin mata masu son komi sai masu aiki ko bayi fully house wife ce ita.
Cikin awa guda yabar masarautar, ita kuma tasaka aka kira mata masu tsaron kofa tace kar su bari Ya Maheer ya bar gidan.

***
Zarya yake a masaukinshi tare da shafa kumcinsa da na zabga mishi mari, dariya yayi. "Ban tab'a ladabtar da wata mace ba asalima matan bina suke wannan karon sai nasaki kinyi tirr da Rayuwarki Hajja Khadi shi yasa ma na ke niman sauyin gurin aiki, dole na kafa miki tarihin d'a namiji a ranki sai nasanya miki tsanar kowanni d'a namiji daga karshe na aureki nata wulakantaki."Inji Annur knn anya kuwa kudirinka nan.
..........Bayan wasu kwanaki buɗe idanuna a hankali sakamakon jin ana shafa kaina, akan Dadda na zuba, kyakyawan murmushi ya sakar min, bututun shakar numfashine a hancina na d'ago zan zauna ya maidani cikin nutsuwa, murmushi ya sakar min a karo na biyu cikin sanyin murya nace.
"Daddana! Na ɗago ka ko? Na hanaka aikin alumma, tun daga ranar da nazo duniya nake haifa maka damuwa, kama daga ɓacewata har zuwa dawowa na." numfashi na sauke a gajiye tare da ajiye maganar na juyar da kaina gefe na cigaba da cewa.
"A duk lokacin da aka min gorin iyaye, cewa nake Allah ya bayyana min ku kota halin ƙaƙa, ban taɓa nima zab'in ubangiji ba dan gani nake gwara ya bayyana min ku ko za'a kirani da Y'ar halak, duk son na haɗu da mahaifiyata da Mahaifina sai gashi bai zame min alkhairi ba, daga kuskure irinta yaranta na rabu da farin cikina, na sameku shima na same shi amadadin na zauna na kulada lafiyar shi Dadda."
Nishi nayi wanda ya janyo fitowar gudan jini ta hancina. Mikewa yayi ya ɗauko tissue ya goge min hancina yana kallona, cikin karfin hali nacigaba da cewa.
"Amadadin na sadaukar da lokacina dan ganin ya sami lafiya sai nayita hauka ina cewa sai ya sake ni, Dadda ya sake ni amma zuciyata taki barina na nutsu, ina biyan bashi kuntattawar da nayi mishi, Dadda bansan me yasa Mamie bata kaunata ba, dan duk Uwar da takw son d'anta toh burinta ta inganta masa farin cikinta, son duniya da zama wani abu yasa Mamie bata kallona a matsayin Y'a mai yanci, ta maidani kadara mai tsada, ta renawa Mutanen da sukayi jigila dani tun daga ranar da suka tsinceni har zuwa Yau, da nake magana da kai, Dadda waau gudun Yaransu suke su aureni, amma iyayenshi suka amsheni hannu bibiyu dan kaunar da yake min maybe dan Mamie bata san meye So bane, da tasani bazata taɓa barin wani ya shigo rayuwata ba, Dadda Ya Maheer ya bani kariya fiyye da tunanin mai tunani, ya sadaukar da lafiyarshi da farin cikinshi, sabida ni ya ajiye karatunshi da har yau bana tunanin ya cigaba Dadda haka kawai nake maka kallon abokin shawara a matsayinka na mahaifina don Allah karka bani abinda bana so, Idan na tashi kabarni na koma gare shi idan ban tashi, Dadda gawata ina son shi zai sakata a makwancina."
Sauke wasu kwalla nayi masu mugun zafi, tare da saka hannuna na goge hancina dake zubda jini, cikin karfin hali na juyi ina kallon Mahaifina da yake share kwalla na kara matsa hannunshi nace.
"K'addaran da haɗuwa daku ta rabani da shi, gashi na same ku amma kuma narasa shi. Dadda kabar kuka ni kuma tawa k'addaran kenan, amadadin mahaifiyata ta zame min me kawo min farin ciki sai gashi yau ita ke yaƙi da farin cikina, Dadda nafi sonka da ita sabida ita ta ɗauke ni haja ce, wacce zata iya saka mishi furashi ga duk wanda yayi mata, musamman ga masu kuɗ'i da attajirai da sarakuna, Me yasa na fito cikin gidan Sarauta, me yasa ban zo a gidan kananun mutane ba, kasan me Dadda karamin mutum shi yake bawa iyalinshi duk wata farin ciki kuma ya basu zaɓi ga irin rayuwar da suke muradi, suke bawa yaransu rayuwa mai yanci kamar yanda Yaddiko ta bani rayuwar farin ciki gashi ita bata haifi d'ayanku ba amma ta bani kyauta mai daraja, tabani lu'ulu'u dan shi dutse ne mai darajar da ba'a samun irinshi Dadda da za'a sabunta min rayuwa da Ya Maheer zan roka a sabunta min, sabida ina mishi sonda banda Allah da manzon shi banawa kowa sai kai da Yaddiko"

Numfashina ne ya soma sauka da hawa, karan da na'uran da aka samin ya dawo da hankalin likitotin da suke lura da ciwona suka shiga zuwa da gudu, kuka yaci karfin Dadda. Tun ina ganinshi dishi dishi har idanuna suka rufe, fita akayi da shi. Kamar ba tsohon soja ba, Dadda yake kuka lallubar wayarshi yayi ya fara kokarin niman sarkin bauchi...
****
"Wai Abokina! lafiyarka kuwa naga sai gumi kake" inji D'ayif,
Cikin karaji yace.
"Ina son barin gidan nan, yau ba gobe ba dan ina ji a jikina Ummun Aeesha ba lafiya."
"Taya kenan zaka fita?"
Murmushi yayi sannan yaj.......😹👌
'''Banyi alkawari ba, sai a koyaƴshe zaku iya tsintar bazata Allah ya sake haɗamu da alkhairi, har yanzun ina baran addu'arku🙏🙇'''

YAR GIDAN YADDIKO🧕Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz