8

5.4K 461 36
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

*Wannan shafin na kune.*
*Mommyn Abul*
*Jiddart*
*Idon Kuka*
. *Oum Rahman*
_Ayi rawan tunkwal_
_Kabi kwarewa....Nasara sai tabika_

'''I know not with what weapons World War III will be fought, but World War IV will be fought with sticks and stones.'''
By : Albert Einstein _________________________________

Page.8
Kallon yan uwana da muka ci duka dasu suke kuka, amma niko a jikina. Sulalewa nayi nabar hostel na mike cikin dajin makaranta, tafiya mai nisa nayi na samo karara na juyo abuna yo ko tsoro babu a raina.

Koda na dawo nasami ɗalibai a zazzaune ana hiran irin muguntar da senior suke sai banji komi ba,
Tun a lokacin na ɗiɓe ruwan wanka da nasallah nasami Yaran da muke ɗaki daya nace.
"Kowa taje ta ɗibo ruwan wankanta, don gobe babu ruwa."
Kallona sukayi cikin renin hankali ban damu ba, na zauna,sai da yamma yayi muka tafi islamiyya, muna dawowa muka tafi evening lesson.
Bayan magariba muka wucce gurin cin abinci, dake akwai mugun kudiri a raina banci abincin ba na tashi,
Bohul ɗinmu dama ya lalace, a rijiya ake ɗiban ruwa. Gugar nace na zuba karara a ciki, sauran nabi ɗakunarsu na zuba musu a cikin bokatayensu.

Na wucce abuna na dawo ɗakinmu kamar mayya. Na zauns tare da buɗe book ɗina ina karatu.
Can sai ga ɗalibai sun dawo, bayan sallar isha na kwanta sai barci.
Assalatun farko naje nayi wanka na. Na dawo nashafa mai na kwanta lokacin sallah nayi na mike nayi dama da alola na,
Can naji an fara layin ɗiban ruwa,
Senior suka gama ɗiba, sannan kowacce taje ta ɗauko towel ɗinta wanda yasha barbaɗen Karara.
Suka nufi banɗaki suna susa jiki sama sama,

Aiku kafin su shiga wanka komi ya lalace, domin kaikayi har a ruwan da suka watsa, sai kuga katuwar budurwa tanq birgima a kasa, shiryawa nayi na fita abuna.
Ko kallo basu isheni ba, na nufi gurin cin abinci. Ranar da yawan ɗalibai basu yi wanka ba, har da yan ɗakinmu da muka dawo bayan an tashi, aka sake zuwa za'a zane mu dan anyi tunanin jenior ne sukayi haka, har ansa wasu jada gwiwa ns mike tsaye nace.
"Nice Na zuba muku karara a cikin bokiti da towel, matuƙar kuka cigaba da zalinci nima bazan fasa ba, dan haka ni ɗaya zan amshi hukuncinku sauran su je ɗakinsu."

Kamar Mayyu haka suka yo kaina, niko ɗar banji ba.
Bulalar hannunsu suka tawo dashi, duk suka rufa min da duka, banji nayi kuka ba kuma bsn durkusa ba.
Suna gamawa suka ce nayi tsalle kwaɗo, nan ne kan sai da nayi kuka, dakyar suka barni da taimakon metro ɗinmu, ina mikewa nace musu.
"Wallahi kunci bashi sai kun biya."
Koda muka koma.
Zama nayi naci kuka kamar zan cire idanuna.
Yan ɗakinmu sai rarrashina suke, da dare kafana ya hanani barci.
Tashi nayi na ɗauki farin zanin gado, na baɗe fuskana da farin hoda, bakina na lafta jan baki.

Na nufi ɗakunar kwanarsu, dama mutane biyar ne, kafin na tafi na sami katon itacena na tafi dashi, Senior Devana itace na fara da ita, inda na ɗauki katon itacena na maka mata a gwiwarta.
Tana farka da ihu nasaka hannuna a bakina, nace.
"Shiruuuu."
Duk wanda ya farka ya ganni ds farin kaya komawa yake, ɗan buuuu sai da na make mata kafa.
Nafice zuwa ɗakinsu Senior karima,itama na mata,

Yaseen duk sai da na buge musu gwiwarsu na dawo ɗaki na kwanta bayan na antaya kashedi da karsu kuma taɓani dan aljanatace tazo ɗaukar fansa.
Ina shiga ɗakinmu naga Yan ciki duk sun mike a tsorace cikin tashin hankali Metro tace.
"Kece kika sake zuwa ko, mi yasa baki da hakuri."
"Iya jeki kwanta nima na gaji."
Haka nace mata, sauran na kallesu nace.
"Saura wata tayi gigin magana Yaseen gobe zata rasa kayan zuwa aji."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now