38

5.6K 629 62
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.38
       Nuna mishi motar da takawo abincin dabobi yayi, dan alokacin ake saukewa kuma motar Babba ce sosai, kallonshi  Ya Maheer yayi cikin nutsuwa yace.
     "D'ayif zan bar gidan nan baka faɗa min kai waye ba, meye nasabarka da gidan nan."
        Murmushi D'ayif yayi sannan yace.
   "Kakanina sunyi bauta a gidan nan har zuwa kan iyayena, abin nufi ni bawa ne a gidan nan, amma kuma nasami ilimin addini da na zamani, inda na karanci duba gari shi yasa zaka ga gidan yana yawan samun kulawa ta musaman, wannan shine tarihina."
   Mika mishi hannu, Maheer yayi cikin jinjinawa yace.
     "Zan dawo kwanan nan dan dole kaima kafita kayi rayuwa kamar kowani d'an adam, naga sun sauke kayansu. Komina na jikina saduwar Alkhairi.
         Har gurin motar ya isa sannan ya samu ya haye ta gefe ya dire cikin motar D'ayif ya wurga mishi bag ɗinshi, kamar jira suke ya shiga suka ja motarsu suka bar gidan ba tare da an bincike su ba, yana tabbatarwa sun bar cikin masarautar ya shiga buga musu motar dole suka tsaya, tare da buɗe bayan motar, dira yyi yana dariya sannan yace.
     "Afuwa! Ni airport nake son zuwa shine na biyo motarku kuyi hakuri."
       "Shi kenan muje, sai mu sauke ka." Inji driven motar,
          *****
    Cikin kiɗima da tashin hankali Dadda, yake faɗawa sarkin bauchi abinda ke faru, ce masa yayi.
   "Bari na tura a kira min mahaifin yaron."
        Bayan awa guda Mai martaba sarkin bauchi ya kira Dadda yace.
     "Iyayenshi sun tabbatar min  yana  maiduguri, dan basa samun wayarshi, kuma shi gurin Hajja Khadi yaje."

          Shiru Dadda yayi sukayi sallama, sannan ya nufi inda window na yake, yana kallon yanda likitoti suke kokari akaina,.
  Zuciyarshi ce take raya mishi Mamie tasan komi, girgiza kai yayi yana alajabin halayartar,,

          Sai da likitoti suka kusan kwana akaina kafin numfashina ya daidaita lokacin kan dadda banda kaiwa Allah kukanshi baya komi, har suka fito sannan  suka nime idan yadawo daga masalaci a turashi gurinsu.
         ****
   Suna sauke shi a airport yayi musu godiya sannan ya shiga cikin, buɗe jakarshi yayi ya ciro passport ɗinshi, kafin nan dole ya sayo tickit ɗin dan zuwa kano, abinda yayi kenan kuma a cikin daren ya sami yan kasuwar da zasu dubai ta kano, karfe uku na dare jirginsu ya tashi zuwa kano,  su. Sauka hud'u saura, a lokacin yayita shige da ficce har ya samu jirgin da zai bi zuwa Abu Dhabi.
    Bayan sallar asuba, jirgin ya tashi zuwa can karfe biyu na rana suka sauka, hutun mintina arba'in da suƙayi ji yake kaman shekaru arba'in ne, daga nan kuwa da jirgin ya tashi basu kuma tsayawa ba sai a khartum, a da misalin karfe goma na dare, suka sauka.
            Masauki ya nima ya kwana washi gari ya bazama cikin makarantar, inda yayita nimanta bai sameta ba.
           ****
  A asibiti kuwa ina cikin wani hali, dan sun faɗawa Dadda yanda zuciyata ta kumbura shi yasa nake yawan fidda jini ta hanci da baki, da za'a nima min abinda nake so da zai fi sauki.
               Hankali shi ya tashi gashi yana son zuwa maiduguri ya tawo da Ya Maheer ga kuma baya son ya tafi yabarni dan gani yake kamar zai iya dawowa ya samu na mutu.
           Haka dai muka kwashi kwana uku, wanda a ɓangaren Ya Maheer shima haka yake ta faman nima na, ranar na hud'u Buhaina da Sajida sun fito makaranta zasu zo dubani, suka hango shi yana tambayar wasu,  rike Sajida Buhaina tayi cikin mamaki tace.
      "Wancan kaman Dr mijin Aisha." dake ita Tana ganin hotonshi akan laptop ɗina, shi yasa tasan shi, da sauri suka nufi gurinshi. Buhaina tace.
"Dr Maheer Imran Gumau."
Kamar ya kifa haka ya juya, cikin wani farin ciki, yace.
"Na'am! Ina Ummi Aeesha?"
           Idanunta ne ya cika da ruwa tace.
         "Tana asibiti, me yasa kayi nisa da ita.? Gata can ciwon zuciya zai kasheta sabida kai."
     Girgiza kai yayi a ranshi yace.
*Banda Umma ke kika haifar min matar da nafi so da na zabga miki Allah ya isa* (😹 Luv ooo)
       "Muje asibitin " Inji shi,
    Taxi suka tsayar shi ya shiga gaba su kuma suka zauna a baya, har asibitin, shi ya biya kuɗin. Yanda yaga suke tafiyarsu sai ranshi ya ɓaci amma dole yayo hakuri dasu, har suka iso inda aka kwantar dani, a bakin kofa suka haɗu da Dadda zai fita niman abinda zai ci, Buhaina tace.
     "Dadda munzo da abinci gashi a baske..."
      Kallon Ya Maheer yayi sosai sannan yace.
      "Yaushe kazo, har nasa a nima min kai."
Sunkuyar da kai ya Maheer yayi cikin jin kunya. Ya kasa cewa komi, koda su Buhaina suka shige,  yakawa Dadda yayi cikin dattako yace.
    "Ga matarka nan, ni zan koma yau tunda dama ciwon naku haka yake wannan natashi wannan zai kwanta, tunda ka iya biyota na yarda bakai ne ka saketa ba, na kara baka amanarta a karo na biyu. Allah ya bata lafiya."
         Komawa ciki dadda yayi ya had'a wayoyinshi yayi musu sallama tare da barin asibitin baki d'aya, tunda ya shiga d'akin yake kallona ina kwance ban ma san yana yi ba, jingina yayi da wall ɗin dakin, sannan ya tsura min ido can su buhaina suƙa mishi sallama tare da mishi fatan Allah ya bani lafiya.
           A hankali ya taka har bakin gadon, ya zauna a bakin gadon ya kalli yanda nayi fayau, shafa fuskana yayi cikin sanyin murya yace.
"Kee! Yar aljanata tashi gani nazo gareki, raguwa kawai."
         Surutu yayi ta min, tare da buɗ'e takardun da aka rubuta rahoton ciwona, shiru yayi. Ya ajiye. Sumbatar goshina yayi cikin jin daɗi ya zauna a gurin,
       ........Dadda ya bar sudan da kwana biyu na farka, a hankali nake buɗe idanuna tare da shakar kamshin turaren da bazan iya mantawa ba, buɗe idanuna nayi na ganshi kwance a gefena yasaka hannunshi ya makale ni, sosai kuma dan iyaye a wannan karamin gadon, inda ya ɗaura ni a kirjinshi. Cusa kaina nayi cikin kirjinshi ina sauke numfashi da sauri da sauri a hankali nace.
     "Ya Mayyer!"
      Kaman a mafarki yaji murya na buɗe idanunshi yayi, yana kallona  juyawa yayi tare da janyo fuskana yace.
    "My Diva har kin farka, daga duniyar suma." duka na kai mishi cikin shagwaɓa nace.
"Ni kyale ni,"
           Riko hannun yayi ya sumbaci tafin hannun sannan ya koma goshina sauka yaƴi ya gyara min kwanciya, ban daki ya shiga ya ɗauko min tootbrush ɗina da maclear, ya kawo min ya wanke min bakina sabida bushewar jini, yana gamawa ya haɗa min tea, mai kauri ya shiga bani ina sha. Cikin tsokana da zolaya.
      "Yarinya taga zabgeggen namiji duk ta sussuce, har da nima shekawa lahira, yo idan kika tafi ai ni sai dai na kara wani auren ya..."
Pillow da nake kai ne na dauka na maka mishi ina kukan sakalci nace.
     "Allah sai na faɗawa Dadda da Mamah da yadikkona." kura min ido yayi bayan na gama shan tea ɗin, a hankali yakai hannunshi kan fuskana ya shafa, tare da goge min d'an ruwan tea da ya rage, a bakina make hannunshi nayi. Tare da tura mishi baki nace.
      "Zan sha ruwa."
    Goran ruwa ya buɗe, ya kunsa abakinshi sannan ya matso kusadani, ya mika min bakinshi yayi a hankali na faɗa jikinshi tare da had'a bakinmu na shiga karɓ'an ruwan ba iya shi ba, hatta komi karɓ'a nake daga gare shi, tabba wallahi ina son mijina ba saki uku ba ko saki dubu ne sai dai suyi, sam na manta ds jinya nake shima kuma haka ya manta da jinya muke, burinmu mu farantawa kanmu, kiran sallar asuba yasa shi sake ni, yana sauke numfashi kamar wanda yayi wasan tsire.
        Gyara min kwanciya yayi ya fita zuwa masalaci, yana dawowa ya samu nima ina kan abin sallah, zama yayi yaja min hanci cikin faɗ'a yace.
   "Wa yasaki kitashi, wato har wanka kikayi shine baki jira ni ba"
    Murmushi nayi na mike na, nace.
"Kwana na nawa ina kwance."
       "Kamar sati biyu "
       Tadda kabara nayi na fara gabatar da sallar dake kaina ban dakata ba sai karfe tara nasafe, inda na had'a har da walaha, koda likitotina suka shigo sunsha mamaki, lokacin da suka ga ina sallar a tsaye, yana gefena. Har na idar suka kara dubani, sannan suka ce dole nakara kwana biyu gudun kar wani abu ya taso.
             Haka muka zauna a asibitin, zai fita ya karɓ'o mana abinci a gurin Buhaina, sai anzo gurin cin abincin ne kuma nan muke karewa da shiririta, dan cewa nake.
      "Ni bazan cida hannuna ba, kuma bazanci da daga hannunka ba, na bakinka zanci."
   Haka zai ɗiba abincin yayi min yanda nake so.
        A nan muke karewa da shirme, Ya Maheer yayi kokarin goge laifinshi sosai, asalima nikam banga laifinshi ba kodan idanuna sun rufe ne akanshi oho.
     Ranar monday aka sallame ni, bansan ya akayi yasami gida flat mai kyau, da tsari ba sai dai ya kaini gidan, inda muka shiga falon gidan kome a shirye kamar ansan da zuwa na, sai bedroom d'in shima haka. Ina shiga dakin na fuskana ta sauka akan wata tangamemmiyar hotona, wanda nayi cikinsu Faratuna, da Uwar garke, juyawa nayi muka had'a fuska kallon cikin idanunshi nayi ina son yin magana amma bakina yayi nauyi, sakamakon jin hannunshi akan k'uguna  ba sabon abu bane a gurina amma yanda yake tafiya da yanayine,, a hankali ya janyo ni sosai zuwa jikinshi tare da ajiye kanshi akan wuya na, yana goga hancinshi kan wuyata riƙe rigarshi nayi jikina na rawa, na d'ago kaina nace.
     "Me yasa ka sake ni? Kuma har saki uku fa meye matsayin aurenmu.?"
          D'ago kaina yayi cikin wani yanayi yace.
       "Koda sara naman jikina kike da wuka, kina kasawa Ummi Bazan sake ki ba, balle kuma so da yarda duk na sadaukarwa rayuwarmu, ni da hannuna ban sake ki ba. Allah ya gani kuma bazan taɓa wannan kuskuren ba dan ina son matata, sannan kina son sanin matsayin aurenmu muje can na nuna miki matsayin da aurenmu yake dashi, daga yau ki fara tunanin darajar aurenmu."
Kafin nasan abinyi yayi ban ɗaki dayi, ruwa ya haɗa mana, sannan ya shiga cire min kayana, ina ture hannunshi dariya yayi yace.
    "Yan mata. Wato boons ɗinki sun kara girma, kema kin zama big gal shine kike kunyar na gansu yo sai na gani yau ki shirya karɓ'an Maheer Imran gumau....

      *Allah dai ya kara baku hakuri tunda ku nayiwa laifin*👏
               

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now