9

5.5K 451 23
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
      *Wattpad:Mai_Dambu*
          

    *Allah nabaku Kyauta Uwar garke, tunda baku so hikenan sun sheka Lahira*😂

       Alhamdulillah😉
Page.9
        "Wallahi na faɗa miki, sai na farke yarinyar dan tayi min." ya faɗa cikin salon yan daba.

    "Dalla can ana maganar arziki kana sako na tsiya" inji Hajiya sadika.

         Shiru yayi yana cizon lip ɗinshi, irinta rikakkun Yan iska, ya mike tare da buga sowa,
         
     Kallon Sailuba Hajiya tayi cikin nutsuwa tace.
"Miye ya faru?"
    "Hajiya nifa ban gane kanshi ba, sai magana yake faɗa min."
  Bakinta ya gaza furta komi sabida tashin hankali. Allah ya gani ta haɗa aurene dan ƙuɗin Yayanta, kuma tasan Mahaifiyar Maheer bata da matsala kamar Hajiya Salma mahaifiyar Najib.

      Hajiya Safiya tana da halin kawaici irin na fulanin Katagum, gata da mutunta mutane, uwa uba abinta bai rufe mata idanu ba, shi yasa Hajiya Sadika ta makale mata, banbancinta da Hajiya Salma kenan tana da iko da jin kai, irin na ɗiyoyin sarauta.
      Gata da mugun rowa. Abin hannunta ba kowa keci ba, kuma ta maida Alhaji Ibrahim kamar buje, juya shi take son ranta. Sai gashi ɗanta Najib bai ɗauko halinta ba, dan Allah yayi mishi yawan kyauta.

           Furza da iska tayi tace.
"Kyale shi, karki damu zanyi maganinshi."

    .....
          Fitsarine ya dame ni, cikin dare amma haka na kwanta abuna, dan dole na mike tare da sauka a gadona na ɗauki lenta na na fita zuwa waje bakina dauke da Addu'a.
                   Nazo zan yanki kwanar da zan yanka na shiga ban ɗakine sai ga wata dirkekiyar kuliya, akan wata yarinya tana lasar jikinta.
           Abinda ya fito bakina shine.
  "7 A'uzu bikalmatullahi tam......"
   Kafin na karasa sai ji nayi kamar an sure ni anyi sama dani aka maka da kasa, mikewa nayi ina kara maimaita.
        "K'alu Innalillahi..."
          Aka sake sama dani, wannan karon ban faɗi ba, cak na tsaya a iska, idanuna rufe.
    A hankali aka saukar dani kasa aka jingina ni da bango, na zame na kwanta. A gurin ban kuma sanin abinda ya faru ba sai bayan kwana uku.
    Na farka a ɗakin Yaddiko, Mama tana kusadani, Ya Najib na gefen Yaddiko da take fyace majina tana kuka, dama abinda ta guda kenan gashi nan mayu zasu kasara mata Yar mareniyar Allah.

       Gogan na bakin kofa. A tsaye yana kare  min kallo.
     Nima tunda na tashi nayi mika tare da addu'a nace.
"Mama jikina na ciwo."
   Na faɗa a shagwaɓe. Shafa kaina tayi, tana murmushi tace.
"Sannu dole jiki yayi ciwo Baby, kwana biyar kina barci tunda aka kawo ki daga schl."
     Dafe goshina nayi tare da cewa.
"Washi Allah na, kaina zai fashe."
  Dan jin wani kuwwa, da kararrawa, tare da hayaniyar mutane. Komawa nayi na kwanta tare da lumshe idanuna. Sannu suka dame ni da cewa, na buɗe jajjaye idanuna na daka musu tsawa tare da mikewa a iska.
        A razane Mama da Yaddiko sukayi baya, Ya najib yakai hannunshi da niyyar taɓa ni aka maka shida bango.
   Naɗe hannun rigarshi yayi, ya shiga karanto, (229:2: bak'ara)
     Ya iso har inda nake, kamoni yayi ya danna nida gadon nasake mikewa ya maza ya haɗani da kirjinshi, yana karanto Ayoyin alkur'ani.
  Ihu nake tare da kururuwa, dukar shi nake ina cizon shi tare da yakushi bai fasa ba, haka Mama itama ta cigaba dayi. Tana haɗa maganin da aka bani lokacin da Aka kawo ni daga makaranta aka kaini gidan Imam Nafi'u Saɗ'e babban Malami a cikin garin bauchi, kuma yana daga cikin Member na Izalatul Bidi'a waikamatul Sunnah.
       Shi ya haɗa maganin da kanshi dake Ya Najib ɗalibinshine yace a na shafa min a jikina kuma a bani nasha.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now