32

5.1K 672 55
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

        👌👌👌👌
       _Wallahi Maman Iman kin bani dariya bake ba har da Ladingo da Biyuti da tallatuware😹 Duk inda na kutsa Y'ar Yaddiko, yo nasan Aunty Safara da Ummin Adnan shiru sukayi, Zahra da Hjy Aisha kuwa sun bini da ido😹 Yo sai kuyi hakuri kunsan Giyar Cele By Force y yana kaɗani, Masu fatar najib Ya wula na hangoku_

   
Page.32
    Kurra mishi ido tayi cikin kaɗuwa da tashin hankali, hawaye na wasan tsire a idanunta.
           Rike hannunshi tayi cikin kuka tace.
"Ummi Aisha kake so? Wallahi zan nima kama ita."
      Ta karshe maganar cikin kuka da shasheka.
    "Aikan aiki yasame ki, dan da alamu kin manta furucinki na cewa da Najib ya auri Shatuwa gwara ki ga gawanshi, yo ce miki akayi Allah abokin wasankine da zakiyi wannan furucin ya kyaleki, ki girbi abinda kika aikata, kin zata Allah baya amsar addu'ar mutane lokacin da kikayi taki, Shatu Matar Mahar ce, ko mi zakiyi kiyi amma nayi imani kinyi wasa da kanki."

     Yaddiko nagama fadar haka ta juya ta fita tana share kwalla, gani take duk itace ta janyo musu matsalar da bata korini ba ranar da komi yazo cikin sauki.

         ......
"Wakili kaida barden ina son kuje asibiti ku duba min halin da Yaron Alhaji Imran Gumau yake ciki." Inji Sarkin Abdullah,

   "Angama rankashi "Inji wakili.
     
        ****
   "Hmm! Bamai baka ce komi ba, akan maganar Khadija." inji Mamie,
     Juyawa yayi ya kalleta da kyau sannan yace.
"Toh mi zance tunda yarinya dai tace bata son Izzudeen, asalima ki bar shiga abinda bai dameki ba dan gudun jin kunya, dan na fahimci ita mijinta tak...."
       "A wani duniya ake wannan kwamacalar,  yasaketa har uku kace tana son mijinta ko mutuwa zatayi bazata koma gidan shi ba na fada maka wallahi" sake baki Dadda yayi cikin mamaki, kafin ya taɓe bakinshi ya fita zuwa fada dan ya lura sarai idan ya biye mata Allah sai ya raba hali da ita sam ya gaza fahimtar wata iriyar macece, mai shegen fadin rai.
     (Irinsu wata a wani grp😂)
                Shiru Mamie tayi zuciyarta na tafasa, wayarta ta ja takira. Aunty Zaituna, sama sama suka gaisa sannan tace.
"Hajja Khadi tana kusane?"
        "Eh gata."
          Cikin saukar da kai tace.
"Uwata! Har yanzun kina son Maheer ne?"
      Shiru nayi duk na diririce can nace.
"A'a ni bana sonshi."
    Yanda na fada a sakalce yasata sake murmushi, "Toh Hajjana ayi karatu mai kyau banda kula maza ki nutsu ki zama the best."
    "Toh! Mamie"
   Daga haka ta datse kiran.
Shiru tayi tana jijjiga kafarta irin masifa yana cin ranta.

         ****

       Lokacin da Abba yazo yasami Mama da maganarshi shiru tayi tace.
"Yanzun dai mu bar maganar, amma ina mamakin wannan alamarin, tunda ya faɗi a gida har yanzun bai farka ba, taya zai saketa. Mu ajiye maganar dan idan muka fito dashi mune zamu kuma shiga damuwa.
    Zuwansu Wakili, suka samu Ya Maheer a cikin halin coma fatan Allah ya bashi lafiya suka mashi. Gefe guda kuwa jikin Ya Najib ya kuma rikicewa, tun yaji abinda Yaddiko ta faɗawa Umma.
       Kokari ake a fiddashi kafin ranar tafiyarsu, amma abu yaci tura dan aman jini yake guda guda. Idanunshi sunyi fari haka fuskarshi zuwa bakinshi.
      Binta tafi kowa damuwa, kuka yake kaman ranta zai fita ga karamin cikin jikinta shi tafi tausayawa.
  
           Umma kuwa ko mahaukaciya tasallama mata, dan ta gigice ainun.
                 Duk iskancin Sailuba itama tana manne da mijinta tashiga damuwa ainun.
         ****
       "Amma dear ! Miye na kuka?" Buhaina tayi tambayeni,
    Cikin kuka nace.
"My Sis! Tana bazanyi kuka ba, tambayana Mamie tayi ko ina son Dr, ni bansan mi nake ji akanshi ba amma by now, ina jin ɓacin rai akan abinda yayi ai ko ba komi zai nime inda nake, amma ko ba komi ai hannun Yaddiko na tashi ya bibiye alamarina, duk baiyi haka ba sai ma mantani da yayi a duniyarshi ina jin ciwon haka."
   Na karshe maganar cikin kuka.
     Shiru tayi kafin tace.
"Toh shi yasan inda kike ne? Balle yayi tunanin nimanki, kiyi nazari da kyau mana. Yan matan Dr Gumau."
      Duka na kai mata cikin jin haushi nace.
"Taya bazai san inda nake ba, tunda yana son..."
     "Kuma kema kina son..?" ta kashe min ido mikewa nayi daga gurin hutawar d'alibai na shige bayi na wanke fuskana na fito.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now