42

5.9K 520 35
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAK'A WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu
*Watpad:Mai_Dambu*

_Kyauta ga Masoyan Asali_😘💃🏼

_😊Allah sarki Ummu Khadi nagode sosai da kauna, idan da akwai abinda zan fanshi soyayyar da kike min toh zan iya fansar haka da book da ciwo a rayuwata return Insha Allah gaba d'ayarshi nakine sadaukarwankine book d'in amma sai 2020 insha Allah wannan karon inna wuro da Tanimundari tare da Aiyan maska, kai har da Su'ad ga kuma Junaina, Allah ya bamu aron numfashi, wannan karon babu batun zungura ko raruka, an hanani shirin kunya🤭🤪😜_
Saura wata tace min Chaiii😼

#Team Mamie Zauren Mai_Dambu naga kunfi kowa kaunar Uwargida Fulani Nafi......
Page.42
"Waye shi?" Ya jefa min tambaya, a tsorace nace.
"D'an Yayan Dadda ne sh."
"Ban tambayeki ba, meye alakar shi dake?"
"Shine zan fad'a maka ka katseni." Kallona yayi yanda kwalla ke bin fuskana.
"Ok ina jinki."
Yace min,
Sunkuyar da kaina nayi, sannan na d'ago kaina. Rike hannunshi na rike dake kan sitiyeri.
"Mamie ce ta turo shi tayi mu daidaita kanmu yanzun hak."
"Ok kenan kishi yake yayi kyau amma me yasa mamie take son kanta da yawa, a gask..."
Kura mishi ido nayi cike da mamaki nasan gaskiya ya fad'a amma take naji raina ya bac'i nace.
"Uwata ce duk lalacewarta haka nake sonta, sonkai ba sabo bane dan tayi akan Y'arta idan baka manta ba a bisa kuskure ka kore ni dan zan zubda cikin matarka, sannan dan ta nuna sonkai a kaina ba wani abin damuwa bane pls ka tayani mutunta Mahaifiyata idan bai maka ba zaka iya cikawa wandonka iska."

Ina gama fad'ar haka na juyar da kaina jikin window, ina kallon titi bakinshi bud'e yake kallona, yanda na tsaya na tsife shi kad'a kanshi yayi ya cigaba da tuki, har muka isa gida kafin yayi parking na fice saura kiris na fad'i a tsorace yace.
"Wallahi kika kuskura wani abu ya sami lafiyar cikinki sai na baki mamaki."
Ko sauraranshi banyi ba na shige cikin gidan na zube a kujera na fashe da kuka, wallahi ban ji dad'in rashin kunyar da nayi mishi ba ga kuma wani tashin hankali wai cikin jikina.
Shafa cikin nayi dan banji alamar kome ba tunda cikin a d'akale yake manne da bayana ko abinci naci ba zaka tab'a ganin yafito ba.

Shigowa yayi ya ajiye min jakata, ya wucce d'aki can sai gashi da bomshort da kuma singlet, hannunshi rike da katon roba. Ya d'ibo ruwan zafi a ciki. Yana zuwa ya dire a gabana.
Ya durkusa takalmina ya zare min, sannan ya cire safar da nasaka ya sanya kafar a cikin ruwan zafin, bud'e idanuna nayi na kalle shi, sake lumshi idanuna nayi kwalla na zuba min.
Cire d'ayar kafar yayi ya sanya min a cikin ruwan, ba tare da b'ata lokaci ba ya zare min hijab dina ya nad'e sannan ya zauna a gabana yana matsa kafar. Wanda sukayi bulu bulu, d'ago kanshi yayi cikin sanyin murya yace.
"Ummi Aeesha kiyi hakuri."
Kura mushi ido nayi na girgiza kaina cikin kukan da ya taso min nace.
"Kai zan bawa hakuri bazan kuma ba."
"Ya wucce."yace min.
Shiru mukayi. Can naji yana min tafiyar tsotsa bansan lokacin da nace.
"Ya mayyer na! I miss you."
Murmushi yayi sannan ya mike cak ya d'auke ni zuwa cikin d'akinmu, kwantar dani yayi ya shiga cire min rigar jikina dan doguwar rigar lace ce.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now