23

4.7K 600 36
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.23
     Bai nuna musu shi ɗin wani bane yaje musu a bafaden sarki da niyyar auren bodd'e, dukda sun ganshi da cikar kamala haka yasasu bashi auren Mamana, a gurin bayan an shaida auren ne, ya gabatar musu da kanshi inda ya nime alfarman iyayenta su xauna a gari haka zai sakata itama tasamu nutsuwa a gidan aurenta.
        Basu ki amincewa ba amma sunce zasu zauna a wajen garine haka zai basu damar kiwon dabobinsu.

            .....
Zuwan mahaifiyata gidan yasaka tasami ilimi sosai dan itace mace mafi karancin shekaru, kuma kusan sa'ar yarshi ta shida.
      Alhamdulillah zamansu ba laifi, dan tana da shekara guda ta haife ni, sai dai haihuwar tazo da tangarɗa. Kwnanta biyu Allah ya amshi rayuwarta, sai Lamiɗo ya bawa kakata rikona. Anan na tashi har shekaru bakwai, inda muke tare da ɗan kawuna Yayan mamana, Nazif wanda yake matukar sona.
           Ina cika bakwai Lamiɗo ya dawo dani, cikin masarauta na cigaba da karatu kamar sauran Yayuna.
        Dake bayan rasuwar mama ya kuma aure yacike gurbinta.
            Kasancewa na taso cikin jama'a ba kaman masarauta ba sai nake da ɗabi'a rigima, ɓarna da gaggara. Sau da dama nasha kunce dawakai a bargansu ko kuma naje na sami girkin da akewa bayi na cika mishi wuta, abubuwa dai wanda kullum sai lamiɗo yayi min nasiyya akan na daina.
     Ina gama primary aka kaini makarantar kwana, dan duk yaran gidanmu mata suna zuwa F.G.G.C. can ma duk nabuwayi mutane, a haka duk abinda nayi Nazif kaɗai ke ce min dai daine, a haka har na kammala karatuna.
         Lokacin soyayya tsakanina da nazif ya bunkasa, ina dawowa abin tashin hankalin wai ambani, kamar sauran yayuna, kuma mijin zai zo mugana.
      Cikin kuka naje nasami lamiɗo kaina a kasa nace.
"Baffana don Allah ka taimakeni ka barni na zauna da Nazif wallahi shi nake so."
      Gyara zamanshi yayi sannan yace.
"Nafisatuh! Ki kwantar da hankalinki inda zaki je kamar gidane, sai dai ina son kisani karki bar fuskarki ta zamewa magautarki madubin dubawarsu, karki sake magautarki sunsan fitar numfashinki, ki rayu dasu kamar kurma, ko bebiya kyaji bakya gani, zaki shiga inda makiyanki zasu zame miki abokan farin cikinki masoyanki zasu zame miki abokan bakin cikinki. Sai kin nutsu zaki iya banbance masoya da makiya, Allah yayi miki albarka, tashi kije."

          Mikewa nayi ina kuka sabida wallahi bana son auren haɗi,duk iyayenmu mata nabi kansu suka ce min nayi hakuri na karɓi zaɓinshi, ban amince ba naje na sami kakana  na fada mishi shima rarrashina yayi kawai dan bai da ikon hanawa.

        A cikin watani uku, tsabar tashin hankali baka iya fahimtar halinda nake ciki, a cikin wata na biyu Yazo mu fahimci juna.
               Inda aka sauke shi a falon bak'i lokacin shekarunshi bazasu wucce ashirin da takwas zuwa da tara, ni kuma ina da sha shida zuwa da bakwai.
       Tunda aka faɗa min yazo naki fita sai da akaje aka faɗawa lamiɗo, ya turo min babban Yayanmu Maddibo, yasani a gaba. Dama kafin isowarshi Lamiɗo ya fadawa Jakadiya, ita kuma ta sanarwa matanshi. Shine aka zauna aka shiryani tsaf.
      Tunda Hamma Maddibo ya kaini ɗakin na haɗe kaina da gwiwa ina kuka, bai ce min kiyi shiru ba, bai kuma bani hakuri ba.
     Dana gaji dan kaina na ɗago sai naga mutumin rike da jarida yana karantawa wato bai masan ina gurin ba, haushin yasani watsar da komi na gurin, bai ɗago ba bai damu ba, wani center tablen ɗin kwalba nasaka hannuna na finciko kayan dake kai duk na watsar, kamar ba mutun a gurin cire alkyabbana nayi naje nayita na fasa glass ɗin dake jikin bangon falon, nan ne ya ɗago a hankali ya dubi falon yanda nayi musu kaca kace, tangarayen da aka zuba mishi abinci duk na farfasa, gashi na taka wasu. Tsabar taurin kai baisa na fasa ba, kallon yanda gashina ya rufe min fuska yayi. Ga hanuna na zubda jini.
     Tasowa yayi har gabana ya tsaya zai magana nace mishi.
"Bana kaunarka! Bana sonka, kuma nice ajalinka dan kasa an rabani da wanda nake so, tun wuri kaje kace kafasa aurena dan kuwa wallahi nice zan kasheka."
     Ganin yanda nake magana babu tsoro a ciki yasashi murmusawa yace.
"Toh gimbiya Nafisatuh! Sai nikan bazan iya zuwa faɗawa Mahaifina bana sonki ba, kodan na mutu a hannunki nikan zan aureki, dan ina son mutum mai faɗar abinda zaiyi, sai dai zan baki shawara ki ɓoye kiyayyarki akaina, dan bazai amfaneki da komi ba sai tarin dana sani, gidan da zaki shigo cike suke daniman abokin aiki da zaran kika basu damar haka toh, ba mamaki gidan yari ne makomarki, Kina tare da Abubakar Muh'd Abubkar Bamai"
    Yana gama faɗar haka yayi wuccewarshi, basan lokacin da kuka ya kwace min ba, alkyabbana nasaka na fito daga falon bayi suka shiga tare da tattare gurin tass.

        Ban kuma ganinsa ba sai ana gobe ɗaurin aure sai gashi tare da ibrahim,  inda suka so ganina ni kuwa naki zuwa. Tunda auren ya rage wata guda aka fara min gyaran al'ada irinsu dilke wanka da madaran shanu, ina bani safe da yamma. Da abubuwa duk yanda naso kaucewa haka bai samu ba.
        Ranar jumma'a aka ɗaura aurena tare da Bamai. Ji nayi kamar na cire zuciyata nayi wurgi da ita, tanadin da nayi mishi kuwa sai Allah.
              Ana ɗaura auren aka kaini falon Lamiɗo yayi min nasiyya mai shiga jiki sosai sannan aka kaini ɗakin sauran matan suka min faɗa, uwar gidan lamiɗo ita ta kawo ni har Maiduguri. Inda ta damkani a hannun Nanah Asiya.
    Nan ma wani bikin akayi sosai, washi gari dangina suka koma. Nayi kuka har na gaji. Tunda aka kawoni ban kuma ganin fuskarshi ba, sai ana gobe zai koma lag ya shigo yasame ni, Ina aikin kuka zama yayi a cikin ɗaya daga cikin kujerun falona na biyu.
        "Fulani Nafisatuh! Yaushe zaki kasheni? Gashi ni tafiya takama ni, zan koma bakin aikina da fatan babu matsala."

            Ba tare da wata matsala ba ya mike zai fita nace.
"Allah yasa idan katafi ka mutu a can, nima na huta. Naje na auri wanda nake so."
     Bai ce min komi ba yayi tafiyarshi. Haka na cigaba da zama a gidan, Rafi'a da Fatima ke shigo min, sabida suma ba'ayi aurensu ba, maryam da Karima akayi aurensu lokacin.
            Tsakanina da Allah nake faɗa musu ni bana son Yayansu, tsabar wauta, jin haka suka faɗawa Nana Asiya, ta kirani tayi min jirwaye. Amma dake bani da hankali ban fahimci komi ba saima haushinta da naji.
     Bayan kwana biyu Gimbiya Amrah takirani naje, nan ta shiga niman bugun cikina. Take nasiyyar lamiɗo ya dawo min tare da abinda Nana Asiya ta faɗa min nacewa karki yarda Fuskarki ta zamewa magautarki madubin dubawarsu.
      Haka ma Nanah Asiya ta faɗa min, karki bari wani ya fahimci alkiblanki, ki zame musu hawainiya.
               Tabbas Gimbiya Amrah tasan bana son Bamai, amma ni da bakina naki faɗa mata, sai tace min.
"Idan baki son shi, ki faɗa min a rabaku, dan nasama miki adalci. Idan kuma kina da dabara ma zaki iya faɗa min, sai mugudu tare mu tsira tare."
       Na buɗe baki zanyi magana kenan sai ga Kanna ya shigo dole na gyara zaman alkyabbana na mike tare da ce mata.
     "Ki gafarce ni, zan koma ɓangarena."

            Ina komawa shashina aka turo min wasika daga Gimbiya Aisya.

        *Nafisatu ki kame harshenki da furta abinda zai saki kuka nan gaba, bazan saki kiso Bamai ba sai dai ki kiyayye shiga hurumin, wasu daga cikin wannan masarautan kukan kurciya...*

   Da wannan ta rufe maganar, dan dole nasaka, wasikar a gaba ina kara dubawa.
            ......Bayan fitata bina da Ido Kanna yayi tare da shafe fuskarshi ya kalli mahaifiyarshi yace.
"Wannar itace matar Bamai? Gaskiya an nuna min son kai, taya za'a nimo mishi wannan mai zubin larabawar, kinga mace ga kyau ga halitta ni gaskiya zan taya shi rikonta kafin ya dawo, ko ta yarda ko karta yarda zanbi ruwa da iska nadira na barje gumina dan tayi min na karshe, kuma kana ganinta kaga ɗanya jagwab."
       "Kai wani irin shashasha ne, ina zaka fara wannan haukar, kaida muke kokarin nima maka damar zama sarkine kake niman ɓata rawanka da tsalle baka da hankali." ta faɗa mishi.
   "Toh miye laifina dan naga kayan hutu."
        A fusace ta nuna mishi yatsa tace.
"Wannan mahaifinta shima yana daga cikin sarkin yanka, kuma mahaifinku yayi wannan haɗine domin duk lokacin da aka nime....."
          Vote yayi kasa ainun fa....na kusan ajiye burutun ma na huta....

YAR GIDAN YADDIKO🧕Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora