29

5.4K 817 86
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

        *Aslm Yan uwa da fatan kuna lafiya wato anata bidiri NA mai dambu ta haihu a'a bani Ce NA haihu ba Sister Fiddo ta haihu, Nagode sosai.... Da kulawarku*😹

Page.29
       *****
    "Zamu barta a nan kafin naɗin sarautar, sai tazo idan muka tafi da ita wani tashin hankaline zata zauna ta sami koda nutsuwa ne, sai a kawo mana ita."
     Dadda ya faɗawa sarkin bauchi, jinjina kai yayi cikin jimami da halin da nake ciki.
      ....... Suna gama tsayida maganar Dadda yafito, tare da Mai martaba. Jikin Mamie a sanyayye ta kalle Dadda wani ɗaci take ji a ranta, bata iya tambayarshi ni ba, tashige mota abinta. Dan tasan tunda suka fito, ba dani za'a koma ba.
         Sallama sukayi shima ya shiga motar ya zauna, tare da Abdullah. Ita kuma riƙe da Amaturahmam.
        Suka bar cikin garin bauchi zuwa airport,
              Jirgin da aka kawo mu ptivete jet ne, dan mallakar Dadda ne. Na kanshi, har suka shiga jirgi Mamie taki magana, riko hannunta yayi, dama kamar jira take tasa mishi kuka sosai, murza hannunta ya shiga yi kozatayi shiru, kamar kara mata karfin kukan akayi. Zare hannunshi yayi daga gareta ya juya abinshi bai kuma ce mata kala ba, asalima jijjiga Abdullah yaƙe cike da kulawa dan ya fuskanci so take tamai dashi karamin mutum.
         Kifa kanta tayi a jikinshi tace.
"Abubakar! Kayi hakuri bazan kuma magana akan Khadijah ba, shi knn."
          Banza yayi da ita, dan ya fahimci idan ba zama namijin duniya yayi ba, tabbas zata lalata mishi komi akaina. Janye hannunshi dan ta riƙe hannun tana kuka yace.
"Banga amfanin kukanki ba, Yarinyar nan dasu tasaba, amma kin ɗauki kishinsu kina son juya rayuwar Y'arki sama ya koma kasa. Kasa ya koma sama why Nafi? Kin zata ke ɗaya kike san ciwontane? Nima naji zafin yanda naga sun mata, amma ganin yanda son shi ya rufe mata idanu yasani janye kudirina akanshi. Matuƙar suna son junansu ni zan bar mishi matarsa dan bansan miye Allah ta tsara ba, ki fita hanyar batun Khadija da mutanen can."
          Tsura mishi ido tayi, a ranta tana jin ba daɗi tace.
"Amma Bamai! Baka ga yanayin family bane? Sannan kuma ni banga zasu iya rike min Y'a? Nawa ne arzikinsu? Mi suka tara ? Bamai gwanane ya nemawa D'anshi Naufal auren Khadija, ni banga wani arzikin da Yaron yake dashi ba, idan kuma sun nace su bada gwal ɗin miliyan biyu.?
           Baki sake Dadda yake kallon Mamie, al'ajabi yake da jin abinda ya fito bakinta, murmushi yake yayi mata sannan ya cigaba da girgiza Abdullah. Dan yayi imani matuƙar yace zai mata magana ɓoyayyen ɓacin ran da yake ranshine zai bayyana, ya kuma santa da mugun taurin kai, sai hakan ya iya kawo musu hatsaniya.
             *****
    Farkawa nayi sakamakon kiran sallar magrib da ake, yasani b'uɗe idanuna. Tashi nayi naga bayi sun kewayeni, alamar ni suke jira na tashi. Mikewa sukayi cikin girmawa Babbarsu tace.
"Ranki shi daɗe! An samu mu zauna ne, har kitashi. Sannan mu kaiki ɗ'akinki."
          Lumshe idanuna nayi, can kasar makoshina nace.
"Muje."
         Mikewa nayi na bi bayansu, suka sadani da ɗ'akin da aka kawata shi da komi na ciki, golden ne, ban d'aki na tambayesu suka nuna min, na shiga nayi wanka da alola na fita.
      Doguwar rigar arabia gown nasaka tare da hijab nayi salla, ina idarwa na b'uɗ'e jakata na shafa mai sama sama, sai turaren Ajmal Ahlaam da Sultan Alshabab, na shafa su.
         Sider bag ns rataya na fito har ɗakin Uwar gidan Mai martaba Mama Fulani, na gaida ita. Kaina a kasa na rasa karyan da zan mata can ta kula da haka tace.
"Kina son zuwa asibitine?"
  A razane na ɗago kaina,  murmushi tayi nima sunkuyar da kaina nayi.
    "Karki jima a can, sannan akwai abincin da zaki tafi dashi, Allah yabashi lafiya."
       "Nagode." nace mata,
     Sautin murmushinta kawai naji nasan ta amshi gódiya, sannan na mike, nasami abinci kusan kwandona h'uɗu, sai bayi yan mata h'uɗ'u, suka ɗauka min, ɗakina na koma nasanya takalmina gyara zaman gyalena nayi na fito.
              A hankali muke tafiya, har gurin ajiye motoccin, buɗe min kofa akayi na shiga, yan matan suka jera abincin awata mota na daban, mota uku aka ɗauka ɗaya bayin da zasu rakani ɗaya kuma ni ɗayata sai ɗaya dogarawan da aka umarcesu da su take min baya.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Donde viven las historias. Descúbrelo ahora