22

5.2K 366 19
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.22

Ajiye hannunshi yayi tare da barin gurinta ya tawo ɗakina.
          Yana murɗa kofar yasame ni a zaune, na dunkule hannuwana na ɗaura fuskana akai. Narasa wani irin hali nake ciki, zama yayi a bakin gado ya zare hannun yace.
"Mamana! Tunanin mi kike? Bayan gamu nan,"
          Murmushi nayi na matsa jikinshi ina sauke ajiyar zuciya sannan nace.
"Dadda! Ban tsamanci haɗuwa daku cikin sauki bane, ban kuma san mi Mamie take rokona akai ba, amma koma meye Dadda ka amince nima naje naga dangina, zanyi alfahari da ganin dangina."
          "Allah yasa karki ɗauko halin Mamienki rigima, zamu tafi dan nima ina kewar mahaifata bari naje gurin y'an uwana." inji shi,
         Gyaɗa mishi kai nayi, ya fita.
     Mikewa nayi na nufi ɗakin Mamie, zama nayi a gabanta a kasa.
         "Tashi ki zauna a bakin gado." tace min.
        Tashi nayi na zauna, ina kallon kanena mafi soyuwa a rayuwata.
              "Mamie! Mi yasa aka rabani daku garinku? Mi yasa suka sace ni? Mike faru da Dadda baya son komawarku garinku?"
       Cire kanta tayi daga bawa yaronta nonon da take ta kalle ni sannan ta maida hankalinta kan bada nonon, kafin tace.
       
     *_Masarautar Elkanami_*

             Masarauta ce mai daddeɗin tarihi tun kafin zuwa Bayajida, domin an sami wanda ya fara kafa masarautar amma batayi karfi ba, har zuwan Bayajida. Kafuwar daular Usmaniyya yakara wanzar da masarautar inda aka fatatteki masu rike da garin sannan aka shimfiɗa daular musulunci.
         Zamani zuwa zamani ana gudanar da mulki cikin tsarin musulunci har zuwan turawan mulkin mallaka.
            Har zuwa lokacin da kakanki sarki Muh'd Abubakar Elkanami, adalin sarki mai karamci da adalci tare da rikon talakawarshi, Sarki Muh'd yana da mata uku.
               Gimbiya Amratu yar sarkin Bama, itace uwargida, tana da yara biyar mata huɗ'u namiji ɗ'aya,, a cikin yaran Yarima Usman, Gimbiya Kulsum, sai Gimbiya Zainab, da Gimbiya  Safina, Gimbiya Karimah, y'ayanta kenan, mace ce mai mugun kishi da izza, da jin kai.
      Kuma ita burinta a duniya ɗ'anta Kanna ya gaji kujeran mahaifinshi tunda shine babba.
      Sai Gimbiya Nana Asiya Y'ar sarkin Kano, tana da Yaranta huɗu maza biyu mata biyu. Mace ce mai matuƙar kirki da tausayn na kasa da ita, uwa uba kyautatta alakarta da kowa, sannan tayi kokarin ɓoye kishinta akan komi
        Gimbiya Zaituna sai Umar sarkin Yanzun(Mahaifin Annur) sai  Yarima Ibrahim. Sai Gimbiya Rafi'a.
              Sai Mahaifiyar Dadda, Gimbiya Khadija Y'ar sarkin Bauchi(Eh mana, tunda abin nayi ne muma sarkinmu ya shigo jerin gwano😎)
            Yaranta uku ne  Yarima Abubakar, Gimbiya Maryam, sai Gimbiya Fatima. Gimbiya khadija itama bata da matsala asalima bata ɗauko halayar masarauta ba, haka yasa nasu yazo ɗaya da gimbiya Nanah Asiya.
       A cikin wannan zaman da suke gimbiya Amrah taso juyasu, Nanah Asiya tace bata san wannan batun ba, ita tafito daga masarauta mai girman daraja, a cikin nahiyar Africa. Masarautar kano dan haka babu macen da zata juyata, rigimar da takai har gaban Sarki Muh'd. Da ya zauna ya fahimci maganar Asiya sai yaga tafi Gimbiya Amrah gaskiya, amma dan a zauna lafiya sai yace.
"Ina niman zama lafiya da fahimtar juna a tsakaninku, sannan kuma abu nagaba shine, Amrah itace gaba daku ina ganin idan kuka girmamata kamar ni kuka girma, don Allah ku zauna lafiya."
          Gimbiya Amrah bata so wannan maganar da yayi ba, taso yace dole sai sun bita. A ɓangarensu Asiyah kuwa gani suke kamar ya nuna fifiko, dan haka Nanah Asiyah tacewa Khadijah.
       "Bazamu bita ba, dan masarautar da tafito bai kama kafar namu ba, idan tana son mubita ta ajiye izza da jinkai."
    Da wannan suka ajiye maganarsu.
             Tunda Gimbiya Amrah ta haifi Usman Kanna, ta sake ɗauko wani fitina ta ɗaurawa kanta, na uwar sarkin gobe dan har tana kirashin da Magaji, haka bai dami. Nanah Asiya ba dan lokacin tana ɗauke da cikin zaituna.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now