25

5.3K 512 47
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*
    😹😹😹😹
      *Ummu Khadija sakonki Ya iso hannuna ki duba kasar pagen 👇 zaki sami amsarki a gurin nagode sosai😹*
Page.25
              A gigice aka shiga niman yarinyar babu ita babu alamarta, karshe aka rufe masarautar ko za'a sameta, amma babu ita ba mai kama da ita. Tsakanina da Bamai ido dan yak'i amayar da fushinsa, asalima cewa yayi a kaini can ɓangeren da ake kiwon dabobbi na zauna.
           Kwana uku, duk na kara fita hayacina ga nonuwana da suƙe masifar ciwp, dole aka sakashi a gaba ya dauko ya dawo dani.
           Ba tare da wani damuwa ba ya cire rawanimshi ya ajiye akan kujeran, sannan ya mikawa shamaki takardan sakin Mariya da Amina.
       Sannan ya fito daga fadar ya tawo Shashina, ina kwance sabida zazzaɓi tunda nayi wanka, na saka kayana na kwanta a gurin. Yana shigowa ya ɗagani na zauna sannan ya ɗauko takalmina da alkyabbana yasaka min, sarkafe hannuna yayi da nashi sannan yace.
    "Ban ga laifin kowa ba sai naki, sabida ai natura miki sako ko? Toh mi yasa kika tawo min da y'a kinyi kuskuren da bazan iya hukuntaki ba, amm..."
             Kuka nake sosai kaina a sunkuye nace.
"Kayi hakuri ni kaina ina jin tsanar kaina, don Allah karka yi fushi dani, kabar ni naji da laifina."

   D'agoni yayi ya rungume ni, sosai yana shafa bayana har nayi shiru, sannan yace.
"Zaki bini mutafi."
    D'ago kaina nayi tare da kallon fuskarshi na shafa sajenshi nace.
"Duk inda zaka ina tare dakai."
         Lumshe idanunshi yayi yaja hannuna muka fita, duk wani babba da yake da mukami a masarautar ya mishi magana amma bai ce kala ba, har muka bar gidan.
        Jirgin lagos muka bi, zuwa gidanshi na Ekoyi, satinmu biyu muka bar kasan, inda yasamu aiki da United state.
         Munyi yawo sosai a kasashen waje, a u.s nayi degree na na farko a fanin girke girke, na biyu kuma nayi a Dubai a fannin econemis, har izuwa lokacin da muka dawo nan da zama yana aiki da babban ma'aikatar jerage na kasar nan, sai dai duk inda muka je yana tuntuɓer Y'an uwanshi, kuma suna zuwa dan har yanzun bawai yayi murabus bane ajiye musu sarautar yayi ya shiga niman abinda zai dogara da kanshi, Mahaifin Annur shine sarki Umar, yan matan da suka koma kwanakin baya khairat Y'ar Ibrahim ne, sunar Nanah aka sa mata. Ita kuma mubina yar kanwata Asma'u ce.

                Kinji yanda aka sace mana ke, bawai dan bamu sonki bane sai dan rashin jina da nayiwa mijina, kuma har yanzun ina taɓa halin sai dai ba sosai ba dan bana son ganin nacin ranshi shi yasa na watsar da komi.

                   Share kwallar dake bin fuskana nayi sannan nace.
"Kenan  mutanen da suka satoni ne suƙayi hatsari har yaddiko ta ɗauke ni."
          Rike hannuna tayi, sannan tace min.
"Faɗa min suwaye Yaddiko da Maheer?"
       A hankali na shiga warware mata yanda suka rike dani da irin wahalar da na basu, murmushi tayi sannan tace..
"Zamu koma ai, kuma zanje mu ga mutanen kirkin da suka rike mana Ummi Aisha, tunda da sunar kika tashi."
        "Sannunku da gulmata, dan
kunga bana nan ko."
     Zuwa yayi ya zauna a gefena suka sani a tsakiya sai suka bani dariya, zanewa nayi na gudu ɗakina tare da faɗawa gado ina kukan farin ciki, ina fita ya janyo matarshi jikinshi ya shiga shafa bayanta, yace.
"Yanzun naje asibitin da yaron nan yake aiki suka ce min ya koma naija, kuma na fahimci Ummi Aisha tana kewarsu sosai,kodan ita zan koma kasata a karo na farko."
            D'ago kanta tayi tana murmushi tare da kai hannunta fuskarshi tace.
"Nagode haske rayuwata."

    Sumbarts goshinta yayi, cike da farin ciki.
      ****
    Tension ya haye mayyer fa. ga Yaddiko da tasako shi gaba, ga Mama itama da ta watsar da batunshi, wannan kaɗai ya hana shi rutsawa.  Kwatin kayanmu yaje ya buɗe ya ciro rugunan barcina ya saka a gaba, yayita sunsunar kamshin turarena, ko ta cikin sailuba baya yi, shi tani yake.
                Kullum sai ya tuntuɓe hukumar Germany, amma babu wani sako. Hankalinshi yayi kololuwar tashi, dake miskiline ɓoye abin yayi kamar bai damu ba.
          Yau ya fito zai je motsa jiki sukayi kicibis da Mutuniyar tashi, wani lalatacciyar kallo tayi mishi, kafin ta furza goran bakin tace.
"Makiri mugu ɗan wofi, Insha Allah yanda kuka rabani da Y'ar mariniyar Allah, sai kaima Allah ya nuna maka ɗan banza mai suffar bishiyar kuka."
  Tana gama faɗar haka tayi wuccewarta tana zazzaga bala'i.
   Ko kallon inda take bayyi ba, asalima sunkuyar da kanshi yayi, cike da damuwa.
         ......
    Kwance yake a kan doguwar, yayi nisa cikin tunani, binta ta taɓa shi, buɗe idanunshi yayi wanda suka koma ja, ɗagowa yayi ya zauna yana kallonta.
      Cikin sanyi murya tace.
"Ya Najib kaifa likitan zuciya ne? Mi yasa kake damun kanka da tunani ne."
        Murmushi yayi sannan ya kalle cikin idanunta yace.
"Fatima! Ina son Aisha amma Umma ta rabani da ita, abu mafi ciwon shine yanda Maheer da Yaddiko suka wulakantata."
    Rufe mishi baki tayi tana girgiza kai kamar zata fashe da kuka tace.
"Ya Najib nasan ka karɓi aurena ne badan kana sona ba, amma ina maka fatan Allah ya baka macen da tafi Aishatu, don Allah ka rage damuwa."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now