3

6.7K 452 15
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....

_Kuyi hkr na dakatar da Da'iman-Abadan_👏

*Sadaukarwa Ga Aisha Alto*

Kyautar Farko gareku...
Deejer A Chiroma
Ummu Hajra
Ummy
Maryam Candy
*Da kuma member Musha karatu Mmn Sadiq, Action Lady, Nancy, Da Baby Maryam, Yar Yaddiko tace Mahaaaaa😹*

_Akwai Wacce tayi min sticker na suna jiran Yar yaddiko Ina miki fatan alkhairi nagode_

Page...3

"Kaiii Mahar bana son ɗibar albarka, yarinyar ce xaka nemi murkushewa, gafara can."
Yaddiko ta tare shi kafin yace zai iso gareni.
Leka shi nayi tare da zaro harshena nace.
"Yo Yaddiko Yaseen sunar mayye fa, kaii gaskiya kice a sauya sunan."
"Kee tafi can bana son rigima."
Sauka nayi cinyarta na shige gurin Akuyoyina dan naji haushi gwaleni da Yaddiko tayi.
Ina shiga ciki naga faratu ta zabga min harara.
"Kwal Ubanca Faratu ni kika harara."
Kaɗa min wutsiya tayi alamun tayi ɗin, kallon Uwar garke nayi cikin jin haushi nace.
"Yau rahin mutuncinku kaina zata kare."
"Burrrrrrr."
D'an maraya yayi min, cikin jin haushi nace.
"Kundun Ubanku, kuma a bakin abincinku."

Ya Najib na tsaye sai dariya yake yana karawa, ganin na fito a fusace yasashi riko hannuna kwacewa nayi na fashe da kuka.
Ina da wata ɗabi'a shine kishi bana son naga wani ya kwace min abuna ko yakusanci abinda nake so, daga zuwan mayyen can har ya lashe zuciyar Yaddikona.

Rikoni yayi yace.
"Faɗa min mi aka miki."
Cikin zallar yaranta nace.
"Daga zuwan mayyen can har Yaddiko ta fara min faɗa, bata taɓa min faɗa ba."

"Toh kiyi shiru, zan baki alawar birni ko baki sone."
Cikin jin haushi nace.
"Kaga yau har faratu hararata tayi."
Rike baki yayi cikin dariya yace.
"Amma Faratu bata kyauta bawa Aminiyarsu ba, amma naji kince a bakin abincinsu na rana."
Gyaɗa kaina nayi, kallona yayi sama da kasa, bani da makusa tsaf nake kamar ba yar kauye ba. Toh taya zanyi kazamta tunda Yaddiko ce ke min wanka, kuma har almiski take ɗigawa a ruwan wankar, Ni ba fara bace ni bakace amma ina da kyau mai shiga rai, gani da gashi har goshina zuwa saje na ya kwanta, sannan bana kitso dan tun ban kai haka ba aka daina min kitso, amma kullum sai Yaddiko ta wanke min gashina ta tufke, sabida gashine dani kamar ɗiyar turawa nan kuwa bakace ni.

Duk wani abu sabon yayi a jikina ake fara gani, sannan yaran gari, kai nifa ba'a gasa dani.

Komawa kasar bishiyar mukayi na zauna ina kallon yanda Yaddikona ke girki cikin gwanancewa da tsafta.

Dariya nayi nace.
"Mai kama da Sahabi, Ina son Yaddikona ta iya girki.
"Hmm Ummu Aisha haka zaki je gidan mijinki ki masa girki mai daɗi ko."
Washe hakorana nayi, farare wanda kullum sai Yaddiko tasa gawayi ta gurje minshi.
Nace.
"Hmm aure kuma Yar karama dani."
Basar da zance yayi ya cigaba tambayata a mkrnta nan yaga tsabar surgududu, dan bana fahimtar komi, sai tsabar shiririta da shirme, mikewa yayi sakamakon fitowar Mayye, ɗaga kaina nayi na kalleshi ya zabga min harara, ni kuma na murguda mishi bakina. Nace,
"Kurwata kurrrr, babu mayyen da zai iya cinye ni." zaro ido yayi ya kaɗa kanshi ya ficce nima na tashi na ɗibo ruwa a gwangwani, sai lokacin Yaddiko tace.
"Shatuwa zoki rike min miyar nan sallah zanyi."

"Ki jirani nayi sai nazo na amshi girki."
Kamar da gaske nagama jika jikina na wucce ciki.
Karku damu kanku da sanin irin sallata, dan na doka goshi a kasa yafi sau goma, sannan na kwaɗa sallama nafi. Waje,

"Shatu wannan dai ba sallah kikayi ba. Kwaɗa goshi a kasa kikayi."
Tace min.
Kamar zan fasa ihu nace.
"Yaddiko sallahce mana, nayi naka'a sama da goma da asuba nayi goma ynx nayi goma, an jima nayi goma."
Shigowarsu Ya Najib yana dariya yasani cika fam, shikan mayye baikula mu ba yayi shigowarsa, magana yayi min naki kulashi. Sai ya shige falo abin shi,

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now