15

5.8K 432 23
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

     *Aikin kenan.....Mai_Dambu Ƴar Yadikko😂*

         _Maman Gid'ad'o da Jamila Yakasai ga naku nan, saki ne dai baza'ayi ba dan Yar ɗakina bazata dawo ba...Team Sailuba😂_

          '''😯😯😯😯 shiru ayi karanta kar ace komi'''
Page.15
Wani jahilin duka Ya Maheer yayiwa sailuba, wanda yasata zubewa kasa ragwab kamar ɗanye Nama.
  Fita yayi daga ɗakin ya shiga nashi wanka yayi dan hannunshi na masa zafi sosai, yana fitowa yasaka kayanshi ya dawo ɗakinta.
   Ruwan sanyi kalau ya kwara mata, wanda yasata mikewa a firgice mike shake mata wuya yayi yajata zuwa ban ɗaki, ya cika ruwa a baf ya tura kanta kamar zata mutu, ya ɗago kanta yace.
"Waye Ya wurgo Aisha daga sama?"
              Shiru tayi taki magana, bai wani damu ba, dan yana matukar zarginta tunda ta iya zuwa ta cire na'uran da aka samin yake kara tabbatar da zarginshi.
  Sake nutsar da kanta yayi sosai a cikin ruwan, sai da yaga ta kamar numfashinta yana niman tsayawa, ya ɗagota yace.
"Tambaya a karo nabiyu waye ya wurgo Aisha daga sama."

     "Ni....ce don Allah kayi hakuri bazan kuma ba." saketa yayi ya fita daga gidan.
            ****
   Sai da nayi kamar sati biyu a kwance, sannan na suma motsa kafana daga nan ne kuma na shiga motsa jikina.
     Har na buɗe idanuna, dumm naji kaina ya amsa, rufe idanuna nayi.
        Na wani lokaci kafin na sake buɗewa.
                Tunda na farka bana magana sai bin kowa nake da ido har aka cire min wayoyyin jikina,, duk kallonsu nake kamar baki. Abin ba karamin damun Yaddiko yayi ba.
          Bansan jin fitsari ba ko wani abu ba, sai dai a gani a jikina haka ba karamin gigita Yaddiko da Ya Maheer yayi ba. Har aka sake tunanin min wani aikin.
     Ya Maheer yace a'a a barni Allah yana sane da al'amarina.
        Sallama ya nima min muka dawo gida, wanda yake ɗauke da kayan alfarma dan ya zuba komi a gidan,

           Daga shi sai yaddiko suke kula dani, a ɓangaren Ya Najib shima ba laifi kafar shi ta fara warkewa amma dole sai ya zauna har wata uku.

                A ta ɓangarena kuwa, ba laifi jikina yayi kyau. Kai dai rashin hankaline matsalar. Domin yanzun bansan miye zai cutar dani ba bansan mai zai min mai kyau ba.
                 Ga baki ɗaya nazama doluwa, kuma bana juran tsawa ko ihu, zan fashe da kuka ga uban son jiki musaman Ya Maheer da nake makale mishi kamar kuliya.
            Sam baya ta Sailuba dan bata gabanshi tani yake, da alamurana.
               Ga Yaddiko da take zama tare da Binta a asibiti. Idan Ya Maheer zai tafi dani yake tafiya sabida yana ganin barina a gida kamar risking ne.

              Ya maheer yana da matukar hakuri da juriya, dan makale mishi da nakeyi yasashi jin damuwa.  Sosai har takai ya kai hannunshi jikina ni kuma idan naji haka sai nayita dariya.
         ........
     Yau bai fita aiki ba, Yaddiko yakira taxi ya kaita asibiti ina kwance a gadonmu.  Har sha ɗaya ina barci. Yunwa ce tasani farkawa da kuka, dama haka nakeyi idan yunwa ya dameni kuka nake. Fitowa nayi daga ni sai rigar barci iya gwiwa, dakyar Yadikko tasamin dan kamar cizona kaya yake, duk d'abi'ar yara nake musu irin yan kananun nan, masu shegen fitina.
      Ina fitowa na nufi kitchen kuwa dan naga tanan ake ɗiban min abinci ina shiga naganta a tsaye, dake ban cika ganinta ba, sai muryanta.
         Kallonta nayi ina son tuno fuskarta, wucceta nayi na janyo flask sai tussss ya faɗo kasa, alamar tsorone ya kamani.
Na kalleta tare da kankance idanuna sannan na tura mata baki, ina murza idanuna.
         Kama kunne na tayi ta murɗa shi sai da na fasa ihu, da sauri ta sake. Ihuna ya fito da Ya Maheer da sauri ya shigo kitchen ɗin da sauri na faɗa jikinshi ina sauke ajiyar zuciya, shafa kaina yayi yana kallonta, fuskarshi ba sauki ya kankance idanunshi yace.
"Uban mi tayi miki."
    Kamar zatayi kuka tace.
"Ya Man! kalli kasa fasa flask tayi fa kuma."
      "Ya isa koma me tayi kece zaki ɗauka tunda mugun halinki yasa take cikin wannan halin, idan baki bi a hankali ba sauran igiya biyunki zasu dawo hannunki."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now