33

5K 796 58
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

    *_Kalubale baya karewa da zaran kace zaka aza hannunka domin rubutu sannan ina ga rubuta labari ayi a kare  babu Ayan wa'azantarwa takar ɓata lokaci, Mufa ba indiawa bane da zamuyi rubutu ya kare a love zalla. Saki dai halattacene kuma mutuwa Aya ce, duk rayuwar da babu mutuwa toh ba rayuwa bace. Sannan mu Y'an arewa ne inda muke da bila'adadin Zawarawa da Yan mata, Shin kin taɓa tunanin miye Ya kashewa D'ahare aure, shin saki nawa Yayi mata, nifa Ina da banbanci d'abia ni ban muku karyan yafi kowa kuɗi ba, Sannan bance muku Yayi kama da bature ba, Asalin Maheer na ambace shi daga kabilu guda biyu ne, Fulani da Guduri mutanen Yankin katagum, Ita kuma Shatu na ambacetane daga Yanki Barno da Fulanin Yola, bata kama da wata Actress ko celebraters sabida nasan yankin da nafito Northeast. Duk buks ɗina ina alakanta Jarumai na da Zamansu fulani ko bahaushe_*

 
  *Sister Seelat Gadara sakonki Ya iso ina mika ta'aziyar Mutuwar Najibullah karku manta Ummanshi ta roki haka, Allah ka jarrabemu da abinda zamu iya ba wanda bazamu iya ba mutuwa ayace sukutun da guda Allah ya saukar da ita a surori da dama cikin alkur'ani, hakan yakansamu mu halkanta da rayuwarmu Allah kasa mucika da Imani, Ina mika sakon Ta'aziyana ga matan da suka rasa Mazajensu da Uwayen da suka rasa Yaransu da kanen da suƙa Rasa yayunsu, da kuma muma Yaran da muka rasa Uwayenmu mata Allah ya gafartq musu yasa Aljanna ce makomarsu👏*

Page.33
"Anya kana son Najib kuwa wallahi bai mutu ba ku barni naje ga d'an uwana."
      Rungume shi Abban Ya Najib yayi cikin murmushi yace.
"Duk son da nakewa Najibullah Allah yafini sonshi, duk kaunar da zan mishi Ubangiji yafini juya kaga fuskarshi, Juya kaga irin annurin dake kan fuskarshi. Najib ya roki Alfarman karmu zubda mishi hawaye akan mi zamuyi mishi kuka bayan ya nime karmiyi mishi idan kana son abokinka jekayi mishi bankwana, da haka zaka nuna mishi duk wata kulawa. Tashi Najib Allah ya amsa ina da kai Baba bana jin komi sai abinda baza'a rasa ba, jeka kaga Amininka, wanda yace min Abbana idan natashi sai na nimowa Maheer ɗina matarshi koda zan rasa rayuwata a sanadin haka. Abba ina son Maheer. Gashi munyi tarayya akan abu guda, sai dai ni nasadaukar mishi da Ita dan nasan ba matata bace ita Matar shi ce, kaji abinda yace toh kukan mi zaƙayi bayan muma mutuwar tana kusantomu."

    Lumo yayi jikin Abba yana zubda kwalla, shi knn Najib ya tafi yabarshi.
             Yana ji yana gani akawa Najib sutura aka fita dashi daga gidan, ajiyar zuciya yake saukewa a hankali.
       Karshe ya kwanta a gurin, bayan fitar Abba.
      Barcine ya soma fizgarshi ya tsinkayi muryan Mamah tana cewa.
"Bazaka mishi rakiya ba kenan? Mutumin da ya mutu da kaunarku, tashi kaje kaga inda za'a sakashi ya tafi."
    Mikewa yayi Mamah ta turo mishi, keken guragun. Ya hau a hankali ta fito dashi,  Ammar ya karɓe shi suka fita daga gidan.
              Mutuwa Ya Najib ta karaɗe ko ina har gurin Wakilin sarki ya turosu, basuyi kasa a gwiwa ba suka labartawa sarki nan yakira Dadda ya faɗa mishi. Yaji mutuwar sosai, bayan dadda ya koma cikin gidane ya faɗawa Mamie itama taji mutuwa, dan haka suka shirya ranar addu'ar Uku zasu zo.
.....
           Haɗa abinci muke irinta kwaɗayi aka miko min wayan Aunty Zaituna, Buhaina tana da waya Amma ni Fir mamie ta hanani riƙe waya dake nima ban wani damu kaina ba ban ko takura ba. Karɓa nayi na shiga gaida ita, nan take faɗa min rasuwar kuka nasaka tare da zama akan kujeran kitchen, a birkice nake kuka dan nasan irin son da Ya Najib yayi min, bazan iya mantawa dashi ba wasa wasa mutuwarshi sai da tasani na kwanta sosai har da karin ruwa aka min.
               ****
      Mamie bata samu zuwa addu'ar Uku ba, shima dadda bai samu zuwa ba sai ranar da za'ayi baƙwai yazo. Yayi musu ta'aziya, a nan  Abban Ya Najib suka bashi hakuri da abinda ya faru sannan aka ɗauƙo Ya Maheer. Gaisawa suƙayi sannan Abban Ya Najib yace.
"Baba!Sarkin Barno shine mahaifin Aishatu."
     Dukda a gigice yake da maganar mutuwar Najib amma jin wannan maganar yasashi kara kiɗimewa.
     "Kun sameta ne? Don Allah tana ina?"
      Duk lokaci guda ya jefa musu tambayarshi.
      Ganin Yanda hankalinshi ya tashi yasa Dadda yayi murmush, yace.
"Tana nan."
        Ya zubawa Ya Maheer ido, sauka akeken yayi yazo gaban Dadda kamar zaiyi kuka yace.
"Ka gafarceni! Nasan ban kyauta ba na ƙoranta amm."
          "Babana akwai matsala, dan an sami rubutunka da shaidan kasaketa."
              Abbanshi ya faɗa mishi.
    "Innalillahi wainna'illahi rajuon! Wallahi bani nasaketa ba ku yarda dani. Akan mi zan sake abinda nake so ku fahimce ni." Ya faɗa kamar zai fasa ihu.
        Gyara zama Abbanshi yayi ya zaro takardan, ya mika mishi tare da cewa.
"Rubutun waye ne wannan?"
      Jikinshi na kerrma ya amshi takardan. Ya kurawa rubutun ido kwallana ne suka shiga sauka daga idanunshi ya kalli Dadda sannan ya fashe da kuka kanshi a sunkuye , cikin  kuka yace.
"Rubutuna ne!"
             Tausayinshine ya kama dadda, yagyara murya cikin dattako yace.
"kwarai rubutunka ne, amma kana nufin kaine ka rubuta mata."
      Girgiza kai yayi cikin rawan murya yace.
"Ai bani da inda zan kare kaina, tunda ga zahiri rubutuna ne, sai dai nayi imani da Allah Najib kaɗai zan iya sakarwa Ummi Aeesha, bayanshi koda kasheni za'ayi bazan taɓa sake Ummi Aeesha ba, kuma Iyayena kune shaidana da zan saketa da nayi haka. Wallahi bani nasaketa ba,"

              Duk sukayi ana mamakin al'amarin,  cike da tashin hankali kowa ke jajjanta alamari. Karshe Yaddiko suka kira akayi maganar a gabanta, Allah sarki Ya Maheer ya koma wani irin yanayi ɗaura kanshi yayi a cinyar Yaddiko.
   Kan bala'i take gidan kowa ya tashi ya zauna, dan Yaddiko ta gigita kowa jin abinda ya faru.  Ga baki d'aya abin ya ɗaurewa kowa kai. Karshe haka Dadda yayi musu sallama,

            .......Fitar maganar sakin yayi mugun d'agawa kowa hankali karshe kiri kiri Umman Ya Najib ta juya magana tace wato dan umma suna bakin ciki da kar d'anta yayi nisan kwana shine aka ɓoye maganar sakin har ciwon son Shatu ya kashe mata D'anta toh In Allah yaso ya yarda, Maheer ya rasa shatu kenan har abada.
         Hajiya Sadik'a kan tana gefe tana kallon yanda ake kafta dirama,

                ****
    Bayan komawa Dadda gidane suna zaune.
      "Nafisatu!!!"
   D'ago kanta tayi tana dubanshi cikin mamaki tace.
"Lafiya?"
    Gyara kwanciya yayi sannan ya zuba mata ido yace.
"Munyi magana da Yaron nan Maheer, kuma ya tabbatar min da bashi yayi sakin b."
        "Ai haka ne? Kenan aljanune suka saketa kenan, hmm gwara ma ya hakura tunda yana da wata matar da wannan damanmiyar Famil...."
         "Bance kiyi min rashin kunya ba, dan na lura dake tsaf baki san halacci ba, sun rike miki Y'ar shine zaki saka musu da haka, idan akayi bincike aka gano bai da matsala zan bashi Matar shi dan, dasu tasaba."
     Karshe dai chakwakiyya mai zafice ta kafce a tsakanin Dadda da Mamie..

                 *****
      Lokaci yayi tafiyar bazata sosai dan har takai ana niman shekara guda da barina gida, ga mutuwar ya Najib da ta doshi wata kusan biyar.
                 Alhamdulillah sailuba ta haihu, tasami Namiji kirikiri Ya Maheer Yaki bata zaɓe ya saka sunan Najib. Shima yana fama da jinyar zuciyarshine, ranar suna zaune Mamah ta dube shi Najib karami na hannunshi tace.
"Zama zaka cigaba dayi a keken guragu, ka tashi kaje ka nemo matarka a maiduguri."
              Shiru yayi yana kallon Mamah, sunkuyar da kai yayi yana kallon fararren kafarshi sannan yace.
"Mamana! Kina gani har yanzun da aurenmu da ita?"
           "Toh kaine ka saketa knn?" ta jefa mishi tamvaya.
         Girgiza kai yayi cikin sanyi jiki tace.
"Tashi zakayi, kaje niman abinda ka fara."

    D'aukar Najib tayi har zata shige d'akinta tace.
"Shawara na baka ba umarta bace kayi dubi da zuciyarka."

            Bin bayanta yayi da ido kwallah ya cika mishi ido.
....... Tun daga ranar Ya Maheer ya fara koyawar tafiya, sabida kwanciyar da yayi kafarshi yayi sanyi.
           ****
     Alhamdulillah awannan shekaran na gama scndry schl, cike da murna na dawo Naija hutu ni da Buhaina. A lokacin na kara girma sosai, ga wayewa da ya shige ni tare da nutsuwa. Ƙaƙari mamie take gurin koya min, d'abi'a gidan sarauta kama daga magana, tafiya. Kai da duk wasu abinda ya shafi masarauta duk cikin hutun da nazoyi na wata biyu zuwa uku.
           ....... Lokacin da hutuna ya karene, muka koma inda na fara karatu. A jami'a inda na zaɓi karanta law dan shine nake ra'ayi kuma Dadda ya goya min baya.
                 *****
    A cikin watanin da yayi za'a iya cewa komi ya tafi mashi dai dai sai shirin tafiya maiduguri. Tunda Sailuba taji labarin ta fadawa mahaifiyarta dan haka hajiya Sadik'a ka koma gurin Bokonta aka sake murja amma abinda ya faɗa mata sai da yasakata kuka.
      "Yaron nan babu abinda, zai faru da shi sabida yana cikin kariyar Addu'ar Mahaifiyarshi, inda za'a sami matsalar sai ta gurin Uwar Yarinyar kamar yanda nace muku tun farko."

      Da takaicin haka tabar kauyen.
           ****
Yan tagwayen Mamie sun girma suma fa. A yanzun bani da wani matsala sai ta likitana.
......... Tsaf ya shirya ranar Jumma'a ya nufi Maiduguri.....

            Karku manta da Vote....Nd Follow:Mai_Dambu

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now