2

8.1K 491 16
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

   *EWF*

Reposting...

Mai_Dambu....

          _Kuyi hkr na dakatar da Da'iman-Abadan_👏

    *Sadaukarwa Ga Aisha Alto*

Page...2
     Kasake nayi ina kallon yanda mutumin yake magana, ɗan gemunshi nan sai wani motsi yake, girgiza kaina nayi cikin jin daɗi nace.
"Ahe a cikin mutane akwai masu kama da akuyoyi yo dubi gemun wancar kaman ta sahabi Allah sarki."

      Tattara dukkanin karfina na lafta a guje, ga uban kuran da na tadda. Kallona malam Dalha yayi ya girgiza kai yace.
"Ina ga gidan Yaddiko kuke nima, ga can takadarirrayar jikanta can tana tadda kura."

Tunda naga ya nuno ni, nayi kwafa a raina nace.
"Nasan za'a rina."
       A nutse na iso gurinsu na kalli malam dalha nace.
"Naga kana nuno ni? Ince dai lahiya? Da fatan ba wani hairrin za'a ƙulla min ba."

       Kallona bakon yayi cike da mamaki, kardai Shatun Yaddiko ce haka.
           "Ke tafi can shashasha, baki kukayi daga birni."
       Kamar wacce aka ce min ga baki daga kasar waje na wani washe jajjayen hakorana nace.
"Yo kace baki mukayi daga binni, toh kardai a kintsa musu wani hairrin dan nasan a garin ga banda Yaddiko ba me kaunata duk masu kaunata dan kuɗin Yaddiko suke kaunata, mutum yayi magana Kwarankwatsa idan yazo cin bahi nasa Yaddiko ta hana hi."

       Bai ce komi ba, yace.
"Toh bawan Allah ga Yar gidan Yaddiko nan zata kaiku har gida."
   Mika mishi hannu bakon yayi suka gaisa, ni kuwa na leka hannun cikin katsalanda nace.
"Karka wani bahi cin anci, kawai kazo muje."

     Da mamaki ya kalle ni, ni kuwa sai wani buɗe hancina nake, irin na zama wata a garin gumau.
    Cikin daddaɗar muryanshi yace.
"Toh kishiga motar mana."
    Juyawa nayi na kalle shi sama da kasa, nace.
"Yaddiko ta hanani higa motar mutane dan tace yan han jini ne suke cewa a higa motarsu, kagaku biyo ni sannu ahankali zan kaiku Unguwar gabar."

   Gaba nayi abuna shi kuma ya shige cikin motar, ya kalli abokin tafiyar yace.
"Man kaga yanda Shatun Yaddiko ta girma kuwa."
      D'ago kanshi yayi ya kalli mai maganar sannan yace.
"Sai ya."
      Dake yasan halin abokinshi bai kuma cewa komi ba yajasu suka bi bayana.

          Wani irin tafiya ake mai cike da abin takaici da ban haushi kamar abin arziki na ɓoye hali, muna cikin tafiya na hango. Audu ya sayo manja a leda, sai sauri yake zai kai a musu abinci nasha gabanshi nace.
"Yawwa nakama ka."
   Zaro ido yaron yayi cikin tsoro yace.
"Shatuwa, kiyi hakuri Iyata ta aikeni nasayo manjan alale ne."
"Kai tafi can haihaihai, kawai sai na durje bakinka da ka zagen kace min tinkiya."

      Hakuri ya shiga bani, na dalla mishi mari, kafin ya dawo hayacin shi na sami tsakiyar kanshi na zuba mishi rankwashi, sannan na ture shi manjan ya fashe.

          Duk dukar dana mishi bai ji zafi ba kamar fashewar manjan na kuwa tsinka a guje, karshe fitowa sukayi a motar suka ɗaga yaron, da yake kuka.  Biyanshi kuɗin manjan sukayi.

  A can gaba kuwa, ina zuwa dandali naga talatule da tiren gyaɗa,  Talle da kwanon dafaffiyar masara, xuwa nayi na tsaya musu nace.
"A bani alkoro ko nayi aikin."

            Banza suka min nasake nanatawa basu kula ni, fakansu  nayi na wafauce gyaɗa da masaran wanda yayi sanadin tintsirewar kayansu baki ɗaya.

         Koda na isa bakin kasuwa samu nayi ana dambe tsakanin. Hudu da Sanda. Sun yasar da kayansu na talle a gurin, dariya nayi nace.
"Mahaukata yaseen sai na ɗauki, yar yau da kosan rokon."
        Buɗe kayan nayi na ɗiba, aikuwa suka yo kaina na falfala a guje,

YAR GIDAN YADDIKO🧕Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum