11

5.6K 496 44
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
      *Wattpad:Mai_Dambu*

*Kaunarku a jinina Yake Zauren Mai_Dambu*
  
     *Mafi girman soyayyar da kuka min a rayuwa bazai bar zuciyata ba*
      _Maman Hanif, Mr Babana, Aunty Halima Habu nagode kaunar da kuka min_

Page.11
Mai da min gashin matar tayi cikin gyalena, sannan muka fito daga shagon har dare ya fara yi.
      Tura bakina nayi sabida banyi sallah ba, sannan gashi na fara jin alamar ciwon cikin da nake ya fara damuna.
        Shiga motar nayi jikina ba kwari, tun bamu bar cikin gari ba na saka mishi kuka sosai. Shi kanshi sai da ya birkice ya kusan duƙar motar mutane, komawa gefen hanya yayi ya daki kan motarshi ya kuma buga min tsawa.
"Kukan uban mi kike min? Mi aka miki? Sai kace yarinya karama kin sani a gaba da kuka uban mi zanyi miki mara kunyar banza dan kinga ɗazun ban miki komi ba ko?"
      Aikuwa nasake fashewa da kuka tare da riƙe cikina da hannu ɗaƴa, ina yarfe ɗaya hannu.
    "Ciwon cikine?" ya wurga min tambaya,
     Gyaɗa mishi kai nayi tare da tura mishi bakina, juyawa yayi muka koma wani babban shagon magani, ya sayo Allura da magani muka dawo gida,
   Zan fita yace.
"Abun ya saukone?"
    Duk fitsara na sai gashi ina jin kunyar bashi amsa, girgiza mishi kai nayi alamun a'a.

   Na nufi cikin gida, shi kuma ya nufi gurin abokanshi suka.
             Har sun tsareshi da hira ya tuna da alluran, yace musu yana zuwa.
            Ina shiga cikin gidan nasami har Mutanen katagum sun iso, gaidasu nayi na wucce ɗakinmu wanda ya ɗauke da yan mata cire after nayi na ware gyale. A gurguje na faɗa ban ɗaki nayi wanka da alola nafito.
     Har lokacin cikin yana min mugun ciwo.
                Fitowa nayi ɗaure da towel na same shi a tsaye yana haɗa Allura.
            Fuskarshi tam dan kar Yan matan su kawo mishi reni,
              Bubuga kafana na fara tare da rike towel ɗin nasaka kuka ina cewa.
"Nikam kafita idan na gama shiryawa zan zo kai min."

     Tsaki yaja, cikin alamar babu wasa a fuskarshi yace.
"Yaushe kika daina cire kayanki zaki zauna tsirara tunda anyiwa wasu, kayan turawa c'mmon my dear kizo nayi miki allura ina da abinyi fa."
                      Juyawa nayi zan koma ban ɗaki ya fincikone tare da zamar da towel ɗin ta gadon bayana yanda bazai faɗi ba, ya tsira min alluran yana gama jiyeta ya zare daga jikina ya fita.
      Zama nayi na cigaba da kuka abuna, me yan ɗakin zasu banda dariya wata Yar kanwar Mama Shahida tace.
"Allah Aisha baki da kunya kuka kike fa, kuma anan idan aka taɓa ki ur Ss1, ki bar yarinta don Allah kin girma."

          "Kyaleta tayi itace karama a cikin gidan nan sannan ko tayi abun kyau yake mata, Princess ɗin Ya Najib kike gani. Sakaltacciya Yar Mama, fitinaninyar Ya Maheer"
        Mikewa nayi dan nagaji da kirarin Hafsat, da kawayenta. Nasaka kayana sannan nayi sallah Ummi Yar Baba altine tace.
"Aisha! Mi yasa kikewa Ya Maheer rashin kunya? Baki san komu da muke Yaran kanen Mama bamu iya kallon tsabar idanunshi muyi mishi musu ba. Toh ki daina don Allah ke ba Yarinya bace, dan kinga ya damu da sha'inki ko."

         Kwal-kwal nayi da idanuna kafin na fara sauke wani munafikin kwalla nace.
"Ni ban masa rashin kunya ba, shine baya kaunata. Duk wani abin..."
"Dan ubanki taya zai kaunace ki, kalan dangi, wato dan munafuci da kutungwila shine ya kai ki shagari shoppinf complex, aka miki gyaran gashi. Toh yanzun zan yake dan banza gashi naga yanda zakiyi."
       Ko ɗar banji ba na mike tare da ninke abun sallar da nake kai, zan ajiye ta fincikoni.
   Na juya tare da tureta ta faɗi.
     "Kan Uba sailuba idan kika kyale shegiyar nan ta gama dake." Jin Hafiza kawarta.
                   Ban kuma bin takanta ba, na cigaba da hidimar gabana.
     Abinda nake, zare hijab ɗin nayi tayi tozali da jelar gashina a gadon bayana kamar kura haka ta kai min sura.
              Bansan mi ya sake faruwa ba, dan farkawa nayi a jikin Ya Maheer yana tofa min Addu'a.
              Kallonshi nayi tare da son tuno abinda ya faru amma babu hali lumshe idanuna nayi wani barcin yayi gaba dani.
      Ajiyar zuciya suka sauke dukkansu.
         Mama tace.
"Kenan da zaran an kaita bango haka zai na faruwa da ita? Amma ai babu alamar zaman junnu a jikinta, dan tun da Baffa ya dawo da ita ko ciwonkai bata kuma yi ba."
   Kamar baxai tanka musu ba, yace.
"Ai wanda baban nan yayi arangama dasu na matsafa ne, wannan kuma suna tare da ita tuntuni, kawai basa zama jikintane. Kuma basu bayyana kansu ba, damu dage mata ƙawai da nima magani, sannan kuma dai baku lura da ita bane yanda take wasu abubuwan Allah ya kyauta kawai."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Où les histoires vivent. Découvrez maintenant