14

4.6K 521 49
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.14

A sanyayye ya fito ofishin likitan, jikinshi kamar mugun duka, ya nufo ɗakin da naƙe kwance kallon halin da nake ciki yayi, sam zuciyarshi ba daɗi.

    Zama yayi a kujeran dake kallona, tare da sarkafe hannunmu, lokaci guda....
*miyasa komi yazo mishi a karkace ne, mi yasa lokacin da nake shirya rayuwata komi yake shirin lalacewa ne.*

     Da fashi Yaddiko tayi cikin sanyin murya tace.
"Duk wani tsanani yana tare da sauki, ka mikawa Allah alamuranka shi zai baka ikon cinye jarabawarka"
     *(Gashi dai nice na rubuta sai nake ganin kamar dani Yaddiko take magana😊)*
   
A raunane ya kalleta zuciyarshi ba yace.
"Yaddiko na gaza taimaka mata, mi yasa na sauka? na barta a ɗakin? Kuma nayi imanin ba ita ta turon kanta ba."

      "Allah yasan koma waye, yayi mata haka, mudai mucigaba da addu'a Allah ya ɗaga kafaɗarta."

     .......
   A ɓangaren Ya Najib kuwa anyi nasaran aikinshi shima, Binta ke kulawa dashi. Sai dai gefe guda zuciyarshi ba daɗi dan wani sabon soyayyata yake ji, gani yake kamar da gayya Ya Maheer ya barshi ya rufta ciki, miyasa tuntuni suka rufe shi bayan sun san cewa, akwai maganar Ya Maheer.

           Ga baki ɗaya ya ɗaukewa Ya Maheer wuta, ko ya shigo duba shi baya kula shi.
     Ranar sun tawo suka bar ni a ɗakin dan Ya Maheer ya gaji da halin ko inkular da Ya Najib yake mishi, shine ya faɗawa Yaddiko ita kuwa ta sako Ya Maheer a gaba, a ɗakin da Ya Najib yake.

          Suna bada Baya kuwa Sailuba tana zuwa ɗakina, tana shiga Dr ɗin da yake kula dani ya shigo a birkice ta juya dake shi uzurin gabanshi yazo yi, kawai ya gama dubani ya juya abinshi.

   Yana fita ta sauke a jiyar zuciya ta sauke, sannan ta shiga inda aka saka na'uran shakar numfashi, ta zare wasu wayoyyin, sannan tazo ta cire roban kan hancina.
   Ta juya abunta tafita..

        ****
     "NaJibullah mi ya haɗaka da ɗan uwanka? Yace min duk zuwan da yake baka kula shi laifin mi yayi maka da zafi haka, da zaka kullace shi." Inji Yaddiko.
          "Yanzun Yaddiko tsakani da Allah Maheer yasan matarshi ce Aisha sai ya barni nayita shirme, anyi min adalci kuwa? Yaushe akayi abin bani da masaniyya, idan ban kullace shi ba mi zanyi mishi, ai wannan munafuntatta yayi bayan yasan cewa matarshi ce ya barni nayita shiririta."

         "Yo Dama akan wannan maganar kake hauka, kaci kwala Ubanka, nace." ta ware mishi yatsunta,  irin ranta ya gama ɓacin nan.
     "Kuma nice na bawa Maheer auren Yar Yaddiko dan nasan shine kawai da Uwarsa bazasu k'ita ba, da kake shirmenka a nan ko an faɗa maka bansan Uwarka tayi maka iya da Yar Yaddiko bane, wallahi idan na kuma jin kace wani abu akan Yar Yaddiko zan saɓawa Ubanka. Lokacin da Na ɗauketa, nacewa Iyayenku tsakanin kaida Maheer na sama muku mata, buɗar bakin Uwarka tace  ko mata sun kare a duniya ɗanta bazai taɓa son Yar tsintuwa ba,, dataga aurenka da Yar tsintuwa gwara taga mutuwarka, kaje tambayeta.
       Mahaifiyar maheer kuwa bata bar inda akayi maganar ba, tace Yaddiko na amince Maheer ya auri Aisha, da ɗa da dukiya ba'a wulakantawa. Kaje ka tambayi Salmah anyi haka ko ba'ayi ba, tasan halina sarai, zan iya zuwa bar bauchin ayi maganar a gabanta."

  Tana gama faɗar haka ta riko hannun Ya Maheer taja suka fita daga ɗakin, suka nufi bangaren da nake.
             Suna shigowa ɗakina suka same ni, ina jan numfashi kirjina nasama yana sauka yana hawa.
           Da sauri ya mayar min da roban hancin,  ya ɗaga kanshi yana kallon nauran baya aiki, sake ni yayi yaje ya kunna wayoyin sannan  ya maida min, komi.
  Shakar kamshin ɗakin yayi ya fita da sauri.

         .......Tana kwance rike da waya sai dariya take, tace.
"Hajiya ai ina ganin yanzun kam ta mutu, dan na zare abinda yake taimaka mata gurin shakar numfashi, wallahi Yaddiko na bani mamaki ta ware mu kamar ba jikokkinta najini ba, oho ni dai na kashe banza..."

      Bata idda maganar ba taji an rufeta da duka, ta ko ina kamar Allah ya aikoshi, tun yanayi da belt har ya wurga ya saka hannunshi ya cigaba da dukanta......
Kuyi hkr ba lallai bane ku cigaba da samun updater dan gaskiya bana jin daɗi....😳

YAR GIDAN YADDIKO🧕Où les histoires vivent. Découvrez maintenant