28

5.5K 521 53
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

   _Yanzun kowa gani yake zan kahe jikan Yaddiko bayan zunzurutun ɗibar albarkan da akewa Yar Yaddiko_
       No one escape for love......

Page.28
        Dake hannunshi nayi cikin kuka nace.
"Ka tashi mana, don Allah"
   Wani kukan ne ya kwance min na kifa kaina a kirjinshi ina shashekar, karan na'uran da aka samishi yasa Ya Najib shigowa. Kauda kanshi yayi ya cigaba da aikin da yake, ga Abba da yake kallonmu.
                  Likitotine suka shigo, har su uku, suka rufa mishi.
      "Kinga fita ki bamu guri, zamuyi aiki." Inji Ya Najib,
     Kallonshi nayi yaki yarda mu haɗa ido, gabanshi naje ina leka fuskar shi nace.
"Ya Najib! Ka tashe shi, don Allah kace mishi ya rabu dani Kaji,"
                 Lumshe idanunshi yayi cikin tsananin damuwa, a hankali ya buɗe idanunshi ya kalle ni.
"Ki fita naceeeee"
    Ya daka min tsawa,
        "Wai miye laifina? Mi ye nayi muku da zafi ? mi yasa kuka tsanani? Ku wasu irin mutane ne masu mabanbantar halaya, na k'i iyayena sabida ku na dawo kuna tozartani. Zan fita a rayuwarku zan fita kuma zan tafi bazaku sake ganina ba, balle ku wulakantani ina da iyaye da dangin da suƙe sona na k'isu shine da nazo kuka saka min a gaban iyayena."
          Gaban Ya Maheer naje, na dafa hannunshi cikin sanyin murya nace.
"Pls wake up, ina jiran sakonka."
        Ina gama faɗar haka na fito daga ɗ'akin kifa kaina nayi jikin kofar na sake rushewa da kuka. Mai cin rai, a hankali nake takawa har na iso inda Mamie suke nace.
"Mamie muje gida."
        Kallon Mamah tayi wacce kanta yake sunkuye, tace.
"Hajiya kuyi hakuri, munso mu bar muku ita anan amma ba hali sabida wasu daga cikinku basu maraba da ita, mungode da rike mana ita da kukayi musaman Kaka da Maheer, zanyi iya ƙoƙarina na daidaita komi, Allah ya bashi lafiya mungode."
             Jan hannuna Mamie tayi, na juya tare da kallon kofar ɗakin  wasu sababbin kwalla na zuba a idanuna, zame hannuna nayi cikn nata na juya da sauri, na koma ɗakin. Iyakata bakin kofar na kasa shiga zamewa nayi na durkusa a gurin.
         Juyawa Mamie tayi ranta a ɓace, Dadda ya rikota, yace.
"Nafisatu don Allah ki barta son mijinta taƙe, bazamu tafi da ita ba zata zauna a fada. Idan mukayi nesa da ita, zata iya shiga makamanciyar matsalarshi. Shima abinda ya cutar dashi kenan ɓoye soyayyarshi, ita kuma tsabar Yarinta yasa bata san miye take so ba, Khadija tana son mijinta fiye da komi, dan ya koya mata sonshi a ɓoye a zahiri kuma ya cusa mata kiyayyarshi."

      .......Dafa ni Mamah tayi cikin raunaninyar murya tace.
"Tashi kije, karki damu rayuwa da mutuwa duk na Allah ne, insha Allah idan ya tashi zai miki abinda kike bukata, kinji."
    Kallonta nayi zanyi magana ta rufe min bakin, tace.
"In uwace kuma adalice bazanwa hafsa dole ba, haka kema bazan taɓa miki dole ba. Sai dai kisani MAHEER Ya bada rayuwanshi dan ke, ya tsaya maciji yasare shi dan keee, Yaje Miki a matsayin Nadeem Shira, Sannan yabar karatunshi na masters sabida kee, Ya hakura da aikinshi da karatunshi na Phd sabida keee, har yau Aljanunki suna bibiyar Rayuwar shi sabida Keee, shi ɗaya yake iya fahimtarki. Koda ya koreki a germany bai kawo zaki ɓata ba, dan zai iya ɓatar da kanshi dan kiyi farin ciki, MAHEER ya fara sonki daga ranar da yaganki a tsumar goyon Yaddiko,  yace min.
"Mamah! Nikam nasami matata."
            A lokacin mun zata wasa yake, sai da yakai duk hutu sai yaje ya dubaki a Gumau, Maheer ya amshi aurenki kina da shekaru goma  lokacin da Faruq ya fara niman lalataki, ya roka aka ɗaura mishi auranki. Dan kar wani ya shigo rayuwarki, shi ɗaya yake kangeki daga duk wani ɗa namiji, dama can da maganar aurenshi dake inda Yaddiko ta bashi ke, koda aka zo za'a bashi sailuba k'in amincewa yayi, sabida shi kece tsarinshi, Maheer yana miki so ɗaya tak, duk namijin da ya kuskura ya tun kareki da maganar so, toh kai tsaye yake mashi iyaka dake, Aisha Khadija, bansan wani suna zan kira ki dashi ba. Amma zan faɗa miki wani abu guda, a ranar da sailuba ta wurgoki  zama yayi yana kuka wiwi, sabida gani yake bazaki mike ba. Ko a haka nabarki zaki iya tafiya."
       "Mamah mi yasa aka ɓoye min?"
            Ji nayi an ja hannuna, Mamie ce, ina kallon Mamah tana son bani amsa amma Mamie ta janye ni. Dole muka bar asibitin kwallan idanuna sun kafe, bana jin daɗin komi a duniya ji nake ina ma zan iya ciro zuciyata da na yasarta na huta da zafin da take min, juyawa nayi na kalli Mamie nace.
"Am sorry sweet Mother"
       Murmushi tayi nima na maida mata, na koma na jingina kaina, har muka isa fadar bauchi idanuna a rufe cikin gida muka nufa, inda na zube akan kujera dafe da kirjina, wanda yake barazanar fitowa waje. Ruwa Mamie ta mika min nasha, tare da sauke a jiyar zuciya. Na ɗago idanuna na kalleta sannan na lumshesu na gyara kwanciyata. Barci ne yayi gaba dani ina yi ina sauke ajiyar zuciya.
        ***
   Allah cikin ikonshi Ya Maheer ya farka amma sun mashi alluran barci, fitowa sukayi suna taya juna murna.
          Nan Ya Najib ya labarta musu halin da ake ciki, Alhamdulillah Mamah tayi, a hankali Abbanshi yake faɗa mishi irin tabargazar da Ummanshi tayi, ba ita ɗ'aya har da sauran Yan team ɗinsu.
       Shiru yayi ya wucce ofishinsa ya rufe kofar, zama yayi ya dafe kirjin shi. Jini ne ya fara ɗigowa daga hancinsa. Bud'e drower ɗin yayi ya ciro kwalbar, maganinshi ya zazzaga yasha da ruwan dake saman frej.
    Komawa yayi ya jingina da kujeranshi yana jin zafin da zuciyarshi take,a hankali ya buɗe wata yar locker ya zaro. Wani frame hotona ne, sanye da unifoam ɗin mkrnta ina dariya.
     "Sonki shine Ajalina"
  Ya furta a hankali hawaye na bin fuskarshi.

                 *****
    "Kunga nifa karku faɗa la'anta musu Y'a dan zan bi duk inda zan bi na kaso aurensu da Maheer In yaso Najib Ya aureta. Ni sai yanzun ma nake ganin kuskurena na hanashi mu'amala da ita, da yanzun nice uwar mijin Y'ar sarkin borno, kuma kinsan ba karamin dukiya iyayenta suka tara ba, zanje har can na basu hakuri mu kulla zumunci sannan na shigar da Najib, dan..."
    "Amma kee kam Salma dakikiya ce Yar kanwar tawa zan bari kiwa kishiya, toh bari kiji wallahi wancar baƙar ƙ'addara bazata taɓa shigowa cikin wannan ahalin ba." inji Hajiya Sadik'a.
       "Ai kuwa zan sakashi ya saketa, tunda ɗ'ana ne ba wata shegiya ta haifa min ba,, dani kuke zance  kufita min a gida gayyan tsiya gayyan Arna a idi, matsiyatan banza matsiyata wofi, idan kika min hanyar da na rasa wannan damar sai na bankaɗa sirrinki kowa yasani."
      "Kee Salma ba tsoronki nake ji ba, wallahi bazan tab'a barinki ki aurawa Najib Aisha ba, dan nima wa ɗ'ana zan nimawa muguwa kwaɗayayyiya."
       "Ayirrrrrrrrr nanaye! Kan uban can duk wanda ya fasa yarena kanshi wallahi ko zanyi yawo tsirara sai Najib ya auri Yar Yaddiko dani kuke zance, munafukai masu bin malamai da bokaye"

     Hmm haka manyan mata kawayen juna sukayita kwashewa juna albarka tare da gorace gorace......
           Wallahi na gaji sosai......

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now