34

5.5K 596 39
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

*Ku fada min gaskiya wani irin addu'a kuka min ne Yau da nayi muku typing haka😂.*
_________________________________

'''Kowani mutum A duniya yana da hujjarshi nayi dai dai ko ba daidai ba. Dan haka sakayyar Allah itace sama da komi a duniya'''

_______________________________

Page.34

Karfe hud'u na yamma yayi mashi a kofar fadan shehun barno, ajiyar zuciya ya sauke yayi da yafito tare da niman izinin shiga. Amma firr fadawan suka hanashi asalima da ya fad'a musu yana sonsu had'a shi da sarki nan ma suka k'i abu kamar wasa sai ga Ya Maheer har magarib yana fama dasu.

Dole ya tafi hotel ya kwana da safe da yazo ma haka suka hanashi shiga karewa suka ce zasu harbe shi, ko su mashi duka.
Amma bai bar gurin ba, asalima sai bak'ar nace musu da yayi wanda yasa su, fita harkanshi.
A hankali kwanaki suka shiga tafiya har lokacin basu barshi ya shiga ba asalima ko inda suke basa yarda yaje.
Ranar da ya cika sati d'aya. Ranar ana wani bikin Y'ar gwonar barno, kuma an wakilta Mamie ce. Zata kai yarinyar gidan mijinta a Damaturu.
Da misalin karfe uku bayan sallar jumma'a aka fito da ita zasu tafi gidan gwona a d'auki amarya.
Ya Maheer yasha gaban motar da zai mata rakiya, kuma abin mamaki sakamakon cinkoso ya hanashi had'uwa da Dadda.
Fitowa dogarawa suka fito, cikin zafi dama, fushe suke da fushin wani. Tuni suka nemi rufeshi da duka, ita kuma ganin sun tsaya yasata tambayar lafiya shine driventa ya leko ya duba. Fitowa yayi daga motar yaje yaji ba'asi.
Komawa yayi, ya d'ukar da kai yace.
"Ranki shi daɗe! Wani mutum ne daga bauchi wai yazo gurin matarshi Aisha, tana cikin masarautar yau sat..."
"Kace musu, su kyaleshi kuma ka fad'awa Sarkin gida abashi masauki zan nime shi." cikin isa da iko tayi maganar.
Da sauri Ya koma ya fad'a musu sannan aka wucce da Ya Maheer binshi tayi da ido tana jinjina tsabar rashin kunyar da yasashi kwaso jiki.

Haka suka tadda motar suka bar gurin, tana nazarin matakin da zata ɗ'auka.
****
Bayan tafiyarshi da Kwana d'aya Allah ya sauki Binta lafiya inda tasami Y'arta mace, mai tsananin kama da Ya Najib. Wani irin soyayyar da sukewa Najib ne ya dawo kan yarinyar. Ita kanta Umma kamar ta cinye yarinyar dan so dan gani take kamar Najib ɗinta ne ya dawo mata.

Mamah takirashi ta fad'a mishi yace ayi komi. Sai ya dawo , aikuwa Mamah ta taka rawan a gani, dan ita Umma Yarinyar take bawa lokaci yayinda Mamah ta d'auki Binta zuwa gurinta sam Yaddiko taki saka musu hannu tace.
"duk abinda zakayi kuyi, bani tab'a kowacce Y'a sai Shatuwana."
Tsakanin Binta da Baby wacce Abba yayi mata Hud'uba da Nana Aisha, sai shan nono anki barinta ta rabu da Uwarta.
Tun abin bai damun Binta da Mamah har mamah tasami Umma da magana, sosai suƙayi fad'a har da gori akawa Mamah ita kuma tace.
"Ki rike, Y'ar karki kuskura naga kafarki a kofar part d'ina indan kuwa haka ya faru zan baki Mamaki Salmah, ki rike jakarki ni zan rike Binta ba iya binta ba ni Safiya zan shayar dake Mamaki a rayuwa Allah ya bamu nisan kwana."

Tana gama fad'ar haka ta koma cikin gidanta ta cewa binta.
"Kiyi Hakuri, alamarin Salmah akwai takaici ki bar mata Y'ar muga yanda zatayi da ita, kiyi hakuri zaki ci ribarta indai ina raye bazan tab'a barinki kiyi maraici ba, alfarma d'aya zan roke ki ko zaki iya ban sani ba."

Mamah ta tsare ta da ido, sunkuyar da kai Binta tayi cikin zubda kwalla, tace.
"Mamah! Babu abinda zaki rok'eni wanda bazan iya ba Mamah, kin maye min gurbin Mahaifiyata."
Shiru mamah tayi tana kallon Binta, jikinta yayi sanyi riko hannun Binta tayi tace.
"Fateemah! Bani da wani zab'in da ya wucce nace ki Auri..."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now