24

5K 448 39
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

           *_Wannan shafin nakine Fateema Misa Hussein dan ko ta ina kina biyana kuma kina tare dani naji daɗin comments ɗinki, ga kyautar ba Yawa Nagode sosai_*

          _Toh Allah yayi aure da mara kw'abo gashi kun samu da rana ba lallai bane ku samu da dare kuma ina ganin a 25 zan iya dakatawa sabida toh basai nayi dogon Ingilise ba kun fahimta.....Allah ya jikan Iyayenmu mata Ya kuma bawa iyayenmu maza lafiya da nisan kwana_
Page.24
        "Domin nan gaba idan aka zo bada sarauta, ita yarinyar da mahaifinta zasu bashi gudummawar ɗaura shi kabi a hankali dan wallahi tass mahaifinka zai iya sawa a koreka a cikin wannan masarautar."
     Tana gama fad'ar haka ta juya abinta tabarshi a gurin.
        .......Ina nasan mike faru ni dai tunda nasami wasik'ar Nanah Asiyah sai jikina yayi sanyi, amma ba akan Bamai ba.
      
         Gimbiya Amrah taso shiga jikina naki amincewa sakamakon nausheni da Nana take ta hanyar hantara da nuna min kiyayyarta itama, karshe ta janye Fatima da Rafi'a daga gare ni, kuma bata fasa nuna min iyakata ba.

      Watana biyu wata ranar ina barci Allah ya taimaka na rufe kofar ɗakina, sai kawai naji ana ihu da kuwa. Ashe wani ne ya shigo shashina tsoro ya kamani, ban fita ba sai washi gari.
     Inda nasami labarin an yanka wasu dogaran da suke tsaron kofata ta waje,, ɗaya ya rasu ɗaya nacan magashiya.
         Tashin hankali da aka shiga a masarautar babu iyaka, inda wasu suƙe jinjina alamarin da cewa auro kyakyawa irina zai haifar musu da masifa a cikin alummarsu tunda gashi an fara bibiyata.
                 Mai martaba bai ce komi ba, karshe gimbiya Amrah tace na koma ɓangareta da zama Nana Asiya tace.
"Babu inda zata ta zauna dole a ninka, tsaro a shashinta, kuma dole a turawa mijinta aika yazo ya ɗauketa, tunda abin ya zama haka ko shashina bana son ganin kafarta, ta xauna a shashinta daɓ nan gaba ita uwar mutanen borno."
   Tana gama fad'ar haka tafita daga palon.
         Kamar yanda Nana asiya tace haka kuwa akayi amma bai samu zuwa ba sai da ya cika wata huɗu. Ya dawo da Uwargidanshi, Amina, akan zai tafi da Mariya.
              
      Ranar da ya dawo cikin dare ne, kuma ana ruwan sama shashin Amina yakaita, ya koma motar da aka ɗaukoshi, da niyyar ajiye wasu abu, sai ya hango inuwar mutum ya dira ta katangana.
     Ajiyewa yayi ya nufi shashina yana zuwa masu tsaron suka mike, haskashi sukayi  nan suka tabbatar shine, buɗe mishi kofar suƙayi.
          ..... Wani abin mamaki, na tashi yin wanka sabida ɗaukewar hailata, ashe nabar kofar ɗakina abuɗe da zan shiga ban ɗaki ne nayi hikimar saka key.
          Ina cikin wanka naji ana bubuga kofar bayin, can kuma naji karan fashewar abu.
           Kamar ana dambe kin fitowa nayi har aka gama abin can, naji muryanshi yana magana na buɗe kofar ɗakin kin buɗewa nayi dan ban yarda shine ba.
      Dukar kofar yayi wanda yaja kofar ta buɗen dole, ina sunkuye na cusa kaina a tsakanin cinyana, dan ko kaya babu a jikina.
      Juyawa yayi yafita ganin audugar mata makale a jikin pant ɗina.
              Bayi matane suka kawo min kayana nasaka, sannan suka min rakiya har shashinsa, suka barni a falon zaune.
           Har barci ya fara ɗibana ya buga kujeran da nake kai, nuna min hanyar daki yayi, naki tashi yayi juyin duniyar nan fir naki tashi, dole ya kyaleni yayi tafiyarshi zuwa ɗaki.
  A gurin na kwana washi gari yana dawowa masalaci ya sameni a kwance gurin, ina ganinshi na mike zan fita.
     "Ke a gidanku ba'a koya miki gaida manyanki bane."
     "Eh ba'a koya min, sabida mu gidanmu ba'a bin matan aure cikin dare."
      Ashe baiyi nisa ba, dawo dani yayi zai kara taɓani na ɗago a masifance nace.
"Kana taɓani nice ajalinka."
     Jinjina kai yayi ya kyale ni nayi tafiyata, tunda ya dawo. Aka maida ni shashinsa takaici kamar ya kashe ni.
      Ashe maganar da nayi na nice zan kashe shi, har ya isa kunnen Gimbiya Amrah. Abinci tasa akayi a shashina tabada guba aka saka mishi, sannan aka kuma kai gubar aka ɓoye a cikn ɗakina.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now