19

5.3K 459 24
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

      *_Na marasa ta inda zan fara mika mika muku sakon godiyata ban san da wata kalma zanyi amfani da ita ba, Yar Mutan bauchin Yakubu tana muku fatan Alkhairi da godiya Allah ya albarka Rayuwarku da farin ciki Nagode😍😘_*

Page.19
        
        "A'a Bamai k'adr bace son zuciya ce, sabida son mulki suka rabani da farin cikina, mi yasa."
            Numfashinta ne ya shiga yin sama, alamar asthma gareta.
     Inhelar dake kusadashi ya saka mata a bakinta ya matsa, take numfashin ya tsaya. Tsuke fuskar shi yayi tare da janyeta a jikinshi ya cigaba da kallon tashar CNN.
     Kwanciya tayi a jikinshi cikin kuka tare rigarshi.
    "My King! Kayi hakuri bazan kuma ba, amma kasan ni Uwa ce! Kuma dole zuciyata ta rayu da soyayyar Khadija. My King idan ban so khadija ba wa zanso? My king am sorry bazan kuma ba, punish me ta kowani hanya amma banda ta wannan hanyar dan zuciyata tarwatsewa zatayi."
      Juyawa yayi ya zubawa fuskarta ido, sannan ya sake murmushi tare da murza yatsun hanunta yana kallon cikin kwayar idanunta. A hankali ta shiga kiciniyar kwacce hannunta, cikin murmushin dole tare wani shagwaɓa tace.
"Hmmm! Kyale ni Yallaɓa, ka barni na sauke wannan nauyin dake tare dani."
             "Ji yanda kike abu kamar yar sha bakwai, Nafi saida muka shekara goma  sha biyu kafin Allah ya bamu Khadija, itama Allah ya amsheta. Kiyi hakuri ki haifa mana wannan katon cikin naki, wanda suka ja akewa Dadda rowa, wani ni'ima ce da Ubangiji yakewa bayinsa masu hakuri da tawwakali, da Yard.."
     "K'adr ba ai ba yau na haddace su ba My King, Ya wucce."
       Gyara mata kwanciya yayi a jikinshi, cike da tausayinta da kaunarta mara iyaka. Shekarun da aka bashi aurenta tana karama sosai, dan bata wucce sha shida ba. Kamar ba jinin sarauta ba ta taso cike da rayuwar mutanen da basu damu da alakar masarauta. Murmushi yayi idan ya tuna yanda suka sha fama da ita dan sam bata kaunar shi da akayi auren, dukda yasan ambashi aurenta yana da shekaru kusan ashirin da takwasa kuma lokacin....

       Ajiyar zuciya ya sauke tare da shafa kanta, "Bansan farin ciki ba sai akanki Nafisatu." a kalla Yallaɓai Bamai zai kai kimamin shekaru, hamsin da tara zuwa sittin. Amma tsabar hutu da jin daɗi sai ka ɗauka bai wucce arba'in da yan kai ba. Haka ma matarshi wacce kallo ɗaya zaka mata banda cikin jikinta bai wucce ka wurgaka ajin ashirin da biyar ba,

              Shafa fuskarta yayi firgi ta mike daga jikinshi tana tura mishi baki, cikin mita tace.
"My King! Zan tafi shashina na wuta."
        Jan hancinta yayi cikin tsare gida, yace.
"Ki duba min, ɗakina sai ki wucce  shashinki tunda bani na gayyato ki ba."
          Rau rau tayi da idanu kamar zata fasa kuka tace.
"Allah ya taimaki, sarkin gobe likita ya hana fa.."
   Shafa fuskarshi yaƴi wanda yake ɗauke da murmushi ya kalleta, tare da tuna wani abu mai muhimmanci a tare da ita, wanda shine mafarin farin cikinsa da ita wanda yarintar irintata tasashi yaji babu farin cikin da yafi kasancewa da ita.
         "My Queen! Jeki gyara min ɗakina nace bana son yawan korafi."
     Mutsika idanunta ta shiga yi, alamar zata mishi kuka dariya taso bashi yace.
"Da yanzun da Nana a gidan nan haka zaki cigaba da shagwaɓa dan nasan matuƙar tana nan dole ki ajiye wannan rigimar taki my dear tausayawa ɗan tsohon...."

    Mik'ewa tayi dakyar ta nufi ɗakin, babu komi fa. Ban ɗaki tashi ga ta haɗa masa ruwan wanka  tare da turaruƙar wanka sannan tafito. Haɗuwa sukayi a ɗakin,.  Cikin dabara ya lallaɓata suƙa shige ban ɗakin, daga nan koda suka fito. Sai da yayi abinda take gudu, yabarta da shakar inhelarta.
             *****
   Asibitin da Ya Maheer bai koma ba kenan, ya shiga nimana ko zai dace.
      Duk yanda yaso kar Yaddiko ta shiga tashin hankali sai da tashiga lokaci guda, jininta ya hau.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Onde histórias criam vida. Descubra agora