18

5K 452 47
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*
      

           Hmm bani da ta cewa😂

Page.18
     A razane na kalle shi, tare da kai hannuna zan rike shi, tsawa ya daka min wanda yasani yin baya a tsorace, ina kallonshi.
    "Muguwa mai mugun hali, kije can mai kyan ɗan maciji kawai, jin kike idan kika yi min laifi bazan iya hukuntaki ba ko. Jeki bana son ganinki."

                 "Ba sai kayi min koran kare ba, zan tafi kuma na tafi kenan har abada, kuje da sonkanku da son zuciyarku nima Allah zai dawo min da iyayena, abu ɗaya zan faɗa maka idan kaje gurin Yaddiko kace mata ta yafe min, sannan Ina kaunarta kamar yanda nake kaunar iyayena."

   Ina gama faɗar haka na juya tare da barin gurin, lokaci guda naji kwallar idanuna sun kafe, zuciyata tayi matukar sanyi da ɗaukar na dama, mara amfani.
     Tafiya nake bansan inda nake jefa kafana ba.

          ****
     Komawa ciki yaƴi suka cigaba da aikin tsada jinin cikin ikon Allah jinin ya tsaya cikin ma ya tsaya sai dai babu kuzari a tare da cikin, bincike suke ko wani abu ya sami babyn amma babu komi, sai kwanciyar babyn ne ya karkata.
          Dole suka hakura dan taɓa cikin ma hatsarine.

                 Fito da ita akayi bayan an jona mata karin jini ta hannun dama, karin ruwa ta hannun hagu.
                  Barinta yayi ya dawo gida, ya sami Yaddiko tana kuka sosai zama yayi kusada ita yace.
"Yaddiko!"
     "Hmm Mahar nice na goya Aishatu, tun tana tsakanin kwana arba'in zuwa hamsin. Ban taɓa dukarta ba, yau son kai yasani na daketa na zageta bayan an cutar da ita, naji kunyar abinda nayi mata dan har goranta mata nayi ina zan kai tarin alhakin dake kaina, mahar lokacin da na tsinci Aisha kaga awarwaron da nasamu da ɗan kunnenta a jikinta, mahar har yanzun alkyabar da nasamu tana naɗe da ita yana nan, abu ɗaya da nake addane dashi shine wannan takardan."

           Mika mishi tarkacen tayi  jikinshi na rawa ya warware takardan, wanda yake ɗauke....

               ****
   Duhune ya fara rabawa, gashi bansan inda zan tusa kaina ba, koda na koma gidan korata zasuyi dan haka na cigaba da bin titi ina tafiya, jikina ne ya kuma sanyi lokacin da naga dare yayi kafa ya fara ɗaukewa.
             Kame jikina nayi da hannuna na cigaba da tafiya, har na shigo ta cikin mutane, wani mall na gani na tsallaka ta gurin, niman ruwa a gefen gurin nayi sallah.
           Ina tsallakawa titin saura kiris wata mota kiran Nissan tayi sama dani,   amna suka taka birki.
              Tsallawa nayi da sauri, tsoro ya hanani ma tsayawq kawai nacigaba da tafiya dan gani nake zasu saka a kamani.
            Haka na cigaba da tafiya ina ratsa unguwanin, har na gaji na sami wani ɗan karamin lungu na zauna, tare da fashewa da kuka sosai nayi, bansan lokacin da na ɗauka  a gurin ba sai ji nayi ance.
"Hey."
       D'ago kaina nayi a tsorace, aikuwa  matasane guda huɗ'u kamkame hijab ɗina nayi na mike,  kafin su sami ikon kamani tuni na arta a guje.

        Rufa min sukayi, ina kuka ina ambaton Allah, nake gudun ceton raina,dan sannan matukar suka kamani nakaɗe arbuzuna. Suna dab da kamani nafita titin, saura kaɗan mota tayi sama dani, drivn ya taka burki. Hantsilawa gefe naƴi zan mike mai jan motar yayi maza yafito tare da cafke ni.
         "Ke daga Naija kike."
     Jin yayi min hausa yasani cewa.
"Eh...eh"
    Matasan nan basu hakura ba suka yo kanmu, bayanshi na shiga na ɓoya.
     Kallonsu yayi sannan ya saka hannunshi a aljuhunshi ya fidda bindiga, take suka juya.
     Fitowa Yan mata suƙayi sa'anina, ɗaya tace.
"Ya Annoor! Kazo muje gida kasan Aunty Nafi tana can tana jiranmu."
    Juyawa yayi cikin jin kai ya zabga mata harara, sannan ya kalle ni.
     "Ko zaki min kwatancen gidanku na ajiyeki."
       Ya faɗa min, cikin wani sanyi murya mai daɗi,
     Sunkuyar da kaina nayi cikin kuka da son ɓoye abinda ya koroni nace.
"Na faɗa hannun Yan safarane."
            Cikin alamun tausayawa da kuma rashin son tsawaita magana yace.
"Ok! Kinsan inda danginki suke ne a naija? Shiga mota muje."
      Shiga bayan motar nayi, ya rufe motar, cikin kuka nace.
"Ni marainiya ce, Iyayena sun rasu a hatsarin mota."
         Shiru motan yayi yan mata guda biyun da suƙe baya suka wani ɓata rai, tare da matsawa daga inda nake zaune, dan kar na shafa musu, talauci.

                      Bai sake tambayana ba, nima shiru naƴi ina share kwallana.
     ........
      *_Assalamun Alaikum_*
    _Da fatan alkhairi ga wanda ya tsinci wannan yarinyar ya riketa har takai lokacin da zata mallaki hankalinkanta, don Allah Yasadata ga Masarautar barno, an sani na saceta ne, sabida wasu dalilai Allah yasa ta faɗa hannu na gari, idan za'a maidata a nemi  Abubakar Elkanami Bamai_

         A firgice ya juya ga Yaddiko bakinshi na rawa, yace.
"Yaddiko! kinsan gidan da Aishatunki tafito kuwa? Tana ina yanzun?."

         "Ina zan sani bayan kuna fita tabi bayanku," ta faɗa mishi a raunane.
          "Innalillahi! Kardai bata dawo gidan nan ba, na shiga uku Yarmutane ta ɓata Yaddiko, tabini Asibiti na koreta, naxata gida ta dawo, ashe da nace karta dawo gidana ashe bata dawo ba na shiga uku ni Muh'd ina zan fara."
   Dafe kanshi yayi.....
            *****
Wani tangamemmiyar gida naga mun nufa, wanda aka buɗe labcecciyar get ɗinshi, kusan mutane ukune suƙa buɗe get ɗin, dogaraine majiya karfi, masu sanye da kaya ja kore sai uban rawanin da suka naɗe kansu dashi.
     Da sauri  wani daga cikin dogaran yazo ya buɗe motar ta inda drven yake sannan ya koma baya ya buɗe kofar baya.
      A nitse muka fito, tare da kallon gidan yanda aka kawata shi, faɗarshi kaman ɓata bakine. Faɗawa duniyar tunani nayi ina kallon gidan, sai da aka kaɗa min key na dawo kallon wanda ya taimake ni nayi tare da sunkuyar da kaina.
         Zubewa dogarin Yayi cikin fadanci yace.
"Allah Ya taimaki Yarima Annoor, kayan suna cikin gida an kaisu."
        D'aga mishi hannu yayi sannan ya min nuni da cikin gidan, jikina ba kwari nabi bayanshi tare da zamar da Hijab ɗina, ya ɗan rufe min fuskana.
    Da sallama muka shiga cikin falon, nasamu yan matan nan sun saka wata babbar mata wacce bazata wucce arba'in da biyar zuwa da baƙwai ba, tasa abinda aka kawo mata a gaba tana taunawa a hankali, gefe guda kuwa korafin Yayansu suka kawo mata, ga bayi mata a gefen ta suna matsa mata kafarta wanda sukayi luntsuma luntsuma, sakamakon tsohon cikin da take fama dashi.
      Fara ce sosai wacce kana ganinta kasan ta haɗa iri da Fulani.
           "Allah ya taimaki Yarima barka da dawowa." Inji ɗaya daga cikin matan da suke kaikawo a falon, wanda alamu ya nuna kusan amintacciyane a cikinsu.
         D'ago dara daran idanunta matar tayi ta kalleni,  yanda na raɓe can jikin bango. Ina kallonsu, murmushi tayi sannan ta juya ta kalleshi cikin murya mai nuna alamun kayi laifi.
  "Prince! ka kyauta Khairat da Mubina sun kawo korafin wai da suka bika baka saya musu komi ba sannan."
       "Aunty Nafi yaushe zaki daina ɗaukar maganar yaran can." yanda yayi maganar ƙaɗai zai tabbatar maka dacewa a gajiye yake.
           Juyawa yayi ya kalleni sannan ya yafito ni, zuwa nayi kusadashi.
"Aunty gata gobe zan miki bayani."
     Yanda yayi magnar sai ka rantse wani aikin karfi yake nan kuwa tsabar jin mulkine zalla.
         Miƙewa yaƴi yabar falon, murmushi tayi indai Annoor ne tasaba da halinshi.
     Maida kanta tayi gareni tana kallon yanda nake, nutse guri guda, ina jin tace.
"Jakadiya, a kaita ɗakin kusada na Yaran nan, da abinci."
                  Jikin matar na rawa, tace.
"Tashi Yar nan. Sannan ki mika godiya ga Fulani Nafisatu Yar sarki jikan sarki, Matar sarkin Barno na gobe."
        Muryana narawa nace.
"Nagode!!!"
   Kanta a sunkuye yake tana juya zumar dake gabanta, da sauri ta ɗago shi, tana bina da ido.
                   Muna barin falon itama ta mike, tabi wani step da ya kaita wa shashi daban, wanda yafi shashin farko a huɗuwa da tsaruwa,
     A hankali ta tako har inda yake zaune ta zauna tare da kwanciya a jikinshi, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fashe da kuka tare da cewa.
"Na tsani mulki da abinda yake cikinta, Bamai sun rabani da farin cikina, shekaru goma sha biyar zuwa sha shida, Bam....."
       Haɗe bakinsu yayi tare da kai hannunshi kan cikinta yana shafawa, a hankali har sai da yaga ta haɗiye kukan da take ya ɗago kanta.
        "Wato Nafi bazaki girma bane, ki yarda da Qadr mai kyau ko mara kyau......"

             _Chaiii Idan na haifi baby mai karamin hanci zaku gayawa Baban Waleed aika akain da kuke sani na muku typing dole😁_

  Yanzun aka fara.....

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now