chapter 1

2.2K 96 13
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

    🌹 HAR ABADA 🌹
           (Forever)

     LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@seemahwrites

     BY
       UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

My first novel
   01🍎

Wani narkeken parlour na shiga da siririyar sallama ta Wanda ba lallai bane wada suke parlorn suji ba.

Wata dattijuwar mata na hango xaune akan wata makekiyar kujera fuskar ta a murtuke, tare da wasu yan matasa biyu mace da namiji dake xaune a kasa suna facing din ta macen ba zata wuce shekaru 19 ba namijin Kuma xe kai 27.

Fada matan take surfawa cikin yanayin ta na masu sanyin hali Amma a kaushashe take magana.

" I'm really disappointed in you Abdallah,
ko a mafarki ban taba zaton xaka iya yanke irin wannan danyen hukuncin ba!

Nayi zaton kayi girman da ya kamata ace kayi hankali? You are not a teenager anymore! Haba kaikuwa
Don wani xargi da baka tabbatar ba xaka saki matar ka? Baka da hankali ne?

Namijin ne ya qaraso kusa da ita ya kama kafar ta cikin xubar qollah
"Umminah Dan Allah kiyi haƙuri bani so na xama silar bacin ran ki, Nasan nayi kuskure babba Amman Dan Allah ki gafarce ni"

Yarinyan dai hawaye kawai take xubarwa cikin ƙunan xuciya, a fakaice Ummin ta kalleta sannan ta maida duban ta kan Abdallah

"yanzu kana ganin kayiwa Safiyya adalci?iye?
Yarinyan da ta tsaya ma soyayyar ka dukda cutarda kake fama da ita da ba kowane xai iya daukaba kasan wani irin baƙin ciki mahaifiyar ta zata ji? Idan da irin halin ka mahaifin ka yake dashi da baka tashi ka same mu a tare ba"

sai Kuma ta fashe da siririn kuka sabod tuna baya mai cike da ƙunci fargaba dakuma jarabawa data fuskan ta a gidan auren ta.

Sautin kuka ne kawai yake tashi a parlorn babu mae rarrashin wani hakan ne ya bani Daman jin hayaniyan da ke fitowa a wani daki, ƙara gaba nayi na kutsu cikin dakin gefen parlorn shigana yayi dai_dai da saukan wasu wawayen tagwayen maruka da wata dattijuwar mata ta sauqema wa wata budurwa Wanda xata kai kimanin shekaru 17.
"u are very very stupid Fannah!! nayi nadaman barin ki a hannun kakan ki kwata_kwata Bata baki tarbiyya ba, Tirr da irin halinki"

Mijin Fannah dake durkushe da azama ya miqe ganin lafiyayyun marukan da Momy ta sauke mata a kunci,
dana ƙare masa kallo naga Shima badai wuce shekaru 27ɗin ba. Ƙarasowa yayi gaban Momy dake tsaye yana fadin
"Dan Allah Momy kiyi hakuri"
da hannu ta dakatar dashi daga kusanto ta da yake yi tana fadin

"soko kawai. Kaima me laifi ne da baka kashemin ita ba,
Idan ba shashanci ba a kanki aka fara kishi da zaki ɗebi ruwan xafi ki watsa ma mijin ki?
Da kinyi ajalin sa shikenan kema kashe ki za'ayi mu kuma kibar mu da abin kunya da Dana sani, Kaiton ki Fannah"

Sai Kuma ta xauna itama Fannah da mijin ta suka durkusa a gaban ta, a hankali taci gaba da magana,

" Ummin ki nafeesah Wanda kika fi so Kuma tafi baki kulawa fiye Dani kishiya saida tafitar da ita a gidan ta na shekaru biyar!
Ido fannah ta xaro😳 Momy ta gyada mata Kai tana fadin "yess! Shekaru biyar

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now