chapter 49

299 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
  
         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

49🍎

rungume gawan tayi a jikin ta tana kuka Mai cin zuciya, sunfi minti 20 a haka babu Wanda ya dawo cikin gidan ballantana ta samu Mai taimaka mata, ta kwantar da gawar jidda ta fita da gudu kamar mahaukaciya, tana qoqarin bude gate ne Mai gadi dake zaune akan benci Yana sauraron radio ya taso yazo wurin ta Yana kallon Yanda ta fito ko hijabi Babu a jikin ta ga fiskan ta sharqaf da hawaye, kafin yayi wani magana ta bude qofar dake jikin gate din ta fita.

Bata tsaya ko Ina ba sai gidan su Eesher, tana shiga parlor ta samu kowa a zaune suna ta Hira cikin nishadi kaman ba dare ba, Yaya Muhammad ne ya fara hango ta cike ya tashi hade da fadin
"Subhanallah mama lafiya? Mai yafaru?"

Nan da Nan hankalin mutanen parlorn gaba daya ya dawo kanta kowa na Mata kallon mamaki.

Kuka ta saka musu tana fadin
"Na shiga uku, Muhammad qanwar ka ta mutu, hauwa'u ta mutu Muhammad"

Mimmiqewa sukayi daga mazaunin su cike da tsoro da mamaki, babu Wanda ya iya magana acikin su sai ya Muhammad ne ya tattaro qwarin gwiwar shi yace
"Mama jiddan ne ta rasu? Yaushe?"

"Idan baka yarda ba kaje ka gani da idonka, Hauwa'u na tana kwance Bata ko iya numfashi na kirata taqi amsawa saboda Basu yafe Mata ba, tayi ta roqonsu su yafe Mata Amman sunqi shiyasa ta tafi ta barni taqi dawowa"

Rarrafawa wurin da Feenah take tsaye tayi ta riqo qafan ta tana kuka tace
"Nafeesah ki yafe ma hauwa'u na, dan Allah kice Mata kin yafe Mata ta dawo gareni kina gani tana so  tafi saboda kinqi yafe mata, Dan Allah muje kice wa baban ku ya yafe Mata ta fasa mutuwar Nan"

Feenah kuwa sai ja da baya takeyi tana boye babyn Eesher dake hannun ta don mama ta Bata tsoro sosai, kuka takeyi tana roqonta ta sake ta Amman mama said qara rungumo qafarta take.

Ganin Yanda Feenah ta tsorata yasa Ahmad ya karbi babyn hannun ta ya miqa wa aunty laweeza sannan yaja hannun Feenah suka bar gidan zuwa gidan su.

Direct bedroom din hawas suka shiga Feenah taci Karo da gawarta a kwance har ta fara qandarewa saboda ta dade da mutuwa mama Bata sani ba, tayi wani haske fauu ta qara tsayi.

Ja da baya Feenah tayi cikin kaduwa tana qoqarin fadi Ahmad ya riqo ta ta Fado jikin shi, ta juya ta cusa kanta a qirjin tare da sakin wani marayan kuka, Dan tunda take Bata taba ganin gawa da idon ta ba sai yau, gata ga Yar uwar ta kaman ta Kira ta amsa Amman inaa.

Kuka Feenah takeyi kaman ranta zai fita har tana shidewa ganin haka yasa Ahmad ya jata zuwa tsohon bedroom dinta ya zaunar da ita a bakin gado sannan ya tsuguna a gabanta Yana rarrashin ta a hankali Yana shafa bayan ta yace
"Kiyi shiru Hearty ba'ayin kuka wa mamaci jidda addu'an ki tafi buqata a yanzu, Dan Allah kibar kukan Nan Haka kodan lafiyar abin da ke cikin ki, kiyi ta mata addu'a zata Sami rahama insha Allah, ina kin yafe Mata?"
A hankali ta gyada kanta yace "good, yanzu ki fara Mata addu'a Bari naje na dawo" ya fita daga dakin.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now