chapter 27

255 37 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε _ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_ ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

27🍎

_THE BATTLE JUST_ _BEGINS_

Yana sanye cikin baqar babbar riga da ya qara bayyana hasken fatar shi, fuskar shi dauke da murmushi Yana gaisawa da mutanen da suka halarci daurin auren sa, tabbas Yana cikin walwala Dan ji yake to kaman an dauke Masa wani babban nauyi da ya danne Masa qirjin sa.

Imran ya qaraso gefen shi qasa_qasa Yanda mutanen wurin baza su ji ba yace
"Boss kaga ikon Allah ko yau gashi kaima kayi aure zaka fara dandana zaqin rayuwa, nayi mamakin Yanda nayi sake har ka riga ni shiga daga ciki, gaskiya ya kamata nayi wani motsi Dan bani so ka riga ni ajiye magaji".

"Mtswww, Imran stop this nonesense, kaima kasan sunan wannan auren AUREN QADDARA ni babu wani banbanci tsakanin da da yanzu,

Jinjina Kai Imran yayi yace
"Ahmad kenan, kada fa Nan da wasu watanni a sake Tara mu radin suna, dan  na Sanka baka da Sanya ballantana ace Feenah ta murza kambun ta nasan kwanan Nan labari zai canxa"

" Na riga na fada maka friend, ni Ahmad babu yarinyan da ta Isa ta juya ni ko na durqusa Mata da sunan soyayya HAR ABADA baza'a same ta ba"

"tunda Haka kace let's bet, zaka bada 100 millions idan har alqawarin da ka dauka Bai cika ba"

" Ok na yarda let's bet"

Ya miqa Masa hannu suka yi shaking tare da fadin "deal"

**********

Hawas duk ta gama fita hayyacin tana zubda jini Amman firr taqi ta yarda su tafi asibiti.

Gidan cike yake maqil da mutane Yan biki, kowa hankalin sa tashe ga rigima yaqi ci yaci cinyewa.

Feenah dake rungume da jidda tana kuka tace
"Aunty jidda kiyi wa Allah kizo mu Kai ki asibiti idan wani Abu yasame ki bazan yafe ma kaina ba"

" Idan da gaske kina so na rayu ki barmin Ahmad, Feenah kin riga kin San Ina son Ahmad, Ahmad shine rayuwa ta idan bayi tare Dani rayuwa ta Bata da amfani" ta qarasa tana dada sakin kuka.

Da sauri Feenah tace "wallahi na Baki shi, na bar Miki Ahmad HAR ABADA, ki taimaka ki Bari mu Kai ki asibiti in mun dawo sai ki aure shi"

Yaya Muhammad ne ya shigo ya same su cikin wannan yanayin, ya jingina jikin garu ranshi a matuqar bace Yana takaicin zubar da mtuncin da qanwarshi take yi a gaban duniya yace

"Da kin bar Bata lokacin ki jidda, aure an riga an daura shi yanzu Ahmad ya zama mijin yar uwar ki, duk abin da Kika ga dama kiyi idan kin kashe kanki bamu da hasara kin mutu kafura, Kuma wallahi ko sallah ba zamu Miki ba zamu jefa ki cikin Rami mu rufe"

Timm ta zube a qasa sumammiya, ko kallon ta Yaya Muhammad baiyi ba ya wuce ya fita, sai Yaya Saleem ne yayi kanta da qudu ya dauke ta suka yi waje.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now