chapter 10

358 37 6
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

10🍎

Aisha wato Eesher farace sol sabanin Feenah da take da duhu, Feenah ta fita manyan idanu da gashi dakuma qiba kadan, tana da dogon hanci kuma bakin ta nada kauri kadan ita da Feenah sa'annin junane Amman Feenah ta bata wata biyu yanzu suna cikin shekara ta 17.

Durowa Eesher tayi daga kujeran da gudu tazo ta rungumi aminiyar tata cikin murna ta karbi basket din zobon momy suka miqa mata Feenah ta gaishe ta kafin suka wuce daki sukaci gaba da hiran duniya ba ita tabar gidan ba sai kusan magriba.

   Washegari

Sun shiga cikin makaranta Kamar kullum Amman da mamakin ta yau bayinan a wurin da ya saba tsayuwa damuwan ta ne yakasa boyuwa sbd tasan idan har baizo makaranta ba to ba lafiya ba,
ta qarasa class suka gaggaisa da qawayen ta sannan ta jawo wata Amina tana tambayar ta Ina Majeed.
"nima ban sani ba Amman naji abokin shi Sadeeq yana cewa wai bayi da lfy sosai har sun tafi asibiti yau da safen nan"

Kirjin Feenah ne yafara bugun ukwu ukwu jin halin da Majeed yake ciki qarasawa seat dinsu tayi ta fada ma Eesher Amman da mamakin ta sai taga Eesher tafi ta damuwa ko dayake ba abun mamaki bane duba da irin  shakuwa dakuma kusanci da suka samu abaya.

tun asali Majeed abokin Eesher ne tun a jss1 rashin shigan shi makaranta da wuri kuma yana da nasaba da rasuwan mahaifin shi tun Yana Dan shekara 13 ya barsu da mahaifiyar shi da kannensa biyu mace da namiji, namijin Sagir yanada shekara 9 macen Sakeenah kuma 5.
Baban su ya mutu yabar tarin bashi shi yasa basu sami komai na gado ba saima ragowar bashin da ba'a gama biya ba hakan yasa suka saida babban gidan su suka koma wani Dan qarami Amman dukda hakan basu gama biya ba.

Rayuwa tamusu qunci sun shiga tsanani Wanda ko abincin da zasuci yazama damuwa, hakan yasa Majeed ajiye karatu ya fara aikin qwadago don samo musu abinci ahaka har saida yakai shekaru 17 kafin yashiga jss1 sbd Sagir ma alokacin yakawo qarfi kuma Yana aiki Yana taimakawa da wani abun.

A makaranta ne ya hadu da Eesher kasancewan yadan girmi mates dishi shiyasa bayi da abokai da yawa kuma lokuta da yawa yakan zauna shi kadai a class musamman idan bayi da abinda zaici.

Wata rana anfita break Yana zaune shi daya a class saiga Feenah da Eesher sun shigo dasu ci abinci,
Eesher ta qarasa wurin shi ta tambaye shi meyasa ya zauna shi daya baice mata komai ba sai murmushi daya mata sai ta koma ta dauko masa abincin ta itakuma suka raba na Feenah.

Ba qaramin yunwa yake jiba shiya sa a nitse ya fara cin abincin,  ya gama yamayar mata da food plask din ya Mata godiya.

Hakan ya zamo mata dabi'a kullum sai ta Kai masa abinci, cikin qanqanin lokaci sabo Mai tsanani ya shiga tsakanin su da Majeed,
Wanda har Majeed din ya fara son ta ba tare da yasani ba Kuma dukansu ukwun ba baya ba wajen surutu.

Bayan sunkai ss1 ne baban ta ya samu lbr akan alaqan dake tsakanin su, kuma yayi masa kaca_kaca ya sa iyaka a tsakanin shi da ita sbd shi sam bayi son yarsa ta auri talaka (nace kaman baisan Allah bane Mai azurtawa) .

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now