chapter 64

273 33 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

64🍎

Kaman a mafarki ta juya tana kallon fiskar da ta Dade da manta shi, ta Dade da shafe Majeed daga cikin babin rayuwar ta.

Ganin babu Wanda yaji sunan ta da ya kira yasa ta hade ranta ta qarasa wurin Ahmad ta karbi Raheema daga hannun shi, tayi kaman Bata taba ganin Majeed ba a rayuwar ta
"Wifey ga baqon namu fa, Allah yayi da rabon zaku hadu Dan Yana Shirin tafiya Kenan"

Juyowa tayi tana kallon Majeed kaman yau ta fara ganin shi tace
"Ina wuni"

Saida ya tattaro dukkan nutsuwar shi kafin ya iya Nemo kalmar
"Lafiya Yaya gida"

"Lafiya qlau alhmdllh"

Shiru ne ya ratsa wurin na Yan mintuna Majeed Bai tafi ba Suma Basu ce komai ba kowa yayi shiru da abun da yake saqawa a cikin ranshi.

Sageer ya jawo Yusuf a bayan Ahmad ya 'daka Masa duka yace
"Gobe ma ka sake cizo"

"Ayyo Abbah kaga ya dake ni ko?"

" Menene haka sageer Kai ya ciza ne? Bani son cin Zali fa"

Murmushin Dole Majeed yayi ya kalli Ahmad yace "duka yaran ka ne?"

"Aa wannan biyun na sister na ce" ya fada Yana nuna sageer da habeeb " da babana Mai cizo da baby sai Kuma yaron da ya shiga ciki sune nawa"

Wani Abu Mai daci Majeed ya hadiya Yana Jin zafi a cikin ranshi wai yau Feenan shi ce tayi aure da wani daban har ta Haifa mishi yara?

Jiki a mace ya musu sallama ya shiga motar shi ya bar gidan.

9:34pm

Ta shigo dakin da suke zaune, babba ne sosai babu komai a ciki sai tarin kayan wasa, Ahmad na zaune Akan saet cushion Yana Taya Abdallah assignment Yusuf na zaune a Kan cinyar shi sauran yaran Kuma suna wasa.

"Oya everyone should go to their rooms it's bed time"

Babu musu sauran suka tashi sukayi musu Saida safe suka wuce, Yusuf kuwa na qudundune jikin Ahmad sai tsilli tsilli yake da idanu.

Bulalanta dake maqale a jikin garu ta dauko ta nufoshi
"Kai kullum sai anyi drama dakai kafin ka kwanta? Tashi muje na raka ka daki"

Qara shigewa jikin Ahmad yayi Yana
" Ayyo a shiga uku Ummi aquri"
"To tashi mu tafi"

Miqa Mata hannu yayi ta dauke shi, Ahmad Kuma ya qura Mata Ido Yana karantan yanayin ta, tun da yamma mood dinta ya canza tayi  sukuku kaman wani Abu na damun ta Amman baisan menene ba.

Suna fita yabi bayansu, ta fara shiga dakin Yusuf wanda suke tare da sageer ta wuce dashi bathroom tayi Masa wanka yayi brush sannan suka fito ta saka mishi sleeping dress dinshi tayi musu addu'a ta shafa musu sannan ta wuce dakin Abdallah da habeeb Suma ta musu addu'a ta kashe wutan dakin ta fito.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now