chapter 24

247 36 1
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
            (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

     RUBUTAWA

      UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

24🍎

"Ok kema kinzo kiyi threatening din Feenah ne ta amince da qudurin ku?"

Girgiza Kai Sahar tayi tace
" No sister ni bani goyon bayan abin da Yaya na yayi ko kadan I'm on your side".

Daga kallon da Eesher take Mata tasan Bata gama yarda da ita ba.

Sahar tace
"Trust me sister na Miki alqawarin zan Taya qawarki samun yancin ta saboda an zalunce ta da yawa ko ni akayi ma Haka ba haquri danyi ba idan ma baki yarda ba kawo kunnen ki kiji". Eesher da son gulma takai kunnen ta Sahar ta Rada Mata wani Abu da ni kaina ban ji ba, sukayi shewa hade da tafa hannu.

A ranar

dad da baba dasu dadyn Eesher da uncle Omar da sauran uncles din Feenah suka zauna aka tattauna maganar aure bayan sun ji amincewar Feenan, aka tsayar da aure wata 9 lokacin Feenah ta gama aji Daya.

Bayan an saka Rana dad ya fara gyaran gidan su Feenah, sati biyun da suka dauka na cika suka koma Abuja, su baba Kuma suka tattaro gabaki daya suka koma L mansion dake Bauchi kafin a gama renovating gidan.

Qawance tsakanin su Feenah da Sahar Kam ba'a magana ko yaushe suna cikin waya ko Kuma chat,
Tunda Ahmad ya koma Abuja Bai sake waiwayen Feenah ba ko sau daya da yaga alaman dad na so ya takura shi Kan maganan Feenah sai ya tattara nashi ya nashi ya tafi Chicago.

************

Tura qofar main parlor tayi ta shiga  kalle_kalle take kaman kanta zai balle tana mamakin Yanda aka yi barin dukiya cikin wannan gidan, da Yaya Muhammad ta fara cin Karo Yana qoqarin fita.
"Jidda sai yau Kika ga Daman dawowa gida?"

Bata bashi amsan tambayan shi ba sai cewa tayi
"Yaya Nan gidan waye Haka Mai tsananin kyau, ka kalli kayan more rayuwa cikin gidan nan Dan Allah yaushe kuka dawo? Naje can gidan naga ana ta gyara aka mun Kwatancen gidan nan please yaya akayi kuka zo Nan?".

Maganar ta ba qaramin bashi haushi yayi ba, ita ba damuwar da suka shiga a kanta bane ya dame ta gida da Kuma dukiya ne a gaban ta.

"Jidda yaushe zaki yi ma kanki fada ne? Watan ki 2 fa Baki gida bamu San inda Ina Kika tafi ba, Kuma wayar ki Bata shiga, harta mama tace rabon da kuyi waya sati uku kenan, me kike son ki zama ne?

"Haba Yaya menene na tada jijiyoyin wuya ba gashi na dawo ba"

"Tunda Haka Kika zaba shikkenan kije baba na neman ki daman ya Dade Yana jiran dawowar ki"

Bata yi wani magana ba ta wuce ciki, ya bita da kallo Yana Mata addu'an shiriya kafin ya fita.

Hawas Bata je taji Kiran baba ba sai da ta Gama zagaye dakunan mansion din gaba daya ta bama idanun ta abinchi kafin ta shiga dakin da Hussain ya nuna Mata matsayin dakin baba.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now