chapter 39

268 38 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

39🍎

"Bazan je ba kuma? Bikin aminiyata ce fah!"

" Eh haka nace ko kina da ja ne?" bata ce komai ba ta tsaya tana kallon shi Yanda yake wani cika Yana batsewa, gaba Daya haushin shi ya Gama kamata, yayi parking din motan sannan ya dauki waya yayi dialling wani number magana kadan sukayi ya kashe wayan, ya jingina kanshi jikin seat hade da rufe idanun shi kaman Mai barci.

Kallon shi taci gaba dayi na Yan wasu mintuna ganin bayi da niyyan motsawa tace
"Ya Ahmad na fita?"

Shiru yayi Bai amsa ba sai tayi tunanin barci yayi, ta harare shi tana qunquni
"Mutum sai zafin rai, duk yabi ya hana mutane sakewa Amman yazo Yana barcin shi hankali kwance, ni yanzu idan muka koma wurin bikin Nan bansan me zance wa Eesher ba gaskiya ni an takura ma rayuwana" tsinkayo muryar shi tayi Yana fadin "me Kika ce?"

"Aa ba dakai nake yi ba"

" Believe me idan na sake Jin muryar ki a Nan sai ranki ya baci" tun daga lokacin Feenah ta gimtse bakin ta Bata sake ce komai ba, tasan halin shi Sarai yanzu dai iya dama Mata lissafi.

Bayan 1 hour aka mishi text Yana gani yace ta fita su tafi sannan ya bude murfin motan ya fita yayi cikin gidan ta bishi a baya.

Kallon wurin take yi gaba Daya an canza tsarin gidan bayan tafiyar su Chicago, an saka sabbin furnitures, sabbin curtains, harta carpets da wall papers sabbin colors aka saka, riqo hannun shi tayi tace
"Ya Ahmad akwai Wanda suka zauna cikin gidan Nan ne bayan tafiyar mu?"

Bata fuska yayi yace
" Wa kike tunanin dai zauna min a cikin gida bana Nan?"

" To Dan Allah me muka zo yi anan"

" Ki jirani idan na fito zan fada Miki"  ya wuce bedroom dinshi ya rage kayan jikin shi sannan ya fito ya zauna a dining chair yace
"Abinci nake son ki dafa min yunwa nake ji"

Batayi musu ba ta shiga kitchen ta hada Masa abinci Mai sauqi sai kokuwa take yi da rigan jikin ta a haka ta Gama ta kawo mishi sannan tayi serving din shi ya fara ci a nitse, kallon agogon dake daure a hannun ta tayi taga 11:41 tasan yanzu Kam an kusan tashi daga dinnern gashi tabar wayan ta a mota babu shakka su Sahar suna ta nemanta, batasan lokacin da hawaye ya fara zuba a Idon ta ba, Bata taba tunanin akwai abin da zai Hana ta zuwa bikin auren aminiyarta ba bayan cuta da mutuwa Amman gashi ya Ahmad ya mata katanga da damar da take dashi.

Kallon hawayen idon ta take yi cike da mamaki yace
"Feenah yanzu don na Hana ki zuwa wurin dinner party shine kike kuka?" Shiru tayi bata amsa shi ba tana qoqarin share hawayen ta.

A zuciye ya ture plate din da yake cin abincin ya Fadi qasa ya tarwatse, ya tashi yayi bedroom dinshi sannan ya fito da rigan jamfan da ya cire ya Suri key din motan shi sannan ya riqo hannun ta Yana janta da qarfi yace
"Muje na maida ke wurin da yafi Miki muhimmanci"

Tirjewa ta fara yi tana qoqarin kwace hannun ta daga mummunan riqon da ya Mata tana fadin
"Ya Ahmad kana jimun ciwo ka sake ni Dan Allah, na fasa zuwa bikin, please hannu na"

Bai kulata ba ya jata har jikin motan sannan ya bude qofar ya jefa ta ciki ya rufe da qarfi, a garin haka ya hada da Yar yatsan ta, ihun azaba ta kurma tayi saurin bude qofar da dayan hannun ta, yatsan har zubar da jini yake yi, sai da ya zaga ya tada motan sannan ya lura da abin da yake faruwa, a rikice ya riqo hannun, ya zaro farin handkerchief a cikin aljihun rigar shi ya fara goge Mata hannun duk da haka jini sai zuba yake.

A saba'in ya zugi motar suka fita daga gidan saidai baisan Ina ze kaita ba, bayi son ya kaita asibiti don yawanci likitoci maza ne keyin night duty, Kuma rigar dake jikin ta Ya bayyana surar ta, bayi son wani qato ya kalle Masa Mata Kuma Bata fito da gyale ba, sai a lokacin ya tuna gidan doctor ruqy Yana kusa dasu, da gudu ya sake zugan motan suka tafi gidan sannan ya tsaya ya Kira ta a waya aka Basu izinin shiga.

Dr pinky ne ta fito da hijab dinta har qasa tare da mijin ta suka gaisa da Ahmad sannan yace

"Dr ayi haquri na Hana ki barci, Daman matana na kawo tana cikin mota tasan samu rauni ne a yatsan ta"

"Babu komai Mr Ahmad aikin mu ya gaji haka, Bari na shiga ciki da ita sai na dubata"

Godiya ya Mata ta riqo hannun Feenah suka shiga cikin gidan, sai da ta Gama dressing din ciwon Feenah sannan tace "sister kaman na Gane ki"

"A Ina kenan doctor?"

" Ba kece Feenah wanda Ahmad ya taba kidnapping ba?"

Gyada Kai Feenah tayi sai yanzu ta tuna doctor ruqy lokacin da tayi mata treatment na ulcern ta da ya tashi time din da Ahmad ya sace ta,

"Toh me kike yi tare da kidnapper? Ko ya sake Sato ki ne?"

Dariya Feenah tayi tace " mijina ne, ba sato ni yayi ba"

"Woww kice kidnapping yayi amfani kenan, tunda Ahmad harda zuciya ya hada ya sace............... 🧚

Manage pls😁 Dan tsaya da post Sai bayan sallah insha Allah 💞💞

#vote
#share
#comment

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now