chapter 31

306 36 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

        RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

WANNAN PAGE NAKU NE MEMBERS OF REAL HAR ABADA FANS💙.
Ina godiya da tarin comments din da kuke sambado min😍

31🍎

Gyara tsayuwan ta tayi da taga irin kallon da yake Mata tace
"Good morning ya Ahmad"
Bata Ankara ba taji ya rungume ta a qirjin shi Yana fadin "morning wifey".

Zaro idanu Feenah tayi tana jin ta cikin wani Sabon yanayi, cikin ranta tace'wannan mutumin din Dan iska ne wallahi, shi kwata kwata bai dauki taba jikin mace a bakin komai ba".

Sahar ne ta ja hannun ta suka qarasa jikin table ta ja ma yayan ta kujera ya zauna sannan ta ja ma Feenah akan itama ta zauna, taqi.
"Haba sister kece fa baquwar mu, ki huta abin ki zanyi komai"
Ta fara serving din Ahmad kafin tayi serving din Sahar, ita Kuma ta nemi wuri ta zauna tana kallon su.

"Ke bazaki yi breakfast bane? Ko azumi kike?" Ahmad ya tambaye ta.

" Na riga naci nawa dazu, a qoshe nake"

Miqewa yayi ya tafi inda take zaune yace "ai kuwa Baki Isa ba, dole sai kinyi breakfast tare damu"

Da kanshi yayi serving din ta, dan mugunta ya cika Mata plate maqil da abinci saboda haushin karya Masa doka da tayi.

Komawa yayi ya zauna a tsawace yace "eat" Yana muzurai.

Tsoron shi ya shige ta har 'ya'yan hanjin ta suna kadawa, ga cikin ta a cike yake Amman dole ta dauki fork ta fara cin abincin gadan_gadan.

Ganin Yanda Feenah duk ta daburce yasa Sahar saurin tashi ta qwace fork din hannun ta kafin ta juya wurin shi tace
"Yaya what's this?"

"Babu ruwan ki lil sis, give her the fork right now!!!"

" Amman Yaya tace maka ta ci......."a tsawace ya katse ta.

"Asma'a ki Bata fork dinnan kafin ranki ya baci"
babu Yanda Sahar ta iya haka ta miqa mata fork din ta zauna tana kallon Yanda Feenah take dura abincin kaman zata yi kuka, 'Ashe har yanzu Yaya Bai sauya hali ba? Har yanzu Yana nan da zafin zuciya Yana zalintar baiwar Allan Nan? Indai haka ne basu ga ta zama ba dole su sake diban makaman yaqi Dan ganin Feenah ta rusunar Mata da Yaya Ahmad.

Yanda take tura abincin cikin bakin ta ba qaramin bashi dariya yayi ba, Yana tuna cewa itace jiya take cin abinci kamar bakin ta Yana ciwo, badan kada ta Raina shi ba da ya dauke ta a photo saboda ko wani lokaci Yana kallo Yana Jin dadi.

Taci Rabin plate din ta ajiye fork din tana qoqarin tashi Dan ji take kaman zata yi amai, ya taso ya qarasa inda take zaune ya zaunar da ita,"Ina so wannan ya zama na farko Kuma na qarshe da Zaki tsallake dokokin da nake shimfida Miki cikin gidan nan"
da kanshi ya fara Bata abincin Yana tura Mata a Baki cike da mugunta
"Rule number 4 idan ka fara cin abinci dole ne ka qarasa ba'a yimun almubazzaranci a cikin gida, kin jini ko?"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now