chapter 61

275 33 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

_jiya naci Karo da complaints da yawa Akan dalilin da yasa Imran ya mutu dukda kasancewar shi wani jigo a cikin labarin, Amman Ina bawa masoya na haquri domin labarin tun daga farko har qarshe a tsare yake, nidai kuci gaba dabin alqalamin ummu najma insha Allah wataran zakuyi murmushi_

*Na gode sosai da qauna*😍
*I love you so much*❤️

61🍎

A take ta sume a wurin, maid dinda taje hado Mata tea ta dawo riqe da tray me dauke da cup a hannun ta, ganin uwar gidan ta kwance a qasa Bata numfashi yasa tayi kanta da gudu tana qwala Kiran sunan ta, hakan ya jawo hankalin sauran ma'aikatan gidan, aka debo ruwa ana yayyafa Mata.

Tana farfadowa ta sauqe gauron numfashi Dan a tunanin ta mafarki tayi ba gaskiya bane, da sauri ta rarrafa ta dauko wayarta daya Fadi ta sake dialling numbern Imran, Jin wayar na ringing yasa ta fara murmushi tana share hawayen da suka fara zubo Mata, da aka dauka maimakon taji muryan hubbyn ta sai taji muryan wani daban.

Saboda bayan sunyi accident din mutane dake wucewa sun taru a wurin ana son a gane Yan uwan gawawwakin saidai dukan su wayoyin su a kulle.

Hakan yasa aka Kira ambulance aka tattara su za'a kaisu mortuary har a gano Yan uwan su, wayoyin su kuka police suka dauka dan sunsan duk Daren dadewa wani zai Kira.

"Hello hubby kana inane?"

"hajiya muna neman Yan uwan Mai wannan wayan ne, Dan Allah kina da alaqa dashi ne?"

" Eh! Ni matar shi ne Yana inane? Mai yasame shi?"

" Sai haquri Amman Allah yayiwa mijin ki rasuwa tare da sauran Wanda suke motan, sai kuzo ku karbi gawan su a......." Kafin ya qarasa magana Eesher ta sake yankan jiki ta Fadi sumammiya.

Nan hankali ya sake tashi, da gudu Meenal ta shiga bedroom dinta ta dauko mata hijab sannan masu aikin ta suka dauke ta suka saka ta a mota akayi da ita asibiti.

***********

A rikice ya fita daga cikin gidan mom na biye dashi tana tambayansa sa abin da ya faru, Bai kulata ba ya fada mota sannan ya zuge ta da gudu yabar harabar gidan.

Yana shiga dakin da aka kwantar da gawawwakin ya gansu guda uku a jere, na farkon aka fara bude Masa ya kalli mahaifin shi fuskar shi tar kaman babu abinda ya same shi, wani abu mai daci yaji ya taso tun daga cikin sa ya shaqure shi a maqoshi, ranshi na mishi zafi kaman an zuba mishi ruwan dalma, a take idanun shi suka cika da hawaye ya Basu daman sauqowa bisa kuncin sa, (duk Wanda ya rasa daya daga cikin mahaifan sa yasan Yanda ciwon rashin uwa ko uba yake, Allah ya jiqan wa'inda suka rasu namu da suke Raye Allah ya qara musu tsawon Rai Mai albarka)

Duk taurin Rai irin na Ahmad Saida ya zubar da hawaye fiye da qima da qyar ya qarasa wurin gawa na biyu, Rintse Ido yayi hade da fitar da wani sauti Mai ciwo, gawar Imran ba qaramin firgita shi yayi ba dan Ramin harbin dake goshin sa yasa yayi munin ganin da duk wani Mai Imani idan ya kalla sai zuciyar shi ta tsinke, gawan driver kanma bayi ganuwa saboda shi a gaba take crash dinda suka samu yayi fata fata dashi shiyasa ko budewa ba'ayi.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now