chapter 13

284 29 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

13🍎

Juyowa tayi tana fuskantan shi
"Meyasa ka Fadi haka?" Ta tambaya

"Wannan da kike ganin shi shugaban ubannin gidana ne, hamshaqin Mai arziqi ne Wanda samun irinsu yake wahala Dan  haka duk wani kwadayin ki a kanshi ki cire dan wannan shine gani na farko Kuma na qarshe tsakanin ki da shi."

Murmushi ta sake ta gyada Kai kafin tace
" Nayi alqawarin saina sake ganin shi, indai ina raye sai na neme shi Kuma na mallake shi"

dariya yayi
"Lallai yaro baisan wuta ba sai ya taka, yanzu dai muje na saka ki a adaidaita ki tafi gida rayuwar makarantar da kike yi a cikin gida na ya'isa haka." Yaja hannun ta suka fita daga wurin.

Da sallama ta shiga part dinsu babu kowa a tsakar gidan sai Yaya Saleem da ya fito daga dakin Ammi riqe da hannun Feenah dasu tafi asibiti.

Qyallaro idanuwan ta da Basu buduwa da kyau tayi tana kallon jidda sbd Marin da suka kwasa har qasan idon ya Tara jini.

"Laa hawas yaushe a gari kardai sai yau akayi hutun makarantar? gaskiya munyi kewar ki sosai agidan Nan mun kwana biyu bamu bawa hammata iska ba."

"Ke Feenah kike ko wa? To wlh ki kiyaye ni, ni ba sa'ar ki bace idan Baki daina kira na da hawas dinnan ba saina zubar Miki da hakwara anan wurin."

"Aa baiwar Allah maida wuqan ba'a dade da hadamin jini da majina ba daki zo ki qaramin wani, Kuma ni sunan Nan a wurin saurayin ki baqi mulmulallen Nan naji"

Tsaki jidda taja ta wuce dakin mama, Feenah tabi bayan Yaya Saleem da har ya wuce gaba ya barta.

**********

Zaune yake akan wata traditional chair Mai round table a tsakiyan ta Yana kallon screen din system dinshi suna video call da Imran.

"You can't believe idan nace maka ta mare ni"

Jefar da wayar hannun shi Imran yayi, ya tashi daga daga kwancen da yake Yana kallon Ahmad cike da mamaki yace
"What??? Mari fa kace, Mai kamata da har tayi kasadan marinka?"

"Kaji wani magana a wurin ka Dan Allah,
Yanxu ko harbe ta da bindiga nayi sai ta daga filthy hand dinta ta mareni?
Ko dayake ba laifin ta bane laifina ne da nakasa yin wani Abu akai." Ya fada Yana ciza labben bakin shi na qasa cike da takaichi.

Sassauta murya imran yayi yace
"To yanzu wani hukunci ya kamata kayi Mata?"

"Shine Nima ban sani ba, na rasa wani irin hukunci ne ya Dace da laifin ta,
Zuciya na ingiza ni take yi na harbe ta kowa ya huta."

Wani Dan dariya imran yayi
"You are not serious, kasan Mai kake fada kuwa? Kisan Kai fa, baka taba kashe ko kadangare ba sai Dan kawai an daki fuskan ka kace daka kashe mutum.
To gaskiya ka sauya shawara wannan danyen aikin ba Dani ba."

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now