chapter 37

292 40 4
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

        RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

*wata cikin Daya daga cikin groups Dina Mai suna REAL HAR ABADA FANS tayimun abin da ya faranta min rai matuqa💗, duk da tasan cewa novel Dina ba na kudi bane Amman saboda ta nuna min karamci, ta biya page 36 da na sake jiya, hakan ya Sanya ni nishadi sosai Kuma ya nuna irin qaunar da kuke min da HAR ABADA*😍

*NAGODE sosai da karramawa sister Allah ya biya ki*💞

37🍎

Bata ce Masa komai ba, ta bishi da kallo har ya sauqo yazo wurin da take ya miqa Mata hannun shi,
"Kawo hannun ki na daga ki wifey nah, kin gaji da yawa ko? Daman school akwai wahala Amman kwanan Nan Zaki saba"

Bata tashi a wurin ba Kuma Bata miqa Masa hannunta ba tace
"Ya Ahmad dan Allah game din Nan ya qare haka, wallahi na gaji! Na gaji"

"Ok, tunda haka Kika zaba, Amman Ina yanzu kin yarda nayi nasara ko?"

" A Ina kayi nasaran? Ba kayi nasara a kaina ba saboda nafi maka illah, kaga yanzu haka idan na tashi nayi wanka na canza Kaya na zan dawo rass Abu na, Amman jiya da system dinka ya Gama swimming a cikin bucket da ka fito dashi ya ci gaba da aiki?"

Shiru yayi ya qura Mata na mujiya Yana sauraron bayanin ta da ba wani tasiri yake dashi cikin qwaqwalwar shi ba, abin da yake ji cikin zuciyar shi yafi rinjayar shi, Jin shirun shi yayi yawa yasa tace
"Toh ka gani, ni nayi nasara Dan haka ko yau aka bar game dinnan nice winner"

Lumshe idanun shi yayi Yana dariya, ya budesu ya sake zuba Mata su, saboda ruwan da ya watsa Mata gashin ta da ya fito lokacin da take gyara gyalen, da Kuma mayafin kanta sai suka kwanta luff akan natural brown skin dinta, ba qaramin kyau ta Masa a hakan ba, a hankali ya motsa bakin shi yace
"Ok let's continue playing the game baby"

Ta dafa shi ta miqe sannan ta tattara jiqaqqun takardun ta ta wuce ciki tana fadin
" Allah shine shaida na, duk abin da nayi maka Kai ka siya da kudin ka"

Bin Bayan yayi da kallo ya girgiza Kai sannan ya tashi ya wuce study room ya ci gaba da aikin da yake yi,
Dan har yanzu office babu dama idan suka fita tun safe, wataran ma sai yabi masallaci yayi magriba kafin ya dawo, gaba Daya sun fita hayyacin su shida Ayrah, ita kamma abun da hadu Mata double ga stress ga damuwa, don duk it's qoqarin da take yi wajen ganin ta yakice Ahmad daga cikin ranta abun ya faskara, son da take Masa yafi qarfin a cire shi daga qirjin ta lokaci guda.

Babu Yanda Ahmad baiyi da Imran yazo su hadu Akan aikin Nan saboda su Gama da wuri ba Amman qememe yaqi, yace shirye shiryen biki yake yi bayi da lokacin aiki, gashi yanzu dad shike kula da legendary na Nigeria, Feenah ma dake yanzu hankalin ta na Kan makaranta sai rashin zaman shi a gida Bai dada ta da qasa ba, she is always busy don directly aji biyu ta shiga don already tayi aji Daya a 9ja shiyasa yanzu ta duqufa ma karatu, saidai ko yaushe tunanin Mr arrogant na qara zurfafa a ranta, tayi nisa sosai a son shi ba tare da ta sani ba, Amman Bata taba nuna Masa wata alama akan haka ba tana iya bakin qoqarin ta wajen ganin ta kyautata mishi, tafi so shi da bakin shi ya fara furta Mata kalmar SO, a lokacin ne zata gwaflda Masa irin qaunar da take Masa.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now