chapter 45

272 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

       🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

Wannan page naka ne MUHAMMAD KARIM 80K
Allah ya saka maka da mafificin alkhairi🙏🏼

45🍎

7:06 aka bada bailin Ahmad Yana fitowa da gudu Sahar taje ta rungume shi tana kuka, yayanta Bai taba shiga cell ba Amman yau a dalilin son zuciya irin nata ya kwana a cell, Feenah tana tsaye a gefe tana kuka tasan batayi ma Ahmad adalci ba ko yaushe Yana qoqarin saka ta farin ciki Amman Bata taba saka Masa da komai ba sai tozarci.

Dago fuskar Sahar yayi Yana share Mata Hawayen fuskar ta yace
"I'm alright lil sis stop crying"

Ta riqe hannuwan shi tana tsananta sautin kukan ta tace
"Yaya Ahmad Dan Allah ka yafe mun wallahi bazan sake ba kayi haquri please"

" Shhhh! na riga na fada Miki babu abin da ya same ni, mu tafi gida Nan wurin Bai Dace daku ba" yaja hannun ta suka fita, sunzo wucewa wurin da Feenah ke tsaye ya wurge ta da wani mugun hararan da Saida cikinta ya kada.

Ya saka Sahar a motan dake tsakiya shima ya shiga, Yana ganin Feenah ta qaraso ya rufe qofar motan, jiki a sanyaye taja qafar ta ta nufi motar dake bayan nasu, tana shiga ta fashe da kuka yaukam ta hango fushi qarara a fuskan Ahmad.

Batasan wani hukunci zai Mata ba idan sun tafi gida, koma menene ta yarda zaka karbi duk wani wulaqancin da zai Mata tunda ita ta jawo ma kanta Amman idan ya nisanta kanshi daga gareta ba zata iya jurewa ba.

Kowa da abun da take saqawa a cikin ranshi a Hala suka Isa gidan, suna shiga ciki ya wuce bedroom dinshi, Feenah Kuma ta wuce kitchen ta fara shirya breakfast a Kan dining tana da tabbacin Ahmad baiyi breakfast ba kuma rabon shi da abinci tun jiya da rana.

Ganin Yanda duk tabi ta Susuce Sahar riqo hannunta tace "I'm very sorry sister, na dauka Miki alqawarin da na kasa cikawa, banyi tunanin abubuwan zasuzo da hadari haka, it's very hard for me to go against my brother, daga yanzu zan tsame hannu na a cikin al'amarin ku babu abinda zan iya muku yanzu saidai addu'a Allah ya daidaita tsakanin ku"

Murmushin yaqe Feenah tayi tace
" Babu komai sister, na fahimce ki Kuma Nima nasan bamu aikata daidai ba, Amman Ina roqonki ki yafemin damuwan da na saka ki ciki, daga yanzu duk wasu makaman yaqi na zan ajiye su na rungumi qaddarar da tazo min nasan watarana sai labari"

Suna tsaye a wurin yazo zai wuce sanye da black suit fuskar shi tamau ba alaman rahama, da sauri Feenah tace
"Ya Ahmad ga breakfast dinka"

Ya juyo ya kalle ta cikin murya Mai kaushi yace
"Bazan ci ba" ya fita,  an bude Masa mota zai shiga yaga inaaa idan har ya tafi office cikin wannan yanayin babu abin da zai iya Kuna hakan bashi dai saka wutar dake cin zuciyar shi ya mutu ba, gwamma ya je kawai ayita ta qare.

Ya naushi qofar motan da qarfi ya rufu, cikin sassarfa ya koma cikin gidan ya same su a Yanda ya barsu Feenah sai faman kuka take Sahar na rarrashin ta, ya fisgo hannun ta ya jata har cikin bedroom dinta na qasa ya wurga ta ciki sannan ya garqame qofa.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now