FINAL

617 39 3
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

This whole story is devoted to my little sis khadeejah Muhammad (mmn jawwad) I love you so much sis❤️ happy birthday stay blessed🥳🥳🥳

66🍎 *(FINALE)*

Gaba daya mutanen dake parlorn Saida sukayi kukan Jin wannan labarin musamman aunty Meenal da aunty Shaheeda Jin irin kisan wulaqancin da akayi wa mahaifin su.

Feenah taci gaba da cewa
"Allah ya Miki baiwa sosai baiwar da babu Mai irin ta domin cuta ma wata baiwa ce ta ubangiji kada ki karaya insha Allah Zaki warke, ke wata shaida ce ta dawowar farin ciki cikin rayuwar mu muna qaunar ki sosai Fannah Allah ya Baki lafiya" da ameeen suka amsa Fannah kuwa sai matsar qolla take yi.

Juyawa tayi tana fuskantar Abdallah, irin kallon da take watsa Masa kadai Saida ya saka cikin shi kadawa ya hadiye yawu muqut cike da fargaba.

Ta bude Baki zatayi magana Kenan wayarta ya fara ringing ganin hayaty kan screen din yasa ta dauka tare da tashi daga wurin ta koma gefe amsa wayar Ahmad Dan tun Rana na hudu da fara Basu labarin shida Majeed suka tafi Chicago.

"Hello hayaty"

"Wifey nah kin Gama Basu love story ne ko always saura?"

Murmushi Mai sauti tayi tace
"  just now suka Gama Shan labarin soyayyar Mr Ahmad L da Mrs hayaty, kaga text din da na tura maka da safe Kan maganar su Abdallah? A dan tausaya mishi Dan Allah kaga ya damu sosai sannan ga ciki a jikin safiyya dole tana buqatar Mai kula da ita"

" Hmm kin cika son danki da yawa kawai, idan yasan zai damu me yasa ya rabu da ita tun farko? Idan soyayya need Bai Isa ya nuna min ba Amman nayi haquri, so tunda kin matsa shikkenan ta koma Amman idan wani Abu ya biyo baya ki fada mishi ya kuka da kanshi Dan bazan mishi ta dadi ba"

"Insha  Allah babu ibinda zai biyo baya sai alkhairi zan ja mishi kunne"

" Da yafi Kam, ni zan shigar meeting gobe zan kiraki ki gaida yaran"

" Zasuji yanzu ma zan sallame su dare yayi sosai a nan, bye love you"

" Love you too ummin mu" murmushi kawai tayi ta kashe wayar tana komawa wurin zaman ta ta murtuqe fuska sannan ta fara magana.

"Kwata kwata bamuji dadin abinda kayi ba Abdallah, irin wahalan da nake Sha dakai idan ciwon ka ya tashi irin tashin hankalin da nake shiga wani lokaci kamar bazakayi Rai ba irin shi safiyya take Sha.

Girman Kai babu abinda zai haifar maka sai nadama, yanzu ka duba irin rayuwar mahaifin ka, Yana da tarin dukiya Amman hakan Bai Hana shi respecting Dina ba lokacin da mukayi aure, I believe baka son safiyya lokacin da kukayi aure Amman ko babu komai ita tana sonka tana you maka biyayya iya iyawar ta Amman ni babu itin wannan a tsakani na da mahaifin ka lokacin da ya aureni bayi so na Nima banison shi har Yana laqani ma auren mu da sunan auren qaddara Amman ya rungumi wannan qaddarar har Allah ya sauya Mana shi zuwa alkhairi muka same ku,

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now