chapter 14

239 35 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
  
         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

14🍎

Omar mutum ne Mai gaskiya Kuma Allah ya zuba Masa basira cikin qanqanin lokachi kasuwancin su ya bunqasa Kuma Allah ya tallafa musu suna samun riba sosai.

Bayan shekara guda Abdulmaleek ya tafi Malaysia Dan ya gano halin da Sumayya take chiki, da isar shi ya samu tayi aure har tana da yarin ya guda daya, cike da murna ya dauko kason ta cikin gadon da mahaifin su ya barmu su ya Bata Amman taqi karba tace Masa ta amince ya riqe a hannun sa yayi ta jujjuya wa.

Kafin ya baro qasan sai da yayi ma kawun sa goma na arziqi da duk wani Wanda yasan Sumayya ko Kuma ya taimake ta,
Tun daga lokacin ya fara zuwa Malaysia akai_akai Yana duba Yar uwar shi a haka har ya fara soyayya da Yar maqwabtan su Mai suna Huda bayan wani lokachi sukayi aure ta dawo Nigeria da zama.

Tun bayan auren shi da Huda arziqin sa yake ta habbaka kudade ne suke shigowa ta ko Ina hakan yasa ya kafa enterprises company a Abuja sannan ya fara planning din kafa wani a wajen Nigeria.

A wurin launching din legendary enterprises ne familyn mahaifin sa suka Sami labarin dawowar sa a news Kuma sun tabbatar da shi dinne ya zamo mashahurin Mai kudi, Nan da Nan suka fara Shirin ta yanda zasu shige sa.

Tun zuwan su qofar gidan shi na farko ya gane su saboda bayanin da suka yi sai yasa ana wulaqan ta su saboda Suma su dandana abinda yaji a baya,
Idan suka zo daga Ace musu yayi tafiya sai Ace bayi buqatan ganin kowa a hakan dai har suka shafe kusan wata 1 idan suka zo Basu samin ganin shi.

Duk da Haka Basu haqura ba sukayi ta tusa kansu har suka samu ya saurare su, babu Bata lokachi suka fara bashi haquri suna neman yafiyan shi, Daya haqura ya yafe musu tsananin godiya kaman zasuyi Masa sujjada.

Washe gari kuwa sai gashi sun tattaro tarkachen su qwan su da qwarqwatan su suka yada zango a L. Mansion dake Bauchi dukan su matayen su shuwa Arab ne don lokacin da suke ganiyar chin kudin mahaifin shi suka auro su gashi dukiyan ya qare riqe matan na neman gagaran su.

Bayan dawowar su da wata Daya Huda tayi barin cikin dake jikin ta na wata uku tun daga lokacin Kuma sai shiru har ta shekara uku ko batan wata Bata sake ba, hankalin Abdulmaleek yayi matuqar tashi babu kalan asibitin da basu je ba Amman amsa daya ce suke fada masa 'lafiyan ta qalau' daga baya suka sauya suka koma maganin addinin musulunci a nan ne suka hadu da wani malami da yake taimaka musu da addu'a ya fada musu su saka kullum ana musu sauqan qur'ani Kuma suna yawaita sadaka Kuma ya shawarce su da su gwada sauya wurin zama Dan laluran kaman akwai asiri a ciki.

Da ya sanar da Yan uwan sa dai koma L. Mansion na Abuja da zama Nan suka dage sai sun bishi acewar su Basu son su sake rabuwa da Dan uwansu a Karo na biyu.(kaji Dan Adam)

Saboda Bai yarda da su ba yace musu su zauna anan na Dan wani lokaci daisa a yi musu gini na kansu a Abuja, badan sun so ba suka zauna babu Mai iya musu da shi Dan shine boss din gidan yanzu.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now