chapter 53

267 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

*Tirkashi*

*Rigi-rigi babban dahuwa, mai karya itacen yaro. In kaji tambura sai sarki, in kaji jiniya sai gwamna. Biki na farar kaza, balbela ba gaiya ba.*

Ina kuke? Masoyan *PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION.*
Kungiyar da Ta tara kwararrun marubuta, masu aiki da basira da hazaƙa. marubuta ne wadan da suka san kan alkalami, yayinda suka karanci matsalalon da duniyarmu ta yanzu ke ciki, basu tsaya a nanba, saida suka zaƙulo maganin matsalolin.  kai baki bazai iya baku labari ba, sai dai ku kasance tare da mu,  bayan kun antaya a cikin wannan link.👇🏾
        https://www.facebook.com/groups/2455147078097572/?ref=share

🤭Ap. Na manta ban fada muku ba masoya. Wannan kungiyar mai haɗin kai, da zaman lafiya, Uwa Uba soyayyar gaskiya da amana, sun shirya tsaf domin  kawo muku  Audio ɗin littaffan kunyigiyar gaba ɗaya. Bisa Youtube channel namu.👇🏾

https://m.youtube.com/channel/UCa6VZD_0ZlXycCLTT1i-ygQ

*Muna maraba da ku masoya duk ku antayo, domin, muna alfahari daku*😍

~Mu kafta~🤾🏻‍♀️

53🍎

Ahmad ne ya shigo cikin gidan a hankali gaba Daya jikin shi a muce yake, murmushi tayi sannan ta qarasa wurin shi tayi hugging tana mishi barka da zuwa, shirun da taji yayi ne yasa ta dago ta kalleshi gaba daya hankalin shi bayi jikin sa, cikin kulawa tace "hayaty me ya faru?"

Dan firgita yayi ya juyo Yana kallon ta kamar ranan ya fara ganin ta, Yana tsoron ya fada Mata ya kusa yayi accident Amman Roxy ya shiga gaban motar shi ya tare masa, yasan dole hankalin ta zai tashi ga dayan mummunan labarin da yazo Mata dashi.

Sake tabashi tayi ta maimaita maganar ta kafin cikin inda inda yace
"Babu komai hearty Roxy ne yadan samu rauni shine muka kaishi asibiti, kiyi haquri ban kira na fada Miki ba"

" Ai Nima dazu hankali na ya tashi da nayi ta Kiran wayoyinka Basu shiga, amman na gode ma Allah da ya dawomin dakai lafiya, garin Yaya Roxy ya samu raunin?"

Sosa qeyan shi yayi Yana fadin
" Ba wani ciwo Mai girma bane hearty, kada ki damu it's just a minor injury, muje muci abinci yunwa nake ji yau angon Feenah ya gaji da yawa" ya ja hannun ta suka shiga bedroom dinshi ko wanka baiyi ba ya sauya Kaya suka fito tana tsokanar shi
"Hayaty an qajami baya wanka baya wanki sai ruwan sama ya Duke shi"

Riqo ta yayi yafara mama cakulkuli Yana fadin
"Wato nine qazamin ko? Yau Zaki fadamun dalilin da yasa Kika auri qazami" dariya Feenah takeyi tana roqon shi ya rabu da ita, da Haka taja shi da tadi har suka qarasa dining area, taja Masa kujera ya zauna sannan tayi serving dinshi, duk iya qoqarin shi wajen ganin ya boye damuwar shi yayi hakan Amman duk da yunwan da yake ji abinci ya gagare shi.

Tana cin abinci tana bashi labarin lokacin da Abdallah yaga wata mage a gidan Eesher yayi ta binta da rarrafe Yana riqe Mata bindi dukdai Dan ta saka shi ya manta da fadan su na baya Amman ta lura ko spoon Daya na abincin bekai bakin shi ba.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now