chapter 57

254 34 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

  
Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

Wannan shafin naku ne
*aunty Fenarh matar soja* ❤️
*Fatima batula*❤️
*nimcy sarauta*❤️

57🍎

Har ta gama wanka ma Abdallah ta shirya shi Ahmad na qudundune cikin duvet, a kunnen shi ta rada masa
"My boy kaje ka tashi Abbah, zai kaika Nigeria kaga babyn Mami"

Cike da murna yasa gudu har jikin bed dinda Ahmad ke kwance ya fara Jan duvet dinda yake lullube a ciki, cikin maganar shi da baiyi qwari ba  yace
"Abbah ka ashi ka kaini wuyin Mami ta ciyamin, what is it called?" Ya tambaya Yana kallon Feenah " auwaa anjin lijidi and sugar candy"

"Abdallah hanjin ligidi nace maka? Wurin baby zaku je ba Shan hanjin ligidi ba"

Ahmad Bai bude idanun shi ba ya jawo Abdallah ya kwantar dashi a gefen sa sannan yace
"Kana so na siya maka chocolate?"

Da sauri Abdallah ya gyada Kai hade da fadin "yess Abbah"

"To muyi barci idan mun tashi sai muje mu siyo ko?"
Babu musu ya rufe idonshi ya kwanta limui kamar Mai bacci.

Ganin haka yasa Feenah ta qarasa wurin su tana fadin
"Wato har ma yaron naka kake bawa cin hanci ko hayaty? To ka tashi ka shirya ku tafi dan yanzu Eesher ta Kira ni Wai sister ta aifi namiji"

Shiru yayi Mata Bai amsa ba, ta fara jijjiga shi tana
"Ka tashi Mana please baniso kayi isan dare sister tana buqatar ka yanzu ka bude idon ka hayaty"

Tashi yayi ya zauna Yana Bata fuska kaman zai saka kuka yace
" Kin hanani barcin kinji dadi, kira min lil sis din muyi magana"

Dauko wayan shi dake bedside drawer tayi ta Kira Sahar sannan ta saka wayar a speaker, bugu daya ta dauka
"Hello yaya ka iso ne?"

"Na iso Ina? Kinsan yanzu 8:30 na safiya ne Amman kika takura Saida aka katsemin barci, kwata kwata bakuson ganin mutum cikin Jin dadi ko wata 1 banyi da zuwa Chicago ba zaku sake maidani Abuja gaskiya Baki kyauta min ba, yanzu me kike buqata da zanzo miki dashi?"

Lissafa masa tafara yi shikuma Yana rubutawa har suka Gama sannan Feenah ta karbi wayan, tace
"Yanzu Dan Allah kunika kikayi sister??"

" Mtsww banison rashin mutunci sau ukwu Kenan kina tambaya na kokuma kunikan haramun ne?"

Girgiza Kai tayi tace " Aa, Naga ko Eesha da tariga ni aihuwa batayi na biyu ba shine abun yabi ya dameni"

" To kada ki dame ni, da Raina da lafiya ta babu abinda zai daga min hankali, Kinga mutane sun fara zuwa sai anjima" kitt ta katse Kiran.

Jawota Ahmad yayi ta samu matsuguni a cinyar shi Yana kallon cikin idonta yace
"Da yanzu a 9ja muke da kema kinyi ma Abdallah qani ko qanwa"

" Au hayaty nima kunikan kake so nayi?"

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now