chapter 7

387 41 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

    🌹 HAR ABADA 🌹
           (Forever)

     LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

TELEGRAM: https://t.me/joinchat/VOW8-BwH_DjWH1YfVcFONA

WATTPAD: https://my.w.tt/4ZfEeBpVecb
OR
@ayeeshatmuhd

BY

UMMU NAJMA

DEDICATED TO
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

07🍎

Dariya khaleel yayi yace
"Kai gsky guy qanwar kannan drama queen ce, ammafa tamin, gsky na kamu."

Bata fuska Abdallah yayi
"Kaga malam kada ka jawo ma mutane raini, wannan yarinyan da kake gani rashin kunya ma haka ya ganta ya barta,
Kuma qaraman yarinya ce sosai gata a bushe kaman sandan rake."

Murmushi khaleel yayi yace
"eh a haka nagani Kuma inaso"

Tsaki Abdallah yaja
"Da'alla tashi mu tafi"

Sukayi ma Ummi sallama suka wuce.

Wasa_wasa tunda khaleel yaga Fannah barci ya qaurace ma idanun sa,
Da ya kwanta sai hoton fiskan ta Yana masa yawo aka,

Bayan kwana 4 ya Kira Abdallah yace gashinan zuwa, zasu tattauna wani magana Mai muhimmanci, Yana isa ya kuwa ci sa'a tana zaune a parlor tana game a iPad,
Wannan karon gown ne yar kanti a jikin ta red Mai dogon hannu, yasha stones silver, kamar ranan yauma kanta babu dankwali, sai wata yar flower red data maqala a gashin ta.

Gaida shi tayi ciki_ciki kaman Mai ciwon baki, ya amsa yana jin wani Abu na fisgan shi aran sa game da ita,
Miqewa tayi zata je saka dankwali domin tunda tagan shi tasan wannan azzalumin na kusa Kuma ko ina yake zai fito parlorn,
Kuma bata son su hadu kwata_kwata saboda da safe saida tasa Intee kuka tace sai ta fada Masa ta zuba Mata ketchup a foundation .

Juyawan ta keda wuya sukaci karo Yana hararar ta fuska a tamke yace
"Wato baki jin mgn ko? Kina fama da kunnen qashi, ban hanaki zama babu dankwali ba," ya sake kafa Mata ranqwashi tasa kuka.

Har zata wuce ya hango tsagun dake jikin riganta tundaga qasa har wurin guiwan ta
"Kee! Amman yarinyan Nan baki da hankali kin dauka gidan nan kafurai ne aciki da zaki na Mana yawo tsirara, to wlh ki shiga hankalin ki Kuma kije ki chanza kayan jikin ki yanzu.

Wucewa tayi tana qunquni tana kuka.

Ya juya ya kalli khaleel sukayi musabaha ya masa iso cikin qaramin parlorn sa.

Suna zama khaleel yadan Bata fiska yace
"Guy mgnn gsky kana takura min Mata da yawa, kabarta ta sakata ta Wala.
Kallon shi Abdallah yayi na dan sakwanni kafin yace
"Wai Daman da gaske kake yi?"
Saida khaleel yayi dariya kafin yace
"Wlh dagaske nake, babe din ta gama tafiya da imani na,
Abinda yakawo ni wurinka ma kenan kamin kwatancen gidan su na tura a nemo min auren ta."

Gyara zama Abdallah yayi in a serious tone yace
" Khaleel yarinyan Nan da kake ganin ta ba qaramar fitsararriya bace gashi bata da hankali har sau biyu kana ganin haduwan mu da ita kwata_kwata bata jin magana.
Wai a hakan ma ni tana jin tsoro na ne,
Kuma yarinyace qarama she is just 16 and half tsayin qafa kawai takeda shi, bana tagama secondary school fa.
Pls kada kaje ka zubar da girman ka wurin ta."

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now