chapter 47

334 40 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
  
         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

47🍎

Tabe baki tayi ta tashi zatabar wurin yayi saurin riqota ta koma ta zauna, yace
"Feenah har yanzu Baki cire qiyayya ta daga zuciyar ki ba?"

" Nifa ya Ahmad bance Ina qinka ba"
" Amman kince baki Sona"

Batace komai ba ta tashi ta fara dusting Yana ganin haka shima ya tashi ya canza kayan shi zuwa na excercise ya fita.

Bayan 30 minutes ya dawo ya samu ta Gama gyaran dakin ta tattari kayan aikin ta tana Shirin fita yace
"Ina zakije?"

"Zan tafi kitchen ne mu hada breakfast"
"Idan Kika tafi waye zai taimake ni nayi wanka"

Zaro Ido tayi tace
" Ya Ahmad wankan ma said an Taya ka?"

Hannu yakai kaman zai tsole Mata Ido tayi saurin rufesu
"Wannan qananun idon naki masu abun tsoro da kike budemun su na meye? Kinsan ba iyawa zanyi ba jiya ma lil sis ne taimaka min nayi, ki barta ita taje su hada breakfast din ke kiyi aikin ladan ki a nan"

Rigan jikin shi ta cire mishi ta hada mishi ruwan wanka, bayan ya shiga ta ciro mishi kayan da zai saka ya tafi office tabar dakin.

Suna Gama breakfast yace suje su shirya ita da Sahar su tafi office, ta fito cikin atamfa orange color ta same shi Yana tsaye Yana waya da imran, kallon ta yayi tun daga sama har qasa, ta goge makeup din fuskanta ta saka wani qaton gyale, murmushi ya sakar Mata yace "hearty kinyi kyau" sunkuyar da kai tayi tana wasa da zoben hannun ta.

Imran da yaji abin da Ahmad din ya fada yayi dariya yace
"Su friend an fara hawa layi Kai da madam dinne haka kuke soyewa"

"Eh magulmaci, ni banison irin shiga ukun Kan nan, kayi abun da na saka kawai gamunan zuwa"
" Da ita ne Zaki zo office din?"
" Eh! Ko kana da ja ne?"

" Aa Allah ya kawo ku lafiya Nima yanzu zan fita"

Tare suka fita hannun su saqale cikin na juna Sahar tana biye dasu a baya, tun da suka fara tafiya Feenah tayi shiru sai shine Mata Hira jifa_jifa a haka suka Isa gaban katafaren building din Wanda yafi LEGENDARY na Nigeria girma sosai Yana dauke da floors 12 suna fita daga mota motar su Imran ya shigo, har zasu shiga ciki imran yayi Kiran Ahmad Bai juya ba ya tsaya Yana jiran shi.

Wani ihun da Sahar da Feenah sukayi ne ya saka shi saurin Juyowa Yana kallon su, yaga sun rungume Eesher har sun kusan kaita qasa da sauri Imran ya taro ta, ya Bata Rai yace
"Matsalar hada Abu da qauyawa Kenan wallahi, ku bakusan Bata da lafiya bane Kun daura Mata nauyin ku kalen yanzun Nan ku jawo min asara"

Murmushi Eesher tayi tace "I miss you girls"
"Da kinyi missing dinmu da kinzo inda muke tun da kikazo sau Daya Baki sake dawowa ba muna gari daya amman zumunci ya gagare ki" cewar Feenah.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now