chapter 35

315 39 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

  
Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         RUBUTAWA

        UMMU NAJMA
   
DEDICATED TO
MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

Kaman an rubuta min sunanki*✍🏼
A cikin zuciya taaa*💝
Kece saraunya ta yarinya*👸🏽
And I have to let you know oh*👩🏼‍🎤
Fatima...fatyma..fatima fatyma............🤩💓

Honeymoon pages naki ne ke kadai fatymarh isma'il Aka amaryan ahmadulle🤭 idan kinga dama kada ki san musu ko kadan😅

35🍎

A tare suka juyo idanun su ya sauqa Akan fiskan Ayrah dake ta faman zabga murmushi, kallo Feenah take qare Mata tun daga sama har qasa, doguwa ce kuma kyakkyawar baturiya gata da grey eyes gashin kanta Mai haske sosai Wanda ake Kira da blonde hair, tana sanye da gypsy top da mini flowy skirt.

Tabe baki Feenah tayi cikin ranta tace 'mun baro jaraba a 9ja gashi munzo mun hadu da Wanda yafi wancan, Allah ya tsari wata shegiya damun wargi taga Yanda zanci qaniyar ta no mercy' a fili tayi qwafa.

Sai a lokacin Ayrah ta lura da ita, fuska a sake ta miqo ma Feenah hannu sukayi shaking
"I'm Ayrah Felix from L.A what about you?"

Bata jira amsan Feenah ba ta juya wurin Ahmad take
" It's great to have you here Sir, who is she? Is she a relative?"

" She is my wife, her name is Feenah"

A take fara'an Amrah ya bace batt, ta qaqalo murmushin yaqe tace
"Nice to meet you Mrs L" ta maida duban ta wurin Ahmad tace
" sir, shall we leave? The convoy is waiting"

" Ok" yace ya ja hannun Feenah suka tafi.

Suna Isa gidan suka samu komai a gyare an canza abubuwa da yawa, ba qaramin kyau gyaran da yayi ma Ahmad ba, ya kalli Ayrah hade da sake Mata murmushi yace
"Good job Miss Felix, the place looks good I like it"

Har cikin ranta taji dadin yabon ta da Ahmad yayi, gashi har da kyautan murmushin shi Mai tsada.

Feenah Kam ta sake Baki ne tana kallon tsaruwa na wannan tamfatsetsen gida yayi girman duplex dinsu na 9ja guda 3 wajen tsaruwa kuwa ba'a magana don duk wani Kayan qyale_qyale na bature an saka shi, kusan 30% na gidan tinted glass ne.

Maganar Ayrah ce ya dawo da Feenah daga duniyar lissafin da ta tafi, tana tambayar izinin Ahmad da ya barta ta zauna tare dasu don Daman ita ba Yar garin bane aiki ne yake kawo ta Chicago Amman mahaifin ta na Los Angeles mahaifiyar ta kuma ta rasu tun tana shekaru 14.

Ahmad Bai nuna damuwa ba ya Bata izinin zama tare dasu Daman dalilin da yasa yake Hana ta zama babu mace ne cikin gidan.

Kallon shi Feenah take yi da mamakin qarfin Hali irin na Mr arrogant, Bai tambayi izinin ta ba a matsayin ta na matar gida dai bar wannan ta zauna tare dasu? Zanyi maganin ka ne, ta fada cikin ranta.

Dakunan su suka shiga suka yi wanka suka huta, Basu suka fito ba sai dare, sallah ma a daki Ahmad yayi domin masallaci nada nisa daga gidan Kuma Nan ba Nigeria bane ballantana kowa ya samu ikon gina nashi masallacin.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now