chapter 21

267 37 0
                                    


(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      🌹HAR ABADA🌹
          (bazamu rabeba)

       LOVE & FRIENDSHIP

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Vote me on Wattpad @ayeeshatmuhd

DEDICATED TO MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA

Wannan page na sadaukar dashi zuwa ga
sadiya vice
Maman Sadeeq
Hadiza Mustapha
Ummu ammar

Sahrhin ku na matuqar qayatar Dani Ina godiya sosai 😍❤
21🍎

Kallon fuskar ta yake yi Yana tunanin kalar bala'i da masifan da ya jefa kanshi a ciki, muryan dad ne ya katse shi.
"Son ai muma sai a bamu muga picturen yarinyan mu mugani ko, ka qura Mata idanuwa ko Mai kake kallo oho".

Dariya duk mutanen parlorn suka yi shi Kuma yayi kicin_kicin da fuska ya miqa ma dad wayar ya juya cikin basarwa ya ciro nashi wayan Yana Danna wa.

"Subhanallah, Allahu Akbar ai barewa ba data yi gudu Dan ta yayi rarrafe ba" dad ya fada yayin da idanuwan shi suka yi arba da pic din Feenah.

Juyowa Ahmad yayi Yana kallon shi cikin son Gane inda maganar shi ta dosa.

"Huda, Ahmad Kun tuna takardan da na nuna muku ranar da aka Kama su Mr Ezekiel?
To wannan yarinyan ita ta rubuta min shi, ita ta ceci rayuwar gabaki dayan mu a wannan Rana.

Daram...daram...dum...dum... Haka zuciyan Ahmad yake bugawa, sauran mutanen parlorn Kuma suka yi qabbara tun kafin dad ya Fadi abin da ya faru suka Gane maganar babba ce tunda ya hada da ceton rayuwa.

"La haula Wala quwwata illa billa da hasbunallahu wa ni'imal wakeel yake ta mai_maitawa cikin zuciyar Yana tuna irin cin zarafin da yayi ma Feenah, irin cin kashin da ya Mata da Kuma wahalar da tayi a sanadin shi, saboda shi ta zubar da hawaye babu adadi.

"Nafeesah sunan ta ko?"

Gyada Kai baba yayi yace "eh  sunan ta kenan"

"Nafeesah da ita da wata qawarta Aisha idan ban manta sunan ba, wata ranar Thursday sun ceci rayuwa ta a Abuja lokacin da wani maha'in cin driver na ya Kai ni wani daji Yana qoqarin rabani da rayuwa ta, su suka kasance tare Dani har na koma gida lafiya Kuma suka ankarar Dani Akan abin da yake Shirin aikata mun, Allah ya saka musu da alkhairi.

Ameeen, ameen kowa ya amsa Banda mama da taji kamar zuciyar ta zai Kama da wuta saboda baqin ciki, taso ace jidda ce wa'innan masu kudin suke yaba wa haka Amman ko wani lokaci Feenah da mahaifiyar ta suna tsare musu gaba.

Yaya Muhammad yace "baba ba a ranar akayi kidnapping Feenah bah?"

"Baba yace eh toh ai alhamis biyu tayi a Abujan".

"A  ranar alhamis ta farko suka fita ita da Eesher na biyun Kuma tana kwance a gadon asibiti bayan ta kubuto".

Cike da damuwa dad yace
" Subhanallahi, kidnapping Kuma? Yaushe hakan ta faru Kuma wa yayi kidnapping dinta?"

Ahmad Kam yanzu zama ta gagare shi ya game rudewa gabaki daya sai mutsu_mutsu yake yi qiris yake jira yaji sunan shi ya fito daga bakin yayan Feenah.

"Ai dad mun auna arziqi ranan da suka fita Allah ya hada su da mugayen mutane Yan yankan Kai suke sace ta Amman daga baya Allah ya taimake ta ta kubuta daga sharrin su ta dawo gida".

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now