chapter 51

262 32 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

      *🌹HAR ABADA🌹*
          *(bazamu rabeba)*

       *LOVE &* *FRIENDSHIP*

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd
  
         *RUBUTAWA*

        *UMMU NAJMA*
   
*DEDICATED TO*
*MAMAN MAMY SHALELE AND BEELAT SARAUNIYA*

51🍎

Tun asuba suka dauki hanya Basu Isa qauyen ba sai 11 a Hala ma motocin su ba zasu iya qarasawa cikin qauyen ba don gidajen dake Kan hanyan wurin da mutane suke bi suje wurin bokan a cunkushe yake.

Fitowa Amrah tayi daga motarta ta cire sunglasses din dake idon ta tana kallon Yanda Rana ya qwalo ga zafin shi tana ji Akan fatar ta, momyn ta da aunty Zali suka fito daga dayar motan sai Stella dake make cikin motar Amrah Bata da alaman motsawa, leqa cikin motar Amrah tayi ta window tace
"Yaya kike zaune ciki kin barmu cikin wannan uban ranan Kuma kinsan ba lokacin batawa muke dashi ba ki fito ki nuna Mana hanya"

Stella Bata dago ba taci gaba da Danna wayanta tana fadin
"Ki tsaya diva Ina Kiran Mai akori kura be yazo ya shigar damu ciki Dan akwai sauran tafiya Mai nisa Amman wurin Nan babu network sosai"

" Menene Kuma akori kura waye zai shiga Miki wani akori kura? Ni banison lalaci ki fito mu tafi da qafarmu haka kawai a banza bazan Bata kayana Mai tsada ta shigar wani akori kura ba"

Fitowa Stella tayi suka Kama hanya Saida sukayi tafiyan kusa awa 1 a qasa Basu Isa ba gaba dayan su sun galabaita ga Rana, Amrah tace
"Stella Wai yaushe zamu Isa ne? Na gaji fah,"

Stella ma da ta Gama gajiya gaba daya ta hada zufa, foundation dasu contour duk sunji zafi zazzago tace
"Munfi rabi yanzu anjima kadan zamu isa"

Ta juya hade da fadin "gaskiya mu tafi Nikam na haqura irin wannan wahala sai kace aikin neman aljannah mu tafi gida kawai mu nemo wata hanyar daban Amman bazan iya wannan ba"

Maman tace
" Aa baza'a yi haka ba, mun riga mun fito kuma menene amfanin komawa buqata Bai biya ba, kinaji tace Miki munfi rabi, idan muka juya ma babu wani amfani saboda wani wahalan zamu sake Sha a hanyar komawa, ai Daman sai ansha wahala kafin aji dadi"

Haka suka qarasa can cikin jejin ga gajiya ga qishin ruwa, suna nufan gidan wannan matsafin ta fara hongo mutane rututu suna bin layi, yawansu Saida ya Bata tsoro Amman ba abun mamaki bane Dan Suma Saida suka bada 150,000 ma wani mutumi yabi musu layi tsawon wata Daya.

Sunan su suka bayar ma wani mutumi a jikin qofar, Yana riqe da wata takarda fara wall a hannun shi baby ko digon rubutu Amman da mamakin ta tana fadan sunan ta sai gashi ya fito bayyane Kan takardan, mutumin ya Basu Izinin shiga cikin Dan madaidaicin gidan.

Wasu mutane ta samu zaune Akan banci bataji kyankyamin su ba ta zauna a gefen su don kayan jikin su kadai shaidan ne nacewa sun dama ta sun shanye a arziqi, ba'a Jima ba su aunty Zali da Stella suka shigo Suma suka nemi wuri suka zauna suna zaman jira.

Nanma sunfi minti 30 kafin suka samu layi yazo kansu aka Basu Izinin suka shiga, wani fankacecen daki ne da kayan tsubbuce tsubbuce a cikin shi, Kuma komai na dakin na motsi, har da wani cokali ma a tsakar wurin sai shawagi yake yi sai ya shiga cikin wannan buhun ya debo garin magani ya shiga wani ma ya debo ya hada a cikin kwano ya gauraya, a tsakiya Kuma wani babban mutum ne yana zaune cikin jajayen Kaya, idan ka Gandhi kaman wani mutumin arziqi ga gemun munafurci daya tara.

HAR ABADA (Under Edition)Where stories live. Discover now